Monday 12 December 2016

BALLAGAZAR MACE COMPLETE

[10/16, 4:21 PM] mrm kd: ◾BALLAGAZAR MACE ◾ 1&2

©MRS SAIF
                   ®NWA


wannan labarin zan iya cewa ya faru da gaske, Cox some episodes are non fiction, while some are fiction, don na yi k'arin gishiri a wasu wuraren saboda littafin ya fi  d'and'ano 💋

SANARWA
Wannan labarin ban yi da wata manufa sai don fad'akar da 'yan uwana mata, musamman masu aure, da kuma ' yan matan da suke da niyyar yin aure, don haka ban yi don wata ta ji haushi ba, sai dai arashi ne da duk mai irin halin,Allah ya sa mu gyara ameen. 👏🏻


GARGAD'I
Ban yarda gardi ko gardiya su juya mun buk ba, ta ko wace siga, musamman masu editing su cire sunan writer, don Allah ku daina, ba abu mai kyau ba ne.




Tunda na jefa k'afata a cikin gidan na ke ta Karo da kwanika, ga sunan birjik a tsakar gidan, ba wanki, tamkar kwanikan da mutanen gari suka ci abinci, saboda tsananin yawansu,kuma abun da ya dad'a d'auremun kai, gurin da aka zuba kwanukan kwata_kwata bai yi kama da wurin wanke_wanke ba, cikin 2mints na k'arewa gidan kallo.

Madaidaicin gida ne, wanda kana shigowa za ka tarar da parking space wanda aqalla ya ci motoci hud'u, sai parlour d'auke da 4 bedrooms, kitchen, toilet and store.
Sai da muka shiga parlourn, na lek'a kitchen sai na ga ashe kusan duk kayan kitchen d'in ne a waje ba wanki.
Na juya na kalli sister maryam da muka je tare, na ce
"an ya kuwa nan ne gidan amarya da ko wata bata yi a gidan miji ba??
Maryam ta ce "nan ne don nan ta kwatanta mun da ta shiga lokacin ba kya nan".
Ban gama mamaki ba kuwa sai ga ta ta fito, tana washe ba ki, ta ce "maman Twins ashe ke ce a gidan na mu, ku shigo mana"
Murmushi na yi, na ce "eh Amarya, ai sister na ta ce kin zo har sau biyu ba ki same ni ba shi yasa na ce bari na lek'o".
Soshe_soshe ta fara kamar wadda ba ta yi wanka ba, tana fad'in "eh wallahi, zaman ne mutum d'aya ba dadi, shi yasa na ke so mu saba dake, tunda ni dai anguwar nan ban San kowa ba, kad'aici duk ya dameni, kin ga na yi kallon har na gaji, haka ma chat, don haka nake so na dan samu wurin zagawa, ta k'arashe maganar da sakin wata dariya.
Kallon_kallo muka tsaya yi da maryam, sannan cikin yak'e na ce
"haka ne gaskiya"
Sai kuma ta mik'e tana fad'in bari ta kawo mana ruwa, tafiyarta ta ba mu daman k'are ma parlourn kallo, ga parlor har parlour, amma rashin gyara yana barazanar hana a ga kyan parlourn, don TV kawai za ki kalla ki san parlourn yana buk'atar gyara, don k'urar da ke jjkinta tsaf zan rubuta sunayen writters da muke da su a jiki a kuma ga ne.

Ga shi tunda muka shigo wani bala'in zarni ke tashi, daga cikin kujerun da muke zaune, abin ya matuk'ar ba ni mamaki abinda ya kawo zarni d'akin amarya.
Bayan ta kawo mana ruwa muka d'an ta6a hira da ita, muka ce za mu tafi, ta ce
"to shike nan na gode, sai na shigo"
 Na bita da to, sai da za mu fita na hango mage a cikin flowers d'in da ke harabar gidan, cikin raina na ce tabbas zarnin da muka ji, na fitsarin mage ne, don rashin kula har ta bari mage ta rik'a shiga d'aki tana lafta mata fitsari, haka muka kuma tsallake kwanikan nan muka wuce, ina tunanin ita kuwa tana aikin meye har wanke_wanke ya tarar mata haka kamar tun da aka kawo ta ba ta ta6a wanke kwanika ba , don set d'in warmers ga su nan kala_kala banda pots, plates, spoons, knives da sauran kayan amfani duk baja_baja kamar ana gwanjon su.

Bayan mun iso gida na kalli maryam na ce
"gaskiya matar nan akwai gyara a lamuranta, kalli fa gidanta tun kafin ta kai wata biyu da aure, ai dole na cigaba da bibiyarta don ganin irin annakiyar da zata yi, saboda na d'aukowa readers rahoto".....


Mum Twins 😍
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ◾BALLAGAZAR MACE ◾3&4

©MRS SAIF
                    ®NWA

Wacece Nadeeya ???
Nadeeya 'ya ce a wurin Alhaji Sani Haruna, asalin su' yan garin dutsen jahar jigawa ne, domin dukkan su a can aka haifesu, su goma cif, mama Haleema ta haifa, su takwas ne mata, sai maza biyu, su ne manya.
Nadeeya ita ce ta bakwai a gidan, mahaifinsu yana da kud'i dai_dai gwargwado, don ba abun da baya musu na buk'atar su.
Mutum ne shi mai son farantawa iyali, don duk abinda ake ya yi, za ka gan shi a gurinsu, daga kan sutura kayan kyale_kyale ne, da na gyaran gida ne duk a wurin su za ka fara gani, sai dai kash!!! Maman su muguwar k'azama ce,da ko inkula akan komai, domin ko 'ya' yan ta, bata basu cikakkiyar kulawa,bare har su samu kyakkyawar tarbiyya, shi yasa suka taso da baud'add'un halaye duk abinda suka ga dama shi suke yi,Nadeeya ga azababben son yawon tsiya, barin ma aka ce biki, anan kuwa ko za a kasheta sai ta je matuqar ta san da bikin,baya da k'azanta da ta zama kamar gadon gidan su, don kusan dukkansu suna da wannan halin.
Don ma sun samu uba mai kashe musu, don duk abinda ya samo zai kawo gida, amma ina nan da nan abubuwa suke lalacewa da an kawo saboda rashin gyara, gida ga shi k'ato, ya kuma k'eru, amma daud'a duk ta kashe gidan, idan ka shiga gidan kamar shek'ar karnuka, don maman su ba ta iya komai sai dai ta saka 'yar aiki, gata da 'ya'ya mata Allah ya ba ta, amma ba ta saka su sai dai su ci su yi kallo, idan lokacin barci ya yi su je su kwanta.
Ga shi' yar aiki d'aya ta ke d'auka duk girman gidan, ita za ta yi komai, don akwai ta da son kud'i, ba ta son ta d'auki 'yan aiki da yawa ta san za su ci kud'i da yawa, shi yasa da sun fara sun ga baza su iya ba, sai su gudu.
Daga k'arshe ta hak'ura da maganar ' yan aikin, sai su ke damalmalaya ita da sakarkarun 'ya' yan ta, aikuwa a lokacin ne k'azanta ta samu gindin zama a gidan, don sai rana ta kusa fad'uwa suke fara shirin share_sharen gida, wanke_wanke kuwa sai dai duk wanda zai yi amfani da kwano ya je ya wanke da kan shi.

Shi kam mopping ba a ma maganarsa, don sai a yi wata gidan bai samu arzik'in mopping ba. Don idan ki na taka tiles d'in gidan, sai ki rantse gam aka zuba, saboda dank'o, don sai ki na d'aga k'afarki da k'arfi, gudun mannewa a jiki.

A unguwar ma idan ba ki ce gidan k'azamai ba, baza a gane gidan su Nadeeya ki ke nufi ba, tun mai gidan yana fad'a har ya saduda ya hak'ura, shi ma ya bi.
(kun san idan mace k'azama ce, ko da mijinta yana da tsafta sai ki ga a hankali ya fara rikidewa shima yana zama k'azami)kafin daga bisani Allah ya masa rasuwa, a lokacin Nadeeya na ss1.
To daga nan fa sai al'amura suka dad'a ta6arbarewa, don mai hana su wasu abubuwan ba ransa, sai abinda mama ta zartar ita kuma dama ga ta sai a hankali.

Dama hausawa sun ce
"Da na gaba ake gane zurfin ruwa,"
Saboda haka k'azantar Nadeeya da duk wata ta6ara mai license ce, don tun daga gida ta debo ta, ku dai ku biyo ni don Jin irin tata annnakiyar, don bahaushe ya ce
"gado fi ya ke"


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪4&5

©MRS SAIF
                    ®NWA

Misalin k'arfe 6 na yamma Faruk ya dawo daga aiki, ransa a matukar 6ace ya shiga parlourn gidan, akan kujera ya tarar da ita tana shan fruits, duk ta yi kaca_kaca da 6awon kankana da lemo, don gida biyu ta raba kankanar sai ta d'auki 6ari d'aya ta kafa kai tana sha.

Wata naunanniyyar ajiyar zuciya ya sauke, ganin da ya yi ita kanta ba abinda ya chanza a jikinta, don tun shekaran jiya ta saka kayan jikinta, amma har yau ta kasa cireshi, wani d'an k'aramin tsaki ya ja, da niyyar ratsewa ta gaban ta ya wuce d'akin sa.
Hakan ya yi dai_dai dawowar nadeeya daga duniyar da ta lula ta shan kankana, juyowa ta yi tana kallonsa tare da fad'in "Faruk har ka dawo ke nan, ta fad'a tare da washe baki.
Kai kawai ya gyda mata ya k'arasa shigewa d'akin sa, baki ta ta6e tare da fad'in" mutum sai shegen miskilancin tsiya maganar ma wahalar yi take masa".

Faruk kuwa yana shiga d'aki kayan sa, ya tu6e, ya shiga wanka, bayan ya gama ya d'oro alwalar magrib, farar jallabiya sol ya saka, sannan ya feshe jikinsa da perfumes d'in sa masu dadin k'amshi.
Parlourn dai ya kuma komawa, still tana nan yadda ya bar ta, sai remote da ta d'auka tana canja channel, kuma yanzu ta gama shan kankana, ayaba take ci.
Neman guri ya yi ya zauna a d'aya daga cikin kujerun parlourn, duk da bai Jin dadin yanayin tsamin dake ta shi daga cikin parlourn, amma haka ya daure ya zauna.

Ganin ya zauna ya sa Nadeeya Jin dad'i, don akwai ta da d'an banzan surutu, don dai Faruk ba ya sakar mata fuska ne, da ya sha hira.
Sai da ta gutsiri kusan rabin ayaba ta saka a bakinta sannan ta juyo tana shirin masa magana, hannu ya d'aga mata tare da mikewa tsaye yana fad'in "masallaci zan je yanzu, sai dai ki bari sai na dawo, kafin nan kin cinye abinda ya ke bakin ki". Don ya tabbatar idan ya cigaba da kallon yadda bakinta ya dame da ayaba hakan zai iya barazanar sa shi tashin zuciya, wanda zai iya kai shi da yin amai, don dai Faruk akwai shi da k'yank'yami tun yana yaro, hakan yasa ya dade yana neman macen da ta dace da ra'ayinsa amma Ummansa ta yi gajen hak'uri ta had'a shi da 'yar aminiyarta, wadda bai da tabbacin yadda yarinyar take, tun da ba a gari d'aya suke ba.Su Faruk suna kano, su kuma su Nadeeya' yan jigawa ne, kuma ita umman Faruk ba zuwa take yi ba, ummansu Nadeeya ce ke yawan zuwa, ko idan an yi hutu ta turo su Nadeeya.
Dan k'awancen na su dad'add'e ne, ya samo asali tun lokacin da suke boarding school na dala,
Da yake masu son xumunci ne sai ba su watsar ba,amma Faruk kam bai ma ta6a zuwa jigawan ba, sai ranar d'aurin aurensu.

Don ko lokacin da aka saka bikinsu, ba wani zuwa gurin ta ya ke yi  ba, sa dai ya yi ta tura musu kud'i hakan ya saka ba su damu da sai ya zo ba. Nadeeyan ce ma mai damuwa don gaskiya tana tsananin son Faruk, sai dai kash bata san hanyoyin da zata bi don shawo kansa ba, a maimaikon haka sai ta sa a ranta ai da an kawota gidan sa shi kenan dole ya sauko ya bi ta, sai dai abinda ya ba ta mamaki ko bayan aurensu ba ta chanza zani ba.

Don haka ta tattara shi ta watsar, sabgar gaban ta kawai take yi, a cewar ta burin ta ya riga ya cika tun da ta aure shi.

Da wannan tunanin ya fice daga gidan ba ki d'aya, zuciyarsa cunkushe da tunanin wannan wace irin mace ce????
Aure ko wata 3 bai yi ba, amma ya fara Karo da matsaloli, gaskiya Nadeeya kwata_kwata ba ta dace da shi ba, don ta ko'ina ba ta yi kala da matar da ya ke muradin aure ba.

Don aurenta ya d'auke sa, a matsayin k'addara ce kawai, don akwai shi da biyayyar iyaye musamman mahaifiyyarsa da ita kadai ta rage masa sai k'anwarsa....


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪6&7

©MRS SAIF
                  ®NWA

Bayan sun idar da sallah, ya fi k'arfin 30mnts yana zaune a parlor yana jiran Nadeeya ta kawo masa abincinsa, amma shiru ka ke ji, sai da ya lek'a d'akinta don ya sanarda ita ta kawo masa abinci, tunda ita kwata_kwata ba ta san abinda ya da ce.
Turus ya yi bayan shigar sa d'akin , yana duban abinda ke gabanta, taliya ce a gabanta wacce ake kira shar6u take kwasa, kusan rabinta duk ruwa ne, ga shi ta kwasota za ta kai baki ruwan taliyar har yana tsiyaya ta tsintsiyar hannunta.
Bud'e ido yayi yana kallonta, tare da fad'in "amma ni dai ba wannan abincin ki ka dafa da ni ba ko"???
Ita ma kallon nasa ta yi, tana cewa"au dama har wani dafa abinci ake kashi_kashi???
Ta cigaba da fad'in" tab! Wai aiki, don yau ka ji dad'i ma ban yi tazarce ba, don na ji ina son cin jaloup d'in taliya, shi yasa kk wannan maganar."

Dafe kan sa yayi, yana fad'in "yanzu kina nufin wannan k'azamain abincin zan  ci "???
K'ara sul6ar taliyar ta yi, sannan ta ce" ni fa ban ce dole ba, idan ka ga xa ka iya ka ci, idan ba za ka iya ci ba, ka bar shi ba dole."
Kamar zai yi magana, kawai sai ya shareta ya fito daga d'akin.
Kitchen ya nufa ya hada tea ya sha don yunwa ce fal cikinsa, don yau bai samu ya ci abinci a office ba, saboda ayyukan da suka saka shi a gaba.

Tun asuba da ya tashi bai koma barci ba, don da wuri yake son fita, don haka da kan shi ya shiga kitchen ya d'ora ruwan zafi, don ya tashi Nadeeya ya kai so uku ta k'i tashi, tea dai ya kuma had'awa ya sha, a ransa yana cewa "shi bai ga amfanin auren da ya yi ba , har gwanda lokacin da yana gidansu sau dubu."

Har ya kusa gama shiri sannan ya jiyo,, katuwar hammar Nadeeya alamun ta tashi, k'amshin turarensa ne da ya cika gidan ya tabbatar mata da ya gama shiri don haka cikin azama ta diro daga kan gado ta yo waje, dai_dai lokacin Faruk ya fito sak'ale da jakarsa alamun ya gama shiri zai fita.

Kallo d'aya ya mata ya d'auke kan sa duk ta yi wani dagaje_dagaje da ita kamar wadda aka k'wato a bakin kura, gashin kan ta duk ya wani cukurkud'e, haka idonta duk kwantsa ya cikasa, bakin ta taf yawun barci take shirin yi masa magana, da sauri Faruk ya k'ara wuta zuwa k'ofar fita, yana fad'in "akwai kudi na nan na ajiye miki akan stool, ko da za ki yi wani amfanin".

Yana k'arasa maganar ya fice da sauri, don baya son cigaba da kallon yanayin da take ciki, don hakan yana haddasa masa tashin zuciya...........

Maman Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪8_10

©MRS SAIF
                       ®NWA

Dama ita Nadeeya saurin da take yi, don ta kar6i kud'i ne, kafin ya fita, don haka Jin ya ajiye mata kud'in ya sa, ta shige toilet ba tare da ta kuma bi ta kansa ba.

Faruk kuwa driving ya ke, amma hankalinsa gaba d'aya baya kai, yana can yana tunanin halin da ya tsince kansa, a zuciyarsa yana cewa "wai yanzu a haka rayuwarsa zata cigaba da tafiya da wannan yarinyar"????

Tambayar da yake ta nanatawa a zuciyarsa kenan, sai dai kash ya kasa samo amsar tambayarsa, tunawa da yayi yanda mahaifiyarsa ke son aurensa da Nadeeyar , yasan ko giyar wake ya sha ba zai tinkareta da maganar rabuwa da Nadeeya ba.
A haka ya yi ta sak'a da warwara har ya iso office d'in su, don haka ya yi parking ya fito da zummar shiga ciki.

Nadeeya kuwa bayan ta gama dak'ilanta, fitowa ta yi ta chanza kaya don a cewarta sanyi ya yi yawa ba zata iya wanka ba, kayan ma da ta chanza don tana son fita ne, da zaga mak'ota ne, don gaskiya ta gaji da zaman gida, tunda ta ga maman Twins ta su bata zo d'aya ba, don da ta shiga gidanta za ta fara kawo mata zancen girki, ko gyaran gida ko jiki, ita kam kwata_kwata basa cikin tsarinta, don haka ta yanke shawarar watsar da ita kawai ta nemi wata mak'ociyar, wadda ta su zata zo d'aya.

Haka Nadeeya ta fara shiga gidajen mak'ota daga wannan gida zuwa wancan, har ta fad'a gidan maman Nabeela, tun daga k'ofar gida take jiyo shewa da raha na mata, tamkar gidan biki, da sauri ta kutsa kan ta cikin gidan tare da sallama, kusan a tare suka amsa mata sallamar.

Sannan wata mata dake zaune a tsakiya (wadda ga dukkan alamu ita ce mai gidan) ta ce "ah! Sannu da zuwa bak'uwa muka yi"???
Gyd'a kai, Nadeeya ta yi tare da cewa"eh, ai ni ce amaryar can gidan mai red d'in gate, na kusa da gidan Maman Twins".
Gaba d'aya suka d'auki gud'a suna cewa"ki ce amaryar ce "???
Mai gidan ta amshe da cewa"ai mun yi fushi sai yau ki ka shigo mana, ta k'arasa maganar cikin sigar zolaya".
Wata dariya Nadeeya ta saki don ganin cewa lallai yanzu ta samu abokan sha'ani don daga ganin su za a daki chafta da su, sannan ta ce "a yi mun afuwa yanzu ai gani na zo".

Dariyar dai suka kuma yi, sannan aka bata wurin zama ta zauna, aka cigaba da hira, wadda hirar ta su, duk akan maganin mata ne, daga maganar sa mai gida tsalle, sai sa mai gida ihu, sa mai gida kururuwa, kai har da sa mai gida hauka lol, ga sunan dai birjik, dama Nadeeya ta samu abinda take so, anan aka yi mata tallan wasu, ta kwasa, don kud'in da ta fito da shi sai da ya k'are tas, har sai da aka biyota bashi.

12 na rana matan suka fara watsewa, don komawa gida, daga wadda za ta ce, ba ta yi wanke_wanke ba, sai wadda zata ce yaranta sun kusan dawowa daga school ga shi ko girki ba ta d'ora ba. Wata ma ko tsinke ba ta d'aga  a cikin gidan na ta ba, amma ta fito yawon mak'ota, irin su Nadeeya kenan.

A gaban idonta matan nan suka watse duka, maimaikon ta yi haramar tafiya ita ma, ai sai ta gyara zama, su ka d'auki wani sabon shafin hira, suna hirar matar(wadda ake kira da maman Nabeela) na kiciniyar d'ora girki.
Idan ka gansu da Nadeeya sai ka rantse da Allah sun shekara a tare, saboda sabon da suka yi lokaci d'aya.

 ************

Nadeeya ba ta bar gidan ba sai bayan la'asar, don anan ta ci abinci rana.
Faruk kuwa 5pm ya yi shirin barin office, direct gidan su ya nufa, don yana son ganin  ummansa da 'yar k'anwarsa Fateema.


Waye Faruk?????
Umar Faruk Sadauki, shine cikakken sunansa, mahaifinsa haifaffen garin kura ne ta cikin jahar Zamfara, wanda aka fi sani da Aliyu Sadauki, ya dawo kano da zama ne sanadiyyar kasuwanci, inda anan Allah ya hada shi da matarsa wato mahaifiyarsu Faruk hajiya Aysha, sun yi auren so da k'auna, sun kuma yi zaman Jin dad'i, wanda Allah ya azurta su da yara biyu rak, Umarul Faruk da Fateema Zahra, kafin daga bisani Allah ya kar6i ran Alhaji Aliyu.
A lokacin Faruk yana level 3 a university, Fateema kuwa tana j.s.s 2, saboda haka ummansu ta cigaba da kulawa da su har zuwa lokacin da Faruk ya gama karatu ya fara aiki, wannan kenan......


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪11&12

©MRS SAIF
                  ®NWA

Da sallamarsa ya shiga parlourn gidan, da sauri fateema ta taso tana masa sannu da zuwa, tare da fad'in "bro jiya throughout ban ganka ba mun yi missing d'in ka fa ".
Murmushi ya k'ara fad'ad'awa a fuskarsa, sannan ya rik'o hannunta yana cewa "I miss yhu more lil sister, nd ina Umma ta shiga ne, ban ji motsinta ba".
Fateema ta ce "yanzun ta shiga d'aki, ina tunanin wanka ta shiga don ba ta dad'e da dawowa daga unguwa ba".

Faruk ya ce "ok, sannan ya nemi d'aya daga cikin kujerun parlourn ya zauna.
Bayan 10mnts Umma ta fito tana fad'in" Faruk kai ne da yamman nan"???
Sosa kai ya yi, sannan ya ce "eh, umma ina wuni"???
Lafiya Lau, ya Nadeeya take???
Sai da Faruk ya d'an 6ata fuska sannan ya ce" lafiya".

Umma ta dad'e tana nazarin halin da yake ciki kwana biyu, don duk ta ga ya chanza, ta san tabbas akwai abinda ke damunsa, da ta fiso sai ya fad'a da bakinsa, amma zuwa yanzu ta san ba lallai ya fad'a mata abinda ke damunsa ba, don ta san halin Faruk sarai.

Maganarsa ce ta dawo da umma daga tunanin da take yi, yana cewa "wai umma mai ku ka dafa ne yau"???
D'an zaro ido ta yi tana cewa, haba Faruk idan ka cika cikin ka, anan ka je gida ba ka ci abinci ba, Nadeeya ba zata ji dad'i ba fa????
Ka san matan yanzu wayau ne da su, basa so su ga mazajensu na cin wani abinci idan ba na su ba".

Mere baki ya yi, a ransa yana cewa wadda ta san kanta ba, amma wannan BALLAGAZAR MACEN, ai ba ta san da haka ba.
Shirun da umma ta ji yayi ne, yasa ta ce "Faruk anya babu matsala a zaman na ku kuwa???
Shiru ya kuma yi, don har ga Allah shi ba mutum ba ne mai kai k'orafi ba, amma yasan tunda har ta tambaya to dole ya gaya mata, idan ba haka damuwa zata saka a ranta.
Don haka nan take ya juyewa umma abinda ya ke faruwa, duk da ba ta ji dadin abinda ya fad'a ba, amma sai ta ce "Faruk na san halinka yanzu haka, ba ka tsaya ka yi mata bayanin abinda ba ka so ba da wanda ka ke so ba ".

*************

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce
"haba umma, yanzu a ce har tsabtar jikin ta sai na gaya mata ta yi, na d'auka duk a gidansu za a sanarda ita komai ai".
Girgiza kai umma ta yi, tare da cewa
"abinda na ke nufi, ba ka zaunar da ita ka gaya mata irin abincin da ka ke son ci ba, tunda a maganarka ka nuna ra'ayinta kawai take bi wajen girka abincin".
Kallon umma ya yi sosai sannan ya ce
"umma ni fa yanzu ba ma ta abinci na ke yi ba, ta tsaftar jikinta da ta gidan na ke yi, yanzu haka zancen da na ke miki akwai kwanikan da sun fi sati ba su ga wanki ba, parlourn mu kuwa bana Jin tana sharewa bare mopping."


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪13

©MRS SAIF

               ®NWA


Ajiyar zuciya umma ta sauke tare da fad'in
"bari zan je gidan na sameta na nuna mata duk abinda ya dace, tunda ka ga bata da kowa a garin nan, ni ce a matsayin mahaifiyarta, amma na yi mamakin faruwar haka, don na san Nadeeya akwai hankali".

Hmm! Kawai Faruk ya ce don yasan umma ba ta ta6a ganin laifin Nadeeya, mik'ewa ya yi da zummar zuwa masallaci don ya ji ana ta k'wala kiran sallar magrib, sannan ya ce da fateema ta had'a masa kayan abinci kafin ya dawo.

Yana dawowa ya tarar da lafiyayyen tuwon shinkafa da miyar egusi, wacce ta wadatu da kifi, ai kuwa nan Faruk ya gyara zama ya kwashi girki, yana korawa da mango juice.


********

K'arfe tara ta gama shirinta na shiga mak'ota duk da yau ta tsaya ta yi picking ledojin dake a zube a parlourn, sannan ta yi k'arfin halin kakka6o kujerun parlourn, don duk k'ura ta cika su, kasancewar hazon da ake yi kwana biya, maimakon ta share sai ta bar k'urar duk ta bazu kan tiles d'in da ke parlourn da kan center carpet.

Mayafinta ta jawo ta nufi hanyar fita, sai dai kafin ta k'arasa sai ta jiyo kamar ana buga k'ofa, K'arasawa ta yi tare da fad'in
"waye????
Muryar umma ta jiyo tana cewa bud'e Nadeeya."
Da sauri ta bud'e k'ofar, sannan ta zube har k'asa tana gaisheta, d'ago ta, ta yi tare da rungumeta tana fad'in "lafiya Lau 'ya ta, sannan suka nufi ciki.
Nadeeya ta rasa inda zata saka umma da Fateema don murna, ta kwaso wancan ta d'auka wannan, duk ciki kuwa babu wanda ta girka da kanta, don duk drinks d'in kwali ne da snacks d'in da Faruk ke  ajiyewa,tunda ba iya cin abincita ya ke yi ba.

Murmushi kawai umma ke yi ta ce
"Nadeeya bar shi haka kin ga yanzu safiya ce, sai da muka yi breakfast muka fito, daga nan ma asibiti zan wuce na ga likita, saboda ciwon k'afar nan ya matsa mun".

Duk da umma ta sha mamakin ganin yadda gidan ya fara dafewa, amma hakan bai sa ta nunawa Nadeeya wani abu ba, anan dai ta yi mata nasiha da muhimmacin kula da miji da kuma tsafta.
Sannan kuma ta ce Fateema, ta tsaya ta taya aiki, zuwa anjima idan Faruk ya dawo ya mai da ta gida.

Ai kuwa fateema ta sha aiki ba na wasa ba, don har d'akin Faruk sai da ta gyara, duk da yana d'an gyara abinsa da kansa amma ba kamar gyaran mace ba.
Har da turaren wuta ta kunna, tunda ga sunan a cikin show glass d'in ta birjik, amma ba ta sawa, a salima, Nadeeya ta d'auka don kwalliya kawai ake jerasu.

Ita kanta Nadeeyar sai da gidan ya burgeta, sai sannu take wa fateema.
Fateema kam murmushin yak'e take yi, don can k'asan zuciyarta tana mamakin Nadeeya mace har mace amma sai imani, don idan ka kalli Nadeeya dole ka sakata a jerin kyawawan mata, don fara ce sol sai dai, rashin sanin ciwon kai, da kuma rashin gyara ya na nema ya maida mata farar fatarta zuwa bak'a.

Faruk tun cilla k'afarsa cikin gidan, ya ji wani sauyi ya ziyarci sassan jikinsa, K'arasawa parlou ya yi anan ya yi tozali da kyakkyawar k'anwarsa,tana masa sannu da zuwa da murmushi d'auke a fuskarsa ya ce
"Fatee, ke ce a gidan na mu"???
Ta ce
"yeah ai na dad'e ma bro".
Faruk ya ce
"I see! Ga gida nan sai k'amshi ya ke yi.
Bai k'ara shan mamaki ba sai da Nadeeya ta fito sanye da atamfar super Toronto red, d'inkin ya amshi jikinta, duk da Faruk ba wani son Nadeeya ya ke yi ba, amma sai ya ga ta yi masa kyau sosai.

Fateema kallon yayan na ta, take yi cike da jindad'i, don ta ga ya yaba da wankan Nadeeyar, shi yasa ta takurata,sai ta yi wanka ta chanza kayan jikinta, sannan ta feshe mata jiki da turaruka kala_kala, har kwalliya da daurin d'an kwali duk fateema ce ta yi mata.

Bayan sun ci abincin, wanda shi kan sa abincin Fateema ce ta girka, Faruk ya yi shirin mai da ita gida, Nadeeya ta nace sai ta bi su,Faruk bai yi musu ba suka tafi tare.

10pm suka dawo dukansu a gajiye suke, don haka agurguje suka yi shirin barci, kaitsaye bedroom d'in su suka wuce, dama su Nadeeya an d'irki maganin mata an yi tatil,don haka na kwashi takarduna da alk'alamina na yi waje, don ban sani ba ko sa mai gida hauka ta sha, kar ta rutsa da ni....... Lox



Maman Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪14&15

©MRS SAIF

            ®NWA

Cikin farin ciki Faruk yau ya tashi, don jiya barcin dad'i ya yi, don bai ji wannan tsamin da hamami ba, a jikin Nadeeya komai lafiya suka yi suka gama, don haka da wuri ya shirya ya fice office, bai tsaya jiran Nadeeya ba, don sallar asuba ma, da k'yar ta tashi ta yi.

Don shi kam yanzu ya saba shiryawa kan shi komai, don idan ya tsaya jiran Nadeeya makara kawai zai yi a banza.

Nadeeya kuwa ungulu ce ta koma gidanta na tsamiya, don dama ita ba tama fuskanci inda maganar Umma ta dosa ba, don ta d'auka irin nasihohin da akewa amare ne, umma ta zo ta yi mata na ta, domin tun a dutse gwaggoninta sun mata, ta kuma ji amma ita kam har ga Allah ba ta san ana amfani da su ba, don tun tasowarta ta kan ga ana yiwa amarya wannan k'us_k'us d'in, da ta kira shi marar amfani. (kun ji fa...... Anan ina kira da 'yan uwana mata musamman ' yan mata,masu shirin aure, irin nasihohin nan da ake wa amare kafin akai su d'akin aurensu, yana da kyau ki rik'e su, don akwai hikima a cikinsu, amma fa wadanda ake wa hud'ubar arziki).

Taran safiya bai k'arasa ba, Nadeeya ta yi hanyar zuwa gidan maman Nabeela don k'afarta har k'aik'ayi take mata don jiya ba ta je ba, an sha hira ba ita.

*****
Anan aka sha hira, daga bisani aka yi zancen bikin k'anwar d'aya daga cikin mak'ociyar su, anan fa Nadeeya aka yi uwa aka makar6iya, an ji zancen biki, har da cewa a kawo mata anko zata yi, a cewarta za ta fi jindadin zuwa.
K'arfe 2 ta bar gidan don tana so ta dawo gida ta had'a kud'in ankon sannan ta ba da d'inki ko express ne a mata tunda ta ji an ce bikin wani sati ne.

Sai da ta fara zuwa gurin mai kayan miya ta siya, kafin nan sai da suka yi daru da shi don duk wanda ya saka mata bai mata ba sai ta zare shi, ta ce ya chanza mata,
wai bata son gwalagwaji. Tun yana mata kawaici don ya ga matar aure ce, har suka fara sa'insa da shi, daga k'arshe ta tattara kayan miyarta ta yi gaba.

Daga nan ta wuce wurin mai nama, don kura ce duk neman dake cikin Freezer d'in su ta soye ta cinye.
Malam nama nake so cewar Nadeeya"
Mai nama yace "
na nawa ki ke so"???
Nadeeya ta ce
" na 1k".
Cewa ya yi to, sannan ya fara yanko tsoka yana had'awa da k'ashi.
Sai ko Nadeeya ta ce
"Malam ni fa bana so da k'ashi".
Juyowa ya yi, yana dubanta sannan ya ce
"ni kam bana sai da na sai na had'a da k'ashi".
Tabd'i Nadeeya ta ce
"Ai ni kuwa bana buk'atar kashi, ya ya ke nan??
Mik'o mata kud'in ta ya yi tare da fad'in
"sai ki kara gaba, don ko uwata da k'ashi take miya".

Maimakon Nadeeya ta k'yale shi, ta wuce abinta, ai sai ta  ce
"yo ni ina ruwana dan uwarka tana miya da k'ashi, sai aka ce Maka ni ita ce"??
Kuturu da kud'in sa, alkaki sai na k'asan kwano,ta k'arashe maganar tare da murgud'a baki.
A zafafe mutum ya yi cikinta kamar zai daketa, yana fad'in
"ni za ki zaga, nan take ya hau d'ura mata ashar, nan fa rikici ya kaure, suka hau d'ure_d'uren ashar, kan ka ce me mutane sun fara taruwa, dak'yar abokan sana'arsa suka ja shi, ita kuma Nadeeya ta kwashi ledar kayan miyan ta sai gida, naman da ba ta siya ba kenan.


Koda ta koma gida damuwa ce fal cikinta, ga shi ba ta siye naman ba, yanzu haka zata yi girkin ba nama, ga yunwa sai nuk'urk'usarta take yi, don yau ba ta tsaya cin abinci a gidan maman Nabeela ba.

Don haka ta yanke shawarar d'ora farar shinkafa ta ci da mai da yaji, don haka ta kuma rufe gida ta je neman barkono, ba ita dai ta gama dafa farar shinkafa da dakan ya ji sai bayan la'asar, don haka ta ce ta huta a ci har dare.
Shi kan sa mai gidan mai da yaji zai ci idan ya dawo a tunanin Nadeeya ke nan, ba ta san Faruk ko abinci ya fiye ya ji ba ci yake ba, bare tsurar farar shinkafa......


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: [8/10, 10:42 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪16

©MRS SAIF

                  ®NWA

Bayan ya dawo ya yi wanka ya huta, ya buk'aci Nadeeya ta kawo masa abincinsa, nan da nan kuwa ta tashi bazar_bazar ta nufi kitchen, ba jimawa kuwa, ta kwaso kayan abincin ta dire a gabansa.
Shinkafar ya fara bud'ewa sannan ya ce
"Ai ba ki kawo miya ba."
Sai kuwa Nadeeya ta ce
"au ba ka ga yaji a leda ba, sannan ga mai nan a waccen robar".
Juyowa Faruk ya yi yana kallonta ya ce
"uhhm! Sai yaya!"???
Sai ko Nadeeya ta ce
"sai ci".
Tsaki ya ja, sannan ya ce
"wai don Allah me ke damunki ???
Ta yaya za ki kawo mun, mai da yaji da daddaren na ci?? Gaskiya ya kamata ki gyara".
Nadeeya shiru kawai ta yi tana harare_harare.
Mik'ewa ya yi, yana cewa ki samu wani abun ki kawo mun na samu na ci amma ba wannan ba".
Ta ce
"kamar me kenan??
Yace
"ke ba mace ba ce???
ai kin san abinda ya dace a ce na samu na d'an ci kafin na kwanta".

Dogon tunani Faruk ya saka Nadeeya, amma a iya tunaninta, ba ta gano abinda za ta kawo masa ba, don gaskiya ita kam yanzu ba za ta iya wani d'ore_d'oren girki ba.
Don haka ta je ta ce masa ita gaskiya ba ta san abinda zata kawo masa.
Ce da ita kawai ya yi ta je ta kawo masa fresh milk da cake, don yasan ko ta kuma yin wani girkin ba lallai ya iya ci ba.
Ko da kuwa ta dawo fresh milk kawai ne a hannunta, ta fara magana tare da sosa kai
"Ai......da dama ina so na gaya Maka kusan komai ya k'are fa".

Kallonta Faruk ya ke yi tare da nazarin maganarta, ya ce
"wai kina nufin komai ya k'are"???
Gyd'a kai ta yi, tare da cewa
"har kayan abinci, suma sun kusa k'arewa".
Don kuwa kullum za ta yi girki da yawa take girkawa, har yau ta kasa  kwatanta dai_dai cikinsu, ko na ce cikinta,tunda kusan ita kadai ke ci, sai dai ta dafa da yawa, idan ta samu almajirai ta basu idan ba ta samu ba ta zuba a shara, shi yasa tun daga wajen gidan bolar su ke wari.

Da hannu Faruk ya mata inkiya ta tafi kawai, sannan ya dafe goshinsa da hannu,, yana jimamin hali irin na Nadeeya.

Daga k'arashe ya zari key d'in motarsa ya nufi eatery, duk da shi ba gwanin cin abinci a eatery ba ne, tun yana saurayi, don ummansa ta k'ware a girke_girken da ya ke so.

Sai ga shi yanzu da aurensa zai fara bibiyar wurin cin abinci sanadin BALLAGAZAR MACE.....


Mum Twins 😘
[8/10, 10:42 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪17

©MRS SAIF

      ®NWA

Washe gari kuwa wuraren 12 na rana ya dawo gidan don kawo kayan abinci, sai dai ko da ya dawo Nadeeya ba ta nan an fita gantali, don haka sai da ya kirata a waya, sannan ta zo.
Ai kuwa Faruk ya nuna mata 6acin ransa don kuwa ba ya son yawo, don ya tsani gantalin da mata ke yi a wasu unguwanni.
Sai ka ga mace ba za ta zauna a gidanta ba, sai dai kullum tana garari a cikin unguwa bata gidan waccan ba ta gidan wannan daga nan sai tsegumi ya yawaita.
To shi kam ba zai d'aukan mata yawo ba.
Don haka yace da ita kada ta sake fita ba tare da izininsa ba.
Nadeeya kad'a kai kawai ta yi, amma ba mu sa ni ba ko ta ji???
Sai dai mu jira amsa nan gaba.

Bayan ta shige cikin gidan ne, ya bud'e boot ya fara fitowa da kayan da ya siyo, yana ajiyewa a parlor buhun shinkafa ne da cartons na taliya da macaroni su sugar milk, drinks da dai sauran kayan amfanin gida.
Ya d'auko ledar kajin da ya siyo da kifi, yana mitar cewa dole ma ya samu yaron da zai rik'a taya shi wani aikin, don yanzu ko shigo da kayan nan aiki ne, ga shi yanzu sai ya je zai kuma d'ibansu zuwa store.

Maganar zucin da yake yi ne ta tsaya cak, sakamakon K'arasawa da yayi cikin parlourn, mamaki ne k'arara a fuskarsa, wai ana nufin Nadeeya har ta kwashe kayan da ya shigo da su har da buhun shinkafa????
Kallon da ta ga yana mata ta d'auka ta birge shi ne, abinda ta yi, shi yasa sai wani d'ashe baki take.

Zubewa ya yi a kujera yana tunanin wannan wace irin mace ce, komai na ta sangangan kamar namiji, shi da yake son mace mai aji, da yauk'i, wacce ta amsa sunan mace..

*******

Furzar da wata iska yayi, ya had'a hannayensa ya murza sannan ya mik'e tare da fad'in
"bari na koma office, akwai ayyukan da na baro".
Bai tsaya jiran mai za ta ce ba ya fice abinsa.
Ita kuwa mere baki ta yi ta fara magana k'asa_k'asa
"umma ta gaida aysha mutum komai aka yi ba a burgeshi".

Faruk kuwa bayan ya isa office ya ji yau, yana sha'awar cin farfesun kifi don yana son shi sosai, da ya yanke shawarar idan ya tashi aiki ya fara zuwa gun cin abinci ya ci sannan ya wuce gida, sai dai ya tuna da Maganar umma akan ya rik'a bata dama tana masa irin girkin da ya ke so.
Don haka ya kira Nadeeya a waya ya shaida mata abinda ya ke so ta dafa masa.

Bari mu ji yanda girkin Nadeeya zai kaya lol............. Dama macaroni ta yi niyyar dafawa da miya, ta d'ora ruwan zafi kenan Faruk ya kirata, don haka ta ce hutarere ba sai ta yi miya ba, sa ta yi farfesun kifin tunda miya ai duk miya ce, a ci da macaronin.

Kifin kuwa wanke shi kawai ta yi sama_sama, ba maganar ko d'an lemon tsami ta saka wurin wankin don ya kashe k'arnin, haka ta watsa shi a tukunya ta had'a kayan miyanta ta yi blending har da tomoto ta watsa, ba a maganar a soya kifin kafin had'a farfesun, bare maganar wani kayan k'amshi, gaba d'aya ta had'a komai da komai ta d'ora.

Bayan ya dawo Nadeeya sai wani yak'e baki take yi ita a lallai yau ya bata aiki ta yi, tasan dole yau ta burge shi. Don haka nan da nan aka kawo masa abinci.

Yana bud'ewa kuwa wani k'arni ya dake hancinsa, kamar ya maida ya rufe sai dai ya ce bari dai ya ci ya ji, don kar ya sare mata guiwa, tun da ya d'auko salar tsokar kifin ya ke Jin wani santsi a jikinta, duk da haka ya daure ya tura baki, ai kuwa da sauri ya mike yana kakarin amai ya nufi toilet, nan ya fara kwara amai, don bacin kifin da ya ci, har d'an abinda ke cikinsa duk ya amayar, dawowa parlourn ya yi ya zauna.

Nadeeya ta kalle shi cike da tsiwa ta ce
"yanzu abincin nawa muninsa har yakai ya saka ka amai???? "
Kallonta ya yi a kasalance ya ce" ki fara ci ki ji kafin ki yi k'orafi.
Tace
"ci na nawa kuma???
Ai wanda na ci ya fi wanda na kawo Maka yawa.
Kalon ban yarda da abinda kika ce ba ya watsa mata.
Ganin haka yasa ta d'auko kwanon farfesun ta ajiye ta zauna ta fara kwasa har romon, ita ke sha Faruk ke ya tsine fuksa, daga k'arashe ya tashi, ya bar wurin, yana matukar mamakin Nadeeya tabbas ta wuce duk tunaninsa, ta wuce mazaunin inda ya ajiyeta.

Don shi a tunaninsa d'an Adam ba zai iya cin wannan farfesun da ta yi ba , yanda ya ji shi a bakinsa sai wani mugun santsi kamar an sa sabulu ga shi bai dahu ba, sai zallan zak'in farin magi ke ta shi.....


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪18

©MRS SAIF
               ®NWA


Washe gari, ko da Faruk ya tashi ransa duk ba dad'i, haka dai ya shirya zuwa aiki, don ko d'an ruwan tean da ya saba sha yau bai sha ba, sai wurin 12 ya samu sukunin zuwa pizza hot, ya d'an samu abinda ya saka a tunbinsa, don ji yayi har ya fara Jin wani jiri_jiri, saboda yunwa.

Dan haka da ya tashi daga office, sai da ya fara zuwa gidansu ya ci abinci sannan ya wuce gida, ummansu tana ta tambayarsa lafiya ta ga duk ya fad'a, bai ce da ita komai ba illah ba ya jindadi kwana biyu.
Ta masa Allah ya sawwak'e, sannan ya fito daga gidan.

Nadeeya kuwa tana can tana sak'a da warwara, ta yanda zata 6ullowa Faruk ya barta ta je biki, don gobe ne kamu, don haka ta yanke shawarar zuwa ta gaya masa.
Ko da ta shiga d'akin sa yana zaune yana wani aiki a laptop d'in sa.
Sallama ta yi sannan ta nemi wuri ta zauna, sallamar kawai ya amsa mata, ba tare da ya kalleta ba. Sai kuma ta fara magana
"Faruk dama ina so na gaya maka gobe akwai bikin da za mu je".
Kallonta ya yi yana mamakin bikin wa za ta je, tunda yasan ba ta da kowa a kano duk danginta suna dutse. Don haka ya mai da hankalinsa ga laptop d'in dake gabansa yace "bikin wa kenan'????

Gyara zama Nadeeya ta yi, sannan cikin inda inda ta ce
" eh.... ai dama akwai wata mak'ociyar mu ce, za a yi bikin k'anwarta".
Bai d'auke kan sa daga aikin da yake yi ba, ya fara magana
"anan kusa da mu ne za a yi bikin???
Sai kuwa ta amshe cikin zumud'i don ta ga alamar kamar zai barta, ta ce
"Ai yayar amaryar ce a layin su maman Nabeela, nan k'asan layin mu suke, amma a gidan iyayensu da ke kurna za a yi komai na bikin".

What!! Faruk ya fad'a sannan ya ce
"kin san nisan da ke akwai daga nan zuwa kurna kuwa???
Turo baki ta yi tare da cewa
"ni ina zan sa ni, ni kawai izini na ke buk'ata, gobe mu je ka ga na gano daga can".
Kaitsaye Faruk ya ce
"ba za ta je ba".
Dan zaro ido ta yi ta ce
"ba zan je ba????
Gyd'a mata kai ya yi alamar haka ya ke nufi.
K'wafa ta yi, sannan ta mik'e ta fita tare da Jan k'ofar d'akin da k'arfi ji kake garam!!

Rufe laptop d'in ya yi, ya jingina bayansa da kujerar da yake kai, sannan ya lumshe ido yana tunanin matsaloli irin na Nadeeya.

Nadeeya kuwa ta k'udirci aniyar ko za a mutu, sai ta je bikin nan, don ba za ta yi anko a banza ba,tunda yanzu idan ya fita tun safe sai wurin 9pm ya ke dawowa, don haka har ta je ta dawo bai dawo ba.

Ba ta san ita ce silar saka Faruk dadewa bai dawo ba, don idan ya tashi daga aiki sai ya fara zuwa gidan abinci ya ci, ko gidan su, ko abokanansa su ja shi zuwa na su gidan musamman aminin sa Abbas, don matar sa tana da hankali yana sha'awar yanayin zaman su.

K'arfe biyun rana suka isa  gidan bikin, Nadeeya an sha anko ta fito cas kamar ba ita ce k'azamar nan ba. Ai kuwa Nadeeya ta kira wannan fitar da farar tafiya don ta had'u da friends d'in ta da suka yi secondry school tare dama su 'yan Kano, amma GGSS Darki suka yi dake jigawa.
Nadeeya  ce ta fara shaida su, cikin tsananin farin ciki ta nufi kujerun da suke zaune tana cewa
"wai Samee da Zee na ke gani ko ido na ne???
Cikin mamakin Jin an kira sunan su, suka jiyo a tare, ido suka zaro tare da fad'in " Nadeeya!!"
Nadeeya kuwa sai murmushi ake zabgawa, sannan d'aya daga cikin su mai amsa sunan Zee, wadda daga gani tafi d'ayar felek'e da iyayi ta ce
"it's been far too long, kamar ba ke a duniya, ko neman mutane ba kya yi, ga shi muna yawan zuwa dutse, don dai ba mu da adress d'in ki ne da kin gan mu".

Kujerar da ke gefensu ta ja ta zauna, sannan ta ce
ai kar ku damu don kuwa yanzu muna tare domin nima na zama 'yar kano, don aure ya riga ya kawo ni da zama".
Shewa suka yi sannan suka ce
"a lallai kuwa muna tare".
Anan dai suka yi exchanging contact, tare da yiwa Nadeeya alk'awarin zuwa, tunda ba su da wani nesa a tsakaninsu.


Faruk kuwa bayan ya tashi daga aiki, haka kurum, yau ya ji baya son zuwa ko ina, don haka ya d'au hanyar gidansa, sai dai ya tsaya 212 Bakery ya siye bread na breakfast da cakes varieties ya wuce gida.

6:30pm ya shigo gidan, bayan yayi parking ne, ya k'arasa k'ofar parlourn yana knocking amma shiru ba alaman za a bud'e masa, mota ya koma ya d'auko extra key da ke hannunsa ya bud'e, yana cewa a ransa yanzu haka barci take yi.
Sai dai har yayi wanka ya shirya bai ji alamunta ba, don haka ya yanke shawarar lek'awa d'akinta ya gani ko lafiya, tura k'ofar d'akin ya yi ya shiga, sai da wayam bata ciki, sai wani uban hamami dake welcoming nasa, wani dogon numfashi ya ja, don ganin d'akin a hargitse kamar na tsohuwar mahaukaciya, ko ina kaya ne a zube, still d'akin ya ke bi da ido, don shi rabon da ya shigo d'akin nata har ya manta, to mai zai zo ya yi???
Bayan ko d'akinsa ta shiga Allah Allah ya ke yi ta fito, don ji yake duk shak'ar d'akin nasa ya chanza.

Ya fi 3mnts a tsaye, sannan ya yanke shawarar lek'awa toilet, sai dai tura kan sa ke da wuya cuki toilet d'in ya banko k'ofar tare da toshe hanci, sai da ya fito parlour ya saki numfashi tare da zubewa kan kujera, don yasan tabbas ta je bikin da ya hana ta zuwa, idan kuwa haka ne lallai yau zata ga 6acin ransa....


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪19&20


©MRS SAIF
                 ®NWA

Wayarsa ya ciro daga aljihunsa, ya danna kira a no Nadeeya, dai dai lokacin su Nadeeya na ak'ilun neman adaidaita, ta ji wayarta na ringing, sunan da ta ga ya bayyana kan screen d'in wayar ya sa ta ji cikinta ya murd'a, don duk tsiwarta tana Jin shakkar Faruk.

Kasa d'auka ta yi, har wayar ta tsinke, bai dad'e da tsinkewa ba, wani kiran ya shigo, gabanta ne fa ya shiga dukan uku_uku don dai ta tabbatar da Faruk ya dawo gida, tunda ta ga kira haka a jere.
Sai a kira na uku, Hafsat (wadda ake bikin k'anwarta tata ta ce da Nadeeya,
"ki d'auka mana sai kiranki ake yi, yanzu haka mai gidan ne, ai sai ki gaya masa wahalar abun hawa ake yi, har yanzu muna tsaye a titi ba mu samu ba".

Ajiyar zuciya Nadeeya ta sauke, a ranta ta ce
"don ba ki san ba da saninsa na fito ba shi yasa ki ke wannan maganar".
Faruk kuwa ya cika yayi fam, wato wayar ma bata da lokacin d'agawa???

Har ya je sallah ya dawo ba alamar Nadeeya, don haka ya sake kiran wayarta, cikin k'arfin hali Nadeeya ta d'aga ta ce
"hel..... Faruk ya katseta a zafafe da fad'in
"ki tsaya a gidan bikin, ba na buk'atar dawowarki", daga haka bai kuma cewa komai ba, ya katse wayar.


******
Nadeeya ta yi sakato da waya a hannunta, a ranta ta ce
"yanzu ya zan yi???
Da daddaren nan dai ko giyar wake na sha bazan nufi dutse ba, sannan tunda ya ce kar na nufi gidansa gwanda kar na koma, don dama ba na gabansa, kar ya je ya mun wulaqancin da ko kare ba zai ci ba.

Don haka ta yanke shawarar wucewa gidan su Faruk d'in, sai dai ta san a Rijiyar zaki suke, amma ba ta san yadda zata kwatantawa mai adaidaita sahu ba, tunda ita ba 'yar gari ba ce, kuma duk zuwanta gidan tare da Faruk ne.

Tana cikin wannan tunanin, suka samu adaidaita sahu, abokanan tafiyarta, sai kiranta suke yi ta zo, su tafi, anan ta kwashe abinda y faru ta sanar musu.
Hafsat ce ta ce "
Ayya! Nadeeya kin yi shirme ni na d'auka da izininsa ki ka zo,kin...... D'ayar matar da suke tare ta katseta ta hanyar cewa
" hafsat ki zo mu tafi mu kam, kin san dai da k'yar mu ka samu waanna adaidantan, ga shi yana maganar zai tafi idan ba mu tashi tafiya ba".
Ba ta sake cewa k'ala ba Hafsan,ita ma ta shige cikin adaidaita, ya ja suka tafi, suka bar na Nadeeya a titi ita kad'ai.

Ta fi k'arfin 15mnts a tsaye, tana tunanin abun yi, daga baya ta yanke shawarar kiran Fateema k'anwar Faruk, bayan ta kirata ne, take tambayarta kwatancen gidansu, nan da nan fateeman ta sanar da ita, amma sai da ta tambaye ta ko lafiya???
Nadeeya ta ce
"lafiya k'alaau, kawai mun zo biki ne, na ke son k'arasowa na gaishe da Umma".
Duk da k'asan zuciyar Fateema ba ta yarda da maganarta ba, amma sai ta ce da ita "toh,Allah ya kawo ki lafiya".

Cikin sa a ta samu keke napep, nan da nan ya kawo ta, da yake gidan na su ba 6oyayye ba ne har k'ofar gida ya ajiye ta.

Bayan sun gaisa da umma ne, take tambayarta ina Faruk, nan da nan ta juyewa Umma abinda ya faru.
Cikin mamaki umma ta ce
" gaskiya ba ki kyauta ba, Nadeeya ai ita mace da biyyayya aka san ta, shi kuma Faruk ya biye miki da ba ki yi hankali zuwa nan ba ki ka ce garinku za ki wuce da daddaren nan ai da abu bai yi dad'i ba".

Umma har ta d'auki waya za ta kira Faruk sai dai ta ce bari ta bar shi sai da safe, tunda ya saba zuwa gaishe ta kullum, sa yi maganar idan ya zo.

Don haka ta ce da Fateema ta kai Nadeeya ta yi wanka ta bata wani kayan marar nauyi ta chanza sai ta zo ta ci abinci, ta kwanta ta huta.
Nadeeya kuwa cewa ta ke a ranta ita ba wani wanka da zata yi don sanyi take ji, yaushe ta yi wankan da har zata kuma yin wani.

Bayan sun shiga d'akin Fateema ne, take mata maganar wankan, sai ko ta ce
"gaskiya ita ba wankan da zata yi, don sanyi take ji"
Fateema ta ce
"Ai da ruwan d'imi ne".
Ta ce ita fa baza ta yi ba, sanin hali yasa Fateema ta shareta da zancen.
Abincin ma da aka kawo mata tsakura ta yi, sannan ta yi sallah ta nemi lafiyayyen gadon Fateema ta haye sai barci.
Ko da Fateema ta shigo ta tarar tana ta sharar barci, sai dai ta k'udundune da blanket kamar marar lafiya, K'arasawa ta yi bakin gadon da niyyar rage mata bargon, sai dai zafin da ta ji jikin ta ya yi, ya bata mamaki har d'an karkarwa take yi alamun zazz6i ya ci k'arfin ta, da sauri fateema ta janyota jikin ta, tana tunanin to dama bata da lafiya ne, ko kuma yanzu ciwon ya sameta.......????

Afuwan please! posting sai Monday kuma, ina da uzuri ❤❤👌🏻


Maman Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/13, 9:06 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪21


©MRS SAIF
               ®NWA


Girgiza kanta ta fara tana fad'in
"Aunty Nadeeya ba ki da lafiya ne??? Na ji jikin ki zafi rau". Da k'yar Nadeeya ta iya bud'e idonta ta ce
"eh, dama tun kafin ta fito daga gida, ta ji kanta yana mata ciwo, daurewa kawai ta yi ta fito".

Sannu"Fateema ta fad'a tare da ajiye kanta akan pillow ta yo hanyar fita don sanarda Umma, da sauri ta k'arasa wurin da umma ke zaune tana fad'in
"Umma ashe Aunty Nadeeya ba ta da lafiya, ba ki ji yanda jikinta ya yi zafi ba ".
Subhannal! Umma ta ce tare da mikewa tsaye, mu je na ganta".
Ko da suka shiga d'akin itama Umma ta yi mamakin ganin Nadeeya a halin da ta sameta, ta yi ta mata tambayoyin abinda ya kawo mata ciwon nan take, abinda ta gayawa Fateema shi ta kuma maimaitawa Umma.

Saboda haka Umma ta ce
"Fateema ta mik'o mata phone d'in ta dake parlour, da sauri ta hau neman no Faruk, bayan ta kawo mata wayar.
Sai dai an yi rashin sa'a don abu d'aya ake gaya mata, number'n is switched off".
Don shi kam Faruk tunda suka gama waya da Nadeeya ya kashe wayarsa ya saka charging, bayan ya gama abinda ya ke yi, yayi kwanciyarsa don shi kam har ya manta da maganar wata Nadeeya.

Agogon da ke manne a d'akin Umma ta d'aga kai ta kalla, 10:30pm a fili ta ce
"gaskiya dare ya yi, ban son driving d'in dare, da mun je asibiti, amma bari a mik'o miki magani ki sha Insha Allah gobe da sassafe sai mu wuce asibiti".

*******

Haka aka yi kuwa, tun da safe suka yi shirin zuwa asibiti, don ko tabi kan Faruk Umma ba ta yi, suka yi tafiyarsu, sai Fateema da suka bari a gida, ita ma idan ta gama shirinta makaranta za ta wuce.

Sai yamma liki's Faruk ya zo gidan, lokacin su Umma sun dad'e da dawowa daga asibiti.
Nadeeya na kwance akan doguwar kujera, yayin da ta yi matashi da cinyar Umma, sallamar Faruk ta dira cikin kunnuwansu.
Annurin da ya shigo da shi akan fuskarsa 6at ya 6ace, ganin Nadeeya Kane_kane a cikin gidansu, don shi har ga Allah ya gaji, da halin Nadeeya, don shi bai ga amfanin aurenta ba, gwanda mishi zaman sa ba aure,don bai ga abinda auren Nadeeyan ya tsinana masa ba.

Umma ce ta katse masa tunani ta hanyar fad'in "UmarulFaruk tunanin meye ka ke yi ne haka, duk ka wani 6ata fuska kai da ya kamata ace, yau d'in nan kana cikin tsananin farin ciki", ta k'arashe maganar tare da sakin murmushin Jin dad'i.
Cikin rashin fahimtar in da zancen Umma ya dosa Faruk ya ce "Umma wani farin ciki kuma, Allah abinda yarinyar nan take yi kwata-kwata ba ta kyautawa yanzu ya kamata a...... Umma ta katse shi ta hanyar d'aga masa hannu.

Murmushin ne dai d'auke a fuskarta ta ce
" ya kamata ka tsaya ka ji albishir d'in da nake tafe da shi kafin, ka fara k'orafi".
Wuri ya samu ya zauna, sannan ya ce to Umma ina Jin ki.
Umma ta ce
"tun safe muka je asibiti don Nadeeya tunda ta zo jiya bata da lafiya, amma Alhamdulillah rashin lafiyan da ake buk'ata ne, don gwajin farko ya nuna Nadeeya na d'auke da juna biyu!"

Zaro manyan idanunsa waje ya yi tare da mikewa tsaye ya K'arasa wurin da Umma ke zaune ya dafa gwiwowinta ya ce
"Umma da gaske Nadeeya ciki gareta??
Umma cikin zolaya ta ce
"a'a wasa na ke, don sanin yadda Faruk ke da masifan son yara".
Nan da nan kuwa ya 6ata fuska, har sai da Umma ta ji tausayinsa ta ce
"ta ce da gaske ne fa Faruk, nan da wata bakwai ka sa ran d'aukan baby in Allah ya yarda".
Wani irin farin ciki marar misaltuwa ya mamaye zuciyar Faruk, ji yake kamar ya d'auki Nadeeya ya goya don murna.
Sai kuma ya zubawa Nadeeya ido yana tunani
"a ransa da gaske Nadeeya na d'auke da gudan jininsa bai ta6a Jin son Nadeeya ko na second ba, amma yau sai ya ji ta samu wata martaba a zuciyarsa...


Mum Twins 😘
[8/15, 8:06 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪22

©MRS SAIF
®NWA


Anan dai Umma ta yanke shawarar Nadeeya za ta zauna da su, har ta k'ara warwarewa, shi kan sa Faruk ya amince da hakan, sai dai ya ce Fateema ta je ta gyara masa gidan, don gaskiya baya Jin dad'in zaman gidan a yadda ya ke.
Haka aka yi kuwa don dai sai da Nadeeya, ta yi 3wks a gidan su Faruk zuwa lokacin ta warke ras, sai dai ita kan ta Umma d'an zaman da suka yi ta fahimce Nadeeya ba k'aramar k'azama ba ce.
Don haka tayi ta mata nasiha akan tsafta, amma ina wanda ya yi nisa baya Jin kira.

A satin ne kuma ta koma gidanta, k'azanta ta kuwa sabon shafi fal ta bud'e, don irin cikin nan ne mai sa zubar da yawu ke gareta, don haka duk inda ta samu watsarwa take yi, idan ta yi abin arziki ta zuba aleda, amma fa ledar duk inda aka ga dama ajiyeta ake yi daga nan ta tsiyaye guri duk ya dame.

******

Saboda haka Faruk bai ta6a shiga tashin hankali ba irin na wannan lokacin ba, gaba d'aya ya ji ya tsani gidan da duk abinda ke cikin sa, ga shi yana samun k'arin girma da d'aukaka kullum a wurin aikinsu saboda k'wazonsa,don yanzu haka ya siye wani makeken fili a ring road har ya fara gini ya watsar don be ga amfanin saka mace irin Nadeeya a gida mai kyau ba, domin akan matsalar Nadeeya gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa,kullum cikin tunanin mafita yake, abokanansa da dama sun ba shi shawarar ya k'ara aure sai dai gaskiya shi ba shi da ra'ayin mata biyu, don haka yanzu idan ya fita tun sassafe baya dawowa sai kwanciyar barci, don abinci kam ya yafe cin sa a gidan tuni.
Don haka duk wani eatery sabo da tsoho in dai a garin kano yake,Faruk ya San da zaman sa.

Wata ranar laraba Nadeeya ta tashi da rashin lafiya, don haka Faruk ya tsaya tare da ita bai fita ba, don yanzu duk abinda take yi lalla6ata yake don yana matukar tausaya mata albarcin d'an sa dake jikinta.
Nadeeya sai wani narkewa take yi, ita a dole ga mai ciki, ranar Faruk shi ya yi aikin gidan kaf, ya gyara ko ina tsaf abinci ne dai ya fita ya siyo musu.
Ko da ya dawo ya tarar da Nadeeya ta yi bak'i,k'awayentan nan da suka hadu gidan biki, don haka kallo d'aya ya musu ya shige kitchen domin ajiye ledojin da ya shigo da su, don ya tsane duk wani abu da ya shafi Nadeeya, musamman wadan nan 'yan matan daga gani ba su da wata cikakkiyar tarbiyya tun daga yanayin kayan da suka saka.


Su kuwa su zee tun da suka d'ora k'wayar idon su akan Faruk suka dask'are anan, musamman Zainab da da k'yar ta hado wani yawu ta had'iye, body language sukai using tsakaninsu, nan take na ga sun mik'e suna sa6a bags d'in su tare da ce wa Nadeeya
"mu za mu tafi sai mun kuma dawowa kenan"
Itama Nadeeyar mikewar to yi tana fad'in
"haba sameera da zainab, tun yanzu na d'auka sai dare, a tare suka had'a baki suna cewa
"haba mun ce fa za mu dawo, dawowa ta musamman ma kuwa".
Yak'e  baki Nadeeya ta yi alamun ta ji dad'i sannan ta ce
"Allah ya kai mu".
Suka bi ta da "ameen".

Bayan sun fito duban junansu suka yi tare da had'a baki za su yi magana, sai samee ta yi shiru ta ce
"fara fad'an taki maganar tukun".
Zee ta ce
"me za ta ce illah guy d'in can ya tafi da imaninta,don ta ga maza kala - kala, amma gaskiya Faruk na musamman ne kyansa da yanayinsa duka sun mata, ta k'arashe maganar da cewa
"Samee ni fa ya mun 100%,I really luv him with ol my heart, kin san na dad'e ina mafarkin samun namiji irin shi."

Kallon ta samee take yi sosai duk da bata yi mamakin kalamanta ba, tunda ta san halin k'awarta ta ba tun yau ba da son auren kyakkyawan miji, mai kuma ganin gabansa tar, duk da ita ba wani kyau ne da ita ba.
Amma sai ta ce
"yanzu kina ganin ba matsala zee??? Wata kila yana son matar sa, ba lallai ki samu shiga ba".
Wata dariya Zee ta tintsire da ita sannan ta ce
"sai ka ce ba ki sanni be, nd then ki kalli mace kamar jaka a gida, kin san Allah ban yi zaton mijin ta yana nan ba, a yanayin da muka tarar da ita".

Samee ta kar6e da cewa
"ba ke kadai ba, gaskiya yana k'ok'ari,d'an zaman da na yi kusa da ita da k'yar na ke iya had'iye yawu"
Zee ta cigaba "yanda kika san mushe haka take bugawa, kin ga kuwa k'wace goriba a hannu kuturu ai ba zai yi wahala ba...


Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪23


©MRS SAIF
          ®NWA

Ba a rufa sati da zuwan su ba, su ka kuma dawowa sai dai sun yi rashin sa'a don ba su samu Faruk a gida ba, amma da yake 'yan duniya ne sai da suka yi dabara da suka samu cikakken bayani akan sa, daga gurin Nadeeya,don har phone number d'in sa sai da suka sata a wayar Nadeeya.

Bayan sun yi nasarar gano yana aiki ne a federal character, branch d'in su dake Bello road, don haka zee ta ci alwashin daga nan, can za ta nufa.
Faruk yana tsaka da aiki, sai ya ji an ce wai ya yi bak'i, ya yi zaton abokan huld'arsu ne, don haka kaitsaye ya ce
"ace su shigo".

Amma a mamakinsa sai ya ga mata, don haka kallo d'aya ya musu ya d'auke kan sa, don shi ya manta in da ya ta6a ganin fuskokinsu, a dak'ile ya ce
"me ke tafe da ku ne"??
Zee ce ta tashi don K'arasawa zuwa inda Faruk yake zaune sai wani karairaya take, ko ina na jikinta motsi yake, saboda yanayin salon tafiyar da take yi, ga shi wani riga da wando ne a jikinta duk sun dameta, gaban rigar kusan a bud'e yake, kan ta kuwa ya sha kitson attachment wanda ya sauka har gadon bayanta.
Sauke k'wayar idonsa ya yi akan tulin files da ke gabansa, da zummar cigaba da aikinsa, don kallonta ba k'aramin k'ona masa rai ya ke yi ba, don shi tun da suka shigo ya ji ya tsanesu, don sun fi masa kama da karuwan gida.
Maganar zee ce ta dawo da shi daga tunanin da ya ke, ta ce
"Alh Faruk ba ka gane mu ba ne"??
Faruk ya ce ban ma sanku ba,"

Zee ta ce a ranta "daga gani wannan shugaban Jin kai ne, amma a fili sai ta ce
" k'awayen Nadeeya ne, da muka je gidan ku last Wednesday, dama mun yo hanyar nan ne muka ce bari mu zo mu gaisheka". Ta k'arashe maganar tare da kashe masa ido d'aya.
Faruk ya ce
"na gode amma don Allah kar ku kuma zuwa don da mata ta ku ke da alak'a ba ni ba",duk da a ransa tambayoyine birjik yake da su, ta yaya suka samu address na gurin aikin sa, kuma me suka zo yi,duk da sun ce wai gaishe shi suka zo yi, yasan sarai ba haka yake a zuciyarsu ba, amma saboda baya son magana ta tsawaita a tsakanin su yasa kawai ya shanye tambayoyinsa.


Zee har ta bud'e baki za ta ce wani abu ya d'aga mata hannu, sannan ya nuna mata k'ofa alamar su fita, cikin k'unan rai samee ta mik'e, don ita takaici bai barta, ta ce k'ala ba,da sauri ta nufi k'ofa yayin da zee ta biyo bayan ta.


******
A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, don yau ne Nadeeya ta haifi santalelen yaronta,kyakkyawan gaske, ga shi k'ato, Faruk kam yau kamar ya taka rawa yake ji,don farin ciki, in banda hamdala ba abinda ke fita daga bakin sa.

Ranar suna yaro ya ci suna Muhammad amma ana kiransa da Ansar, an sha shagalin suna, don 'yan uwan Nadeeya kaf ba wanda bai zo daga dutse ba.
An yi taron suna an waste lafiya an bar mai jego da d'an ta, sai wata tsohuwa da zata zauna da ita zuwa lokacin da za su yi arba'in.

Sai da suka yi wata biyu cif  tsohuwar ta gangama yana ta-yana ta, ta yi gaba, aka bar Nadeeya daga ita sai halinta. Don kuwa k'azanta yanzu ne ta samu wurin zama, don daga ita har yaron na ta, ba sa shak'uwa don wani irin k'arni ke tashi a jikinsu.
Saboda idan Nadeeya ta saka bra sai ta yi sati bata chanza ba, wanka kuwa tun da ta gama na jego sai ranar da ta ga dama take yi har ta yaron ba kullum ta ke masa ba, ga shi irin yaran nan masu tumbud'i, ga shi Faruk yana masifar son ya ga yaronsa a jikinsa duk likacinta da ya ke gida, amma ina da ya d'auki yaron wani k'arni ke dira cikin hancinsa, a dole yake ajiye shi ya riga masa wasa daga nesa.

Faruk bai k'ara sanin yana cikin babbar matsala ba sai da ta haihun nan, don yanzu tsakanin sa da Nadeeya sai kallo daga nesa, don ko mu'amular auratayya ba ta shiga tsakanin su.

Akwai wata rana lokacin ba su dade da yin arba'in ba, ta d'irki magungunan mata kamar hauka, wai ita alallai tana yiwa mai gida gyara, don haka kan wani lokaci ta hau network mijinta kawai take buk'ata, don haka Faruk bai dade da dawowa ba ta kai tallan kanta.
Haka Faruk ya daure da niyyar faranta mata rai, tun da shi kansa yana buk'atar matarsa.
Amma cusa kan sa da yayi jikin Nadeeya shi ya yi sanadiyyar tarwatsa duk wani tanadin da ya yi, tuni ya saketa ta yi baya, shi kuma ya dafe kansa da duka hannayensa bai an karaba ya ji hawayena na biyo kumatunsa na takaici da tsantsar rashin sanin abun yi, amma dai ya saka a ransa dole ya nemi mafita, tun kafin annakiyar Nadeeya ta kai shi k'asa........



Mum Twins 😘


Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪24&25

©MRS SAIF
            ®NWA


Kwanaki sai dad'a shud'ewa suke yi, amma Faruk ya kasa samun mafita, don duk ta inda ya 6ullowa ummansa ta k'i ganin laifin Nadeeya kullum magana d'aya take nanata masa,shi ne ya yi hak'uri dole wata rana zata chanza, duk da ita kan ta ta sha mata fad'a akan hakan amma ba a samu wani chanji ba.

Yanzu ga shi kusan watan Ansar takwas da haihuwa amma kullum abubuwa sai dad'a ta6ar6arewa suke yi ta 6angaren Nadeeya, ga matsalar k'awarta zee kullum ba ta da aiki sai na kiransa a waya, da bibiyar wurin aikinsa.

Wata siririyar ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in "ya Allah ga ni gareka,, a matsayina na bawanka mai rauni kai ka fi sanin daidai, ya mad'aukakin sarki ya Allah ka kawo mun mafita mafi alkhairi a gareni".

Daidai lokacin ne kuma ya lura da ya kauacewa hanyar da ya ke son bi, sakamakon dogon tunani da ya je, shi da zai karya kwana ya shiga Jan bulo, bai yi aune ba sai ya gan shi kan gwarzo road sosai don ya yi nisa sosai daga kwanar da ya kamata ya shiga.
Da kamar ya yi u-turn ya dawo, sai kuma ya samu zuciyarsa da kimsa masa kawai ya k'arasa BUK ko Fateema ta gama lectures ya d'aukota, sai su taho gida tare.
Straight gate d'in shiga makarantar ya nufa, parking ya yi daidai faculty of science, sannan ya fito daga motar tare da wayarsa a hannu don kiran Fateema ya ji ko ta gama lectures tunda ya ga yamma ta yi.
Kansa a sunkuye yake, yana lalabin number'n tilon k'anwarsa, ta k'asa idonsa ya yi arba da wata kyakkyawar k'afa mai d'auke da zara-zaran yatsu da suka sha jan lallen saajan, d'an mutsutstsuka idonsa Faruk ya yi don ya tabbatar da k'afa ce, ko kuma idonsa ke masa gizo, don k'afar ta fi masa kama da zane ko hoto, don ganin k'afar ya yi tamkar ba a taka k'asa da ita.
Sanyayyen k'amshin turaren 2U ya dake hancinsa hakan ya tabbatar masa mai k'afar tana kusa da shi.
A hankali Faruk ya d'aga idonsa, cikin d'auken ganin fuskar wacce ta mallaki wannan tsaleliyar k'afar.
Karaf! Idanunsu suka hadu lokaci d'aya, da sauri yarinyar ta kawar da fuskarta gefe.


********

Shi kam Faruk ya kasa daina kallonta, for the first time da ya tsaya k'arewa mace kallo a rayuwar sa, yarinya ce wadda shekarunta ba za su wuce 20_21yrs ba, za a iya kiranta da fara amma ba gau ba, sai dai yanayin kyan skin d'in ta shi ke Jan hankalin mutane, sai idanunta masu fizgar hankalin mai kallonsu , tana da hanci dai dai da d'an k'aramin bakinta, za mu iya kiranta da doguwa, wadda tsayinta ya yi dai dai da dirin jikinta.


Sanye take da Arabian gown coffee colour,mai d'auke da adon yellow, yayin da ta yane kan ta da yellow veil, fuskan nan fayau ba wani tarkacen kwalliya sai lipstick da ta zizara a lips d'in ta sai kwalli da ta saka a idonsa wanda shi ke k'ara tona asirin kyaan idanun na ta, ta cikin farin glasses da ta mak'ala a idonta, wanda ga dukkan alamu medical ne.

Tuni Faruk ya daskare a wurin, har ta zo ta ratsa ta gefensa da niyyar wucewa, salon tafiyar ta, shi ya k'ara kambamamata a zuciyar Faruk, yanda ta ke taku cike da nutsuwa da hankali, tamkar ba za ta, taka k'asa ba, wanda wasu za su iya kiransa da yanga, amma samsam a wurin ta abun ba haka ba ne, it's just her nature, saboda tun kafin ta zama cikakkiyar budurwa haka tafiyarta take.


Bai an kara ba sai Jin muryar Fateema ya yi tana fad'in
"friendy kin gaji da jirana ko"???
Murmushi yarinyar ta saki, wanda ya k'ara bayyanar da asalin madarar kyaun da take da shi, tare da cewa "haba friendy sai fa da na ce ki hak'ura ki bar mata buk d'in gobe kya kar6a ki ka k'i ji, bacin kin san maryam da naci". Ta k'ara she maganar fuskarta d'auke da wani Murmushin.
Faruk dake gefe yana kallonsu, sai ya ji kamar kar ta daina magana, don ji yayi kamar tana rera wata daddad'ar wak'a yanda salon maganar ta ta ke fita, dafe ha6arsa ya yi tare da ce wa
"ya ILLah!me yasa yarinyar nan komai ta yi burge ni take yi, duk da ya riga ya gama yarjewa kan sa ya fad'a dumu - dumu cikin k'aunarta.

Ajiyar zuciyarsa, ta yi dai dai da fara tafiyar su don barin gurin gaba d'aya, da saurinsa ya ce
"Fateema"!!
Cikin mamaki Fateema ta jiyo don Jin muryar, yayanta da hanzarinta ta k'arasa gurin da ya ke tsaye tare da cewa
"what a wonderful surprise! Bro kwata_kwata ban lura da kai ba."
Murmushi Faruk ya yi sannan ya ce ni kai na, na san da haka, don na dad'e a tsaye ina kallonku ke da k'awarki, amma ba ki lura da ni ba".
Cikin murna ta koma in da k'awarta ta ke tsaye ta Jawo hannunta tana fad'in
"bro meet my eponym, sweetest,finest friend".
Ido Faruk ya d'an zaro alamun mamaki ya ce
"wow! Yhu mean Fateema is her name too"????
Gyad'a kai Fateema ta yi cike da k'warin gwiwa alamar hakan take nufi.
K'arasawa Fateeman ta yi gun faruk tana gaishe shi, tare da fad'in "ya Faruk, am I right???

Yes! Yes!! Faruk ya fad'a cike da jindad'i, yana tunanin ashe ma ta san shi, har faty k'anwarsa sai da ta fuskanci hakan.
Ta ce
" bro ai ba ka san wani abu ba duk wan da ya zauna tare da ni ko na second ne sai ya san ya Faruk a bakina".
Murmushi Faruk ya ke yi yana Gyad'a kai cike da gamsuwa da maganar k'anwar tasa.

Sai kuma ya ce "ku zo mu tafi ko, kun ga yamma sai dad'a yi take yi".
Fateema ta ce ai kuwa dai bro, sai mu fara sauke friendy a gida sai mu wuce ko"???
Sosai ma kuwa Faruk ya fad'a tare da satan kallon Fateeman.
Dan basarwa ta yi kamar ba ta ji abinda suke cewa ba, sai da faty ta ce da ita
"friendy mu je ko???
Fateema ta ce
"namesake ku yi tafiyar ku kawai na gode, ina ga yaya mus'ab yana hanya za mu tafi tare da shi".
6ata rai teema ta yi ta ce
"haba ta yaya ki kasan yana hanya bacin ban ji kun yi waya ba".
Har fateema xa ta ce wani abu, sai faty ta katseta da cewa
"to wallahi sai kin shiga shi kenan"
Dariya suka yi gaba d'ayan su, saboda fateema tasan halin k'awarta ta idan ba haka ta mata ba, ba lallai ta shi ga ba.

Faruk haka kurum ya tsince kansa cikin farin ciki yayin da ya ke driving, ji yake kamar kar yakai Fateema gida, su yi ta zaman su a haka suna zaga gari, sai dai k'asan zuciyarsa yana mamakin yadda soyayyar yarinyar ta kama shi lokaci d'aya...



Ku yi hak'uri rashin posting jiya yarona ne, ba lafiya amma insha Allah idan na samu kai na, za ku kuma jina ❤👌🏻


Maman Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪26&27
©Mrs Saif


Bayan sun ajiye teema a gidansu ne, Faruk ke ce da Fateema "dama k'awarki ce amma ban ta6a saninta ba"???
Faty tace" ah, ai da yake gaskiya ba ta cika yawo ba, daga gida sai school, amma Umma tasanta, don mun ta6a zuwa sau d'aya da ita ta gaisheta, kuma ina yawan ma Umman hirarta".

Murmushi ya ke yi sosai ya ce
"k'anwata a tsakanin mu ba 6oyeye, so zan gaya miki iya gaskiya ta, ina son k'awarki, ban ta6a tunanin k'arin aure ba, a nan kusa ba, duk rashin cikar da burina bai yi ba ta fuskar auren, sai dai ganin k'awarki nan da na yi, na ji ina son k'arin aure nan ba da jimawa ba, fatana Allah ya sa wani bai riga ni ba".
Ya k'arasa fad'ar maganar da tausayawa kan sa, idan har fateema tana da wanda take so to lailai ya San ya rasa farin cikin rayuwarsa.
Ihun murnar da faty ta saki, shi ya dawo da Faruk daga duniyar tunani, tace "yaya ni dai a iya sani na friendy bata kula kowa, don a cewar ta 6ata lokaci ne, don ita yanzu karatu ta sa a gaba, ka ga kuwa na samu damar kafa gwamnatin yaya na, hankali kwance".


Damk'e hannunta Faruk ya yi sosai cikin farin ciki ya ke fad'in "thank you so much k'anwata, I'm proud of you, don na tabbatar da cewa farin ciki na shi ne na ki".

*********

Fateema tun jiya ta matsu gari ya waye ta je skul ta fesawa Teema abun da ya faru, saboda haka da wur_wuri yau ta shirya ta nufi makaranta, har Umma tana ce da ita ki ka ce yau sai 9 ku ke da lecture, na ga yanzu ko 7 bai yi ba ki na neman fita"???

Sai da ta rataya Jakarta ta ke cewa
"Umma akwai abinda ya taso ne daga baya, shi yasa zan fita yanzu".
Addu'ar dawowa lafiya Umma ta bi ta da ita,sannan ta sa kai ta fice daga gidan.

Teema ba ta isa makarantar ba sai after 8, cikin zumud'i fateema ta je tarota, ba a d'au dogon lokaci ba ta fesa mata abinda ke cin zuciyarta tun jiya.
Murmushi Fateema ta yi tare da cewa
"haba namesake ke fa kin san alk'awarin da na d'auka na ba zan kula ko wani namiji ba, har sai na kammala karatuna,kuma ke kika k'arfafa mun gwiwa, amma yanzu ki zo da maganar ya Faruk"????

D'an 6ata rai faty ta yi tare cewa
"haba friendy yanzu me ye matsalan yayana, wallahi idan ki ka aure ya Faruk za ki ji dad'i, don na fahimci yana matuk'ar son ki, don ni tun tasowata ban ta6a ji ya ce yana son wata mace ba, sai akan ki, kin ga bai kamata ki watsa masa k'asa a ido ba."

Girgiza kai Fateema ta yi tace "ba ki fahimce ni ba ne, ni fa karatuna ne ba zan ajiye ba, na yi aure yanzu, don na san ina amincewa zai fara maganar aure".

Murmushi faty ta yi, don a maganar da suka yi da fateema ta fahimci tana son yayanta, kawai dai ita ta d'auka karatu da aure babban aiki ne shi yasa ta k'i amincewa, don ta tabbatar da zancen wani ta kawo mata a cikin samarin da ke nacin son ta da yanzu sun yi fad'a.
Don haka ta cigaba da nuna mata karatu da aure ba matsala ba ne, kawai ta sawa zuciyarta za ta iya kawai, sai Allah ya taimaketa, ba ta gushe tana bata baki ba, har sai da ta ga ta d'an sauko daga dokin nak'in da ta hau.


Yau kamar yadda ya saba a lokutan baya, k'arfe 6 na yamma ya shigo gidan d'auke da sallama a bakinsa, tsayawa ya yi ya d'an kalleta ya wuce, don inda sabo ya saba, zaune ta ke tana feeding Ansar, amma gaba d'aya boobs d'in ta a bud'e suke, ta yanda  idan yaron ya sha wannan, sai ya juyo ya sha wannan tamkar dai akuya na shayar da d'anta.


********

70:30pm Faruk ya fito cikin shirin sa, da wani tsadaden yadi golden colour wanda aka yiwa ado da zare golden brown, yadin shara-shara ne ta yanda za ka iya hango farar vest d'in sa ta ciki, sai hular da ya kafa akan sa itama golden brown, takalmin da ya saka yayi daidai da kayan, yayi kyau sosai kamar wani sabon ango, k'amshin turaren da ya zuba ne ya tilasta Nadeeya lek'owa ta ga ko lafiya, don gaba d'aya gidan ya k'amshashe kamar wurin kamun amarya.

Ganin yanda ya yi masifar kyau, yasa ta ji wani abu ya tokare mata mak'ooshi, wanda ba komai ba ne, illa kishi, don haka ta sha gabansa tare da rike k'ugu sannan ta ce
"ina zuwa da daddaren nan"????

Ido cikin ido Faruk ya kalleta ya ce
"zance".
Me ka ce"??? Nadeeya ta tambaya cikin k'araji.
Faruk ya ce
"sarai kin ji abunda na ce, don haka I can't repeat myself".
Sai kuwa ta yi bakin kofa da sauri ta saka key ta zare  key'n ta cusa cikin zaninta, wanda garin sauri har d'ankwalinta yana fad'uwa, hakan kuma shi ya tona asirin cukurkud'ad'en gashin kan ta wanda ya fi wata ba kitso ba kuma gyara.

Kallonta Faruk ya yi, ya ce
"wai me ki ke yi haka??? Hauka ko kishi???
Ai duk macen da ta san kanta ba za ta tsaya ta zama BALLAGAZA ba, irin yadda ki ka yi, har hakan ya zama sanadin hango wata da na yi, wadda nake fatan ita ce zata zamemun warkar cutukan da ke, ki ka sa mun, ki godewa Allah da nine mijinki, da wani ne, da tuni kin manta da kin bar gidan, ko ya zama rik'akk'en d'an bariki, ya kuma kwaso cuta ya ya6a miki".

Yana gama fad'ar haka ya janyota, gaba d'aya zanin jikinta ya warware, ya ciro key d'in, sannan ya mika mata, zaninta ya bud'e k'ofar ya fice daga gidan gaba d'aya.

Nadeeya kuwa dask'arewa ta yi a wurin don mamakin kalaman Faruk, kafin daga bisani ta zube a wurin, sannan ta saki wani irin kuka har da dukan bango kamar mahaukaciya sabon kamu....



Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/23, 3:44 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪28-30
©MRS SAIF


Cikin d'an k'ank'anin lokaci soyayya da shak'uwa ta shiga tsakanin Faruk da Fateema, ta yanda in dai suna tare da junansu ba sa kallon kowa sai kan su, soyayya tsaftatatciya mai cike da ganin k'ima da daraja juna.

Ba a d'auki wani dogon lokaci ba, Faruk ya bijirowa Fateema da maganar aure, don baya son dogon zance a yanzu ya fi buk'atar a ce Teeman ta zama mallakinsa, Umma ce ta so ba shi matsala, don cewa ta yi bata amince ya k'ara aure yanzu ba, dududu auren nasa da ko shekara biyu bai kai ba har zai tattago wani auren.

Amma cikin taimakon Allah Faruk ya shawo kanta har ta amince, a dole ita ma Fateema ta amince aka saka ranar aurensu nan da wata uku masu zuwa, don ta gaji da magiyar da Faruk ke mata akan ta taimaka masa ta amince, uwa uba ga shi Faruk ya samu kar6uwa gurin iyayenta, don ta so ta kaucewa buk'atarsa don ta fiso ta d'an yi nisa a karatun ta, in son samu ne ma ta gama, amma k'ememe Abban ta ya amince da buk'atar Faruk.
Don haka itama ta watsar da makamanta, ta amince ta kar6i Maganar auren da hannu biyu, don ummyn ta ta sha gaya mata karatu baya hana aure.


Sai dai damuwarta d'aya da Faruk ya sanarda ita yana da mata, don ko a labari faty bata ta6a gaya mata yana da mata ba, tambayoyi ne birjik a ranta, to me zai saka shi k'arin aure da wuri haka, ga fargaba da ta cika zuciyarta, kar ta je ta tarar da matarsa ta fi k'arfin ajinta, don Faruk bai gaya mata komai ba dangane da abinda ya shafi Nadeeya.
Bare faty da Umma ta mata kashen kada ta sake ta sanar da Fateeman halin Nadeeya, don a cewar Umman ba k'aramin raini zai jawo mata ba.


*******
Fateema ce kwance a kan gadon d'akin ta ta yi rigingine tana kallon fan da ke juyawa, wanda a zahirin gaskiya ba ita take kallo ba, idonta ne kawai akanta amma zuciyarta ta tafi bulayi wata duniyar.
Sallama Ummy (mahaifiyar Fateeman) ta yi tare da k'urawa 'yar tata ido wadda har a lokacin bata san ta shigo ba.

Zama Ummy ta yi akan gadon tare da janwo fateema zuwa jikinta, cikin sigar rarrashi Ummy ta fara magana
"haba mamana me ke damunki haka???
Na shigo ina ta magana hankalinki kwata - kwata baya tare da ke, na fuskanci kwana biyu ki na cikin damuwa gaya mun meye damuwarki kin ji mamana " ta k'arashe maganar tare da shafa dogon gashin Fateeman wanda ya sha gyara, ya kwanta luf zuwa gadon bayanta.

Gyara kwanciyarta ta yi akan cinyar Ummy ta ce" Ummy ni fa kishiya ce bana so??
Ta k'arasa maganar da d'an turo baki.
Murmushi Ummy ta yi tare da d'an zaro idanunta waje ta ce
"haba Azzarah a irin tarbiyyar da na ba ki ai bai kamata ki ji tsoron kishiya ba, sanin kan ki ne, tun kafin ki kai haka nake koyar da ke, duk wasu dabaru na zamantakewa a gidan miji,don haka ki daina Jin shakkar zama da kishiya in dai kin bi kan turbar da na d'oraki, duka lamuranki ki mik'awa Allah shi zai ji6inci lamarinki.

Ummy ta dad'e tana yiwa Fateema nasiha, yanda zata bi mijinta har ma da abokiyar zamanta don Ummy ba ta da duhun kai irin na wasu iyayen, ita ke gayawa Fateema duk abinda ya kamata ta sa ni, matukar shekarunta sun kai ga matsayin sanin abun.
Tabbas Fateema ta ji ta samu kwanciyar hankali da kuma k'warin guiwa, shi yasa take matukar son Ummyn ta don tun tasowarta, ita ce k'awarta kuma mahaifiya don duk matsalar da ta shiga ita take fara gayawa cikin yardar Allah ummy za ta lalubo mata mafita cikin sauk'i.
Dama hausawa sun ce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi......

Let us look back .... Fateema haifaffiyar garin Kano ce, mahaifanta uwa da uba, fulanin garin Garko ne, su shida ne ras a gurin iyayensu, guda biyar duk maza ne, sai a haihuwa ta shida aka haifi Fateema wadda ta ci sunan mahaifiyar Ummy, shi yasa sun fi kiranta da Azzarah musamman Abbansu, Ummy kuma ta fi ce mata Mamana, sauran yayanta kuwa sun fi ce da ita Fateema ko AZZARAH, shi yasa duk wanda aka gaya mata amsawa take yi.

Fateema ta taso cikin kulawa ta iyaye da yayye dukansu k'aunarta suke yi kamar su had'iyeta musamman Abba,ko don ta kasance ita d'aya ce a cikinsu??? domin ba don Ummy a tsaye take ba, da shagwa6awar da Abba zai yiwa Fateema sai ta zarce misali, to da ta ga za a kwacewa daidai za ta yi magana, don ita har ga Allah tana son 'yar ta samu cikakkiyar tarbiyya, wadda take burin ta zama mace tagari a gidan aurenta anan gaba, wacce ko wani miji ke burin samu.

Don haka soyayyarta ba ta hana ta yi mata fad'a idan ta yi ba daidai ba, ta kuma nuna mata tsananin 6acin ranta gudun k'ara afkuwar hakan anan gaba........

[8/23, 4:52 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪
©MRS SAIF


Don haka fateema ta taso da nutsuwa da hankali, sam bata da rawarka irin na wasu 'yan matan wannan lokacin, komai nata mai san yi ne wannan kenan...

****
Faruk kuwa tun bayan, saka ranar auren su da Fateema, ya tashi maganar ginin gidansa da ya fara ya ajiye, don shiri sosai yake wa bikin, tamkar shine na farko duk da  ya ce, wannan bikin ya fi masa na farko sau dubu.

Nadeeya kuwa tun da ta fuskanci da gaske Faruk aure yake shirin yi, ta ce
"ita ba za ta iya zama da kishiya ba, sai dai ya za6a ko ita ko amarya, kun ji fa... Ni dai a nawa hangen sai nake ganin ai sai macen da ta amsa sunan ta na mace a gun miji take ba da wani options a bi ta kanta ba irin su Nadeeya ba... Lolx.

Kallon uku saura kwata Faruk ya bita da shi, sannan ya yi wani malalacin murmushi ya ce
"wato har wani xa6i ki ke ba ni?? Amma da a ce ke mai tunani ce da baza ki ba ni wani za6i ba, don kin san bazan za6eki ba, don haka abinda zan iya cewa dake, idan kin ga za ki iya zama ki zauna idan ba za ki iya ba, ban d'aure ki ba, it's up to you."


Wata k'atuwar k'wafa Nadeeya ta saki sannan ta shige d'akinta tana had'a kayanta tana kuka, don ta sha alwashin daga nan sai dutse, don ko gidan su Faruk ba za ta biya ba, don ita kanta Umman haushinta take ji.

Trolley d'in ta jawo zuwa parlour da niyyar ratsawa ta gefen Faruk ta wuce.
Sai Faruk ya ce da ita
"Ansar kuma fa, na ga kina neman shigewa ki bar shi".
Kallon banza ta watsa masa, sannan ta ce
"Ai ka san da shi na zo, da zan tafi da shi, kai dai da ka ke da jarabar son 'ya' ya sai ka rik'e abunka don ni ko ba shi, zan iya rayuwa".
Daga haka ba ta k'ara ko kqllama d'aya ba ta ja trolley d'in ta tai gaba.

Tsayawa ya yi  rungume da Ansar a jikin sa yana tunanin hali irin na Nadeeya, ya d'auki kusan 5mnts a haka, daga k'arshe ya ga hakan ba zai fitar da shi ba, ya nufi toilet da yaron, wanka ya masa ya shiga d'akin Nadeeya don d'auko masa kayan sawa, sai dai kaf kayan sun yi daud'a, ya rasa mai zai yi, sai can ya tuna da bai dad'e da siyo masa wasu sabbin kaya ba ya manta bai bawa Nadeeya ba, don haka ya koma d'akin sa ya d'auko set d'aya a ciki ya saka masa, sannan shi ma ya shirya, ya rufe gidan ya nufi motorsa rungume da Ansar a k'irjinsa.
Kaitsaye gidan su yana nufa don ba shi da wani za6i da ya wuce ya kai shi can...



Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪31

©MRS SAIF

Umma na kwance a d'aki ta d'an kishingid'a ta jiyo sallamar Faruk da sauri ta yo parlour tare da fad'in "muryar wa na ke ji da safen nan kamar Faruk"??
Sosa k'eya ya yi tare da cewa" ni ne Umma, an tashi lafiya"?
Lafiya qalau Umma ta ce "tare da kai hannu ta kar6i Ansar, sannan ta ce" ina maman ta sa, ba ta fito daga mota ba ne"??
Hannu ya sa ya shafo sumar kansa, sannan ya ce wallahi Umma da ma a.... Sai kuma ya yi shiru, cikin zaro ido waje Umma ta mik'e tana cewa "dama me, mai ya samu Nadeeyan, na ji ka fara magana ka yi shiru".
Kwantar da muryar sa ya yi, ya ce "ba abinda ya same ta Umma, kawai dai ta kasa fahimta ta ne akan zancen auren nan, shi yasa yau tun safe ta shirya ta wuce dutse, don ta ce sai dai na za6a ko ita ko amarya".

Ajiyar numfashi Umma ta sauke tare da cewa "kai kuma sai ka ce da ita ka za6i amarya ko"??
Sosa kai ya yi tare da fad'in" Umma ni fa ta kasa fahimta ta na ne kawai, amma ba nufi na wu......"yi mun shiru ni na nemi mafia, dama idan dai namiji ya so k'arin aure ai dole ta gida ta yi hak'uri, bare Nadeeya da take a lanjare". Umma ke fad'in haka ta hanyar katse maganar Faruk.

Waya ta d'auka ta kira layin Nadeeya sai dai number'n x not reachable, don haka ta lalubo number'n maman Nadeeyar itama x switched off. Wulli ta yi da wayar kan kujera tana kallon Faruk ta ce ga shi wayoyin na su duk ba sa shiga".

Murmushi Faruk ya yi tare da fad'in "Umma ki daina wahalar da kan ki, ita ce mai dawowa da kanta, duk wannan na san barazana ce".
Harararsa Umma ta yi sannan ta ce "wato na k'yaleta tunda kai ba ka da hasara wani auren za ka yi, ni kuma ka lalata mun dangantaka ta da aminiyata, ko da yanzu za ta dawo, dole na cigaba da bibiyarta ita da mahaifiyarta, don gudun samun matsala, idan ka kawo tsiya yanzun za ka ajiye duk abinda ka ke yi mu yi shirin zuwa dutsen".

Ai ba shiri Faruk ya tsuke bakinsa, don idan umma ta ce a je dutse yau, ai duk ta rusa masa schedule d'in sa na yau. Saboda haka ya ce "Umma ki yi hak'uri don Allah, bari na ajiye Ansar na wuce wurin aiki nan ma ba dadewa zan yi ba zan nemi excuse na je duba aikin ginin da ake yi".
Sai da ta kara waya a kunnenta don k'ara neman layin maman Nadeeya, ta ce masa Allah ya taimaka, amma Ansar yana cin abinci kuwa??

Faruk ya ce "sosai ba abinda baya ci".
Umma ta ce "oho! To ai da sauk'i, kasan yaran yanzu sai su k'i bawa yara abincin mu na asali sai na gwangwanaye, sai ka ga yaro ya fi shekara amma baya iya cin abincin gargajiya".
Dariya Faruk ya yi ya ce
"Umma sai na dawo ina makara ".
Umma ta ce to, Allah ya kiyaye hanya".
Ya ce "ameen tare da ficewa daga parlourn.


*****
DUTSE

Nadeeya ce zaune ta yi jugum, tana tunanin wannan wacce irin masifa ce, gidan aure ba dad'i ta zo gidan su don ta ji sanyi nan ma ta tarar da wata masifar, ba ta k'arasa tunanin da take yi ba ta tsinkayo muryar mamansu tana cigaba da fad'in
"to don ma ki ji na gaya miki, ba ki da wurin zama a gidan nan, idan dai ba so kuke ku kashe ni da raina ba,ga yayyanki can guda biyu watan da ya wuce duk aka sako su, har an fara zund'en mu a unguwa, a haka ke ma ki ke so ki kashe na ki auren ku zo duk mu zauna taron zawarawa, to ahir ki fita a idona, tun muna mu biyu ki kwashi kayanki k koma".

Kuka sosai Nadeeya ke yi tana yiwa mama magiya akan ta k'yaleta ta zauna, amma k'ememe maman ta k'i.
Cikin kuka Nadeeya ke cewa "haba mama yanzu ina komawa kano a yau ai zai zamemun abin gori har zuwa k'arshen rayuta, a ce gidan na mu ma sun kasa rik'eni sun koroni".
Cikin tsawa mama ta ce
"su fad'i ko ma meye amma ba zan goyi bayan ki kashe aurenki, ki zo gida ki zauna ba".
Amma mama ai kya bar ni ko zuwa sati ne na yi kafin na...... Ringing phone d'in ta shi ya katse maganar da take yi, ganin sunan Umma ne ya saka ta daidaita nutsuwarta kafin ta d'aga.
Bayan sun gama gaisawa ne, ta ce ta bawa mama wayar, ba musu ta mik'a mata, sun dad'e suna tattaunawa kafin daga bisani su yi sallama.

Juyo da dubanta ta yi ga Nadeeya ta ce "kin ci arzikin sirikarki, da ta biyo sawu don ko ba komai nasan maganar aurenki tana nan, tunda tana ta ba da hak'uri ga shi ta ce a jira Faruk zai zo da kan sa ya tafi da ke".

Wata k'atuwar ajiyar zuciya Nadeeya ta sauke don ko ba komai ta ji kashi hamsin a cikin d'ari na daga damuwarta ya yaye....



Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/26/16, 9:53 AM] phatyma▪BALLAGAZAR MACE ▪32&33
©MRS SAIF



Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, yau bikin Fateema da Faruk ya rage saura 3wks, shiri sosai suke yi ta 6angarorin guda biyu.
Yayin da Faruk ya gama gininsa tsaf, gida ya tsaru ba'a magana.
Fateema kuwa har an fara mata gyaran jiki don musamman Ummy ta d'auko mai gyaran jiki 'yar Maiduguri, cikin' yan kwanakin da aka fara mata gyaran ta koma tamkar wata tauraruwa, lungu da sak'o duk gyara ake mata don matar ta san aikinta sosai.

Nadeeya na gefe, duk takaici ya cikata, don tun dawowarta ta rasa yanda zata 6ullowa lamarin, musamman yadda ta ga Faruk na masifar rawar kai akan auren, har mamaki ta ke yi kamar ba Faruk d'in da ta sa ni ba,dama akwai macen da zai rik'a rawar kai akan aurenta, idan har ta kwatanta da lokacin bikin su yanda ya nuna ko'in kula akan auren a wancan lokacin lallai tana son ta ga wannan yarinyar ta ga da me ta fita,yake wannan uban rawan jiki akanta.

A zaune take parlour ta rafka uban tagumi, yayin da ta saka TV a gaba kamar mai kallo, amma sam zuciyarta ba ta kai, tunanin mafita kawai take duk da ta san ba makawa sai an yi auren, sallamar da maman Deedat(mak'ociyarta) ta yi ne ya katse mata tunani.
Tace "lafiya maman Ansar ina ta sallama amma sai yanzu ki ka jiyo ni"???
Hmm! Bari ke dai, ina cikin wani yanayi ne shi yasa  kwata_kwata ban ji motsin shigowarki ba, cewar Nadeeya.
Maman Deedat ta ce" Subhannallah! Me ya faru ne"??
Murmushin yak'e Nadeeya ta yi, tare da cewa
"akan zancen auren nan mana, yanzu haka dududu bikin bai kai wata d'aya ba".
Neman wuri ta yi ta zauna sannan ta fara magana da cewa "maman Ansar na sha gaya miki abinda ki ke yi ba kya kyautawa, yanzu don Allah kalleki kalli gidanki, ta yaya namiji zai shigo ya tarar da matarsa a haka ki ce zai samu farin ciki, ki na ganin dai wasu mazan ki'ris su ke nema, su k'aro aure, amma ke tsakani da Allah Faruk ya baki lokaci amma kin k'i ki gyara, to ya kike so yayi
Idan bai k'ara aure ba, sanin kan ki ne ya.... A zafafe Nadeeya ta d'aga mata hannu tana fad'in "ya ishe ni haka, ke wace da har za ki shigo har cikin gidana ki ce za ki ci mun mutunci, to wallahi kin yi kad'an, kaitsaye ke ma ki fito ki ce mun k'azama, kamar yadda wasu suka saba fad'a, ya fi wannan lunku - lunkun da kike yi".
Maman Deedat ta ce "ni fa shawara ce na ke ba..." ki rik'e abar ki bana so, taso ki fice mun daga gida", cewar Nadeeya.
Ba musu maman Deedat ta shure takalminta ta fita.

Nadeeya sai wani cika take tana batsewa ita alallai an 6ata mata rai, Ansar ta sa6a a baya ta saka hijabinta, ta kulle gidan ta nufi hanyar gidan maman Nabeela.

*******

Kallo d'aya maman Nabeela ta mata ta fuskanci damuwa tattare da ita, da sauri ta nufo inda ta ja birki ta tsaya zo ta tana fad'in "aminiya me ya sameki na ga ranki a 6ace"??
Tsaki Nadeeya ta ja, sannan ta ce" kin san dai damuwata ba sai na kuma maimaita miki ba, to wata aka kuma dora mun akan wata , yanzun maman Deedat ta bar gidana, wai har ni za ta kalli tsabar idona ta ce wa k'azama".

Shiru maman Nabeela ta yi, don ko ita har ga Allah tana son ta yiwa Nadeeya magana akan wasu halayenta ta daina musamman k'azantar ta tayi yawa, amma tana tsoron ta fara gaba da ita, tunda ta ga duk wanda suka yi gigin nuna mata hakan sun dawo abokan gabarta.

Yana ga Kin yi shiru, cewar Nadeeya, murmushin da bai kai ciki ba, maman Nabeela ta saki tare da cewa "uhmm! Ai mutane ba a iya musu, kana barci ne ana Maka minshari".
Wata doguwar k'wafa Nadeeya ta ja, wanda ya yi daidai ta shigowar mai kayan Mata.
Ta ce "lafiya kuwa na ganku kowa fuska a murtuk'e"??
Anan suka kwashe duk abinda ake ciki suka gaya mata wata dariya ta saki, sannan ta je gurin da Nadeeya ke zaune ta dafa kafad'arta ta ce 'yar uwa kwantar da hankalinki, in dai za ki saki kud'i zan had'a miki magungunan da sai kin sha mamaki a gun mijinki, don kuwa idan har kika yi amfani da su, zai manta da duk wata' ya mace sai ke, za ki zama super star a wurin sa,kishiya sai ta tattara kayanta da kan ta, ta bar miki gidanki don baza ta jure wulak'ancin da zai rik'a mata ba, don yanda kika san kaza wadda ta sha maggi da sauran sinadaran d'and'ano haka za ki koma, ita kuma yanda ki ka san kazar da aka dafa da zallar ruwa ba tare da an gwaraya shi da ko d'an gishiri ba, haka zata zama a gunshi, amma fa akwai tsada sai dai za ki ga aiki da cikawa".

Wani murmushi Nadeeya ta saki na jindad'i ta ce
"kud'i ba matsala ba ne ko nawa ne zan ba da, don na mallaki mijina ni kad'ai, domin bai dad'e da ba ni kud'in kayan fad'ar kishiya ba, don da ya ce zai had'o mun kaya na ce bana so ya ba ni kud'in domin ina da kaya, yanzu haka zancen da na ke yi akwai kaya tun na lefena wanda ban ta6a sakawa ba, to me zan yi da wasu, tunda ni ba wani bari na fita yake yi ba, bare idan zan fita na saka, don haka na ce gwanda ya bani kud'in, yanzu ba ga shi kud'in zai mun amfani ba".

Sosai kuwa mai magani ta fad'a tare da cigaba da cewa "gwara ki gyara jikinki, yanda za ki kaucewa duk wani SABON SALO IRIN NA D'A NAMIJI (Lubiee's buk),da zai bijiro miki da shi lokacin da amaryarsa ta tare".

Ni kam (Mum Twins) na ce anya kuwa maganar, mai maganin mata haka ne???
Don dai na san kaucewa duk wani Salo irin na d'a na miji hanyoyi ne da dama, ba wai sai ta hanyar d'irkar maganin mata kawai ba.

Shewa suka saki don Jin furucin mai maganin mata tare da cewa "gaskiya maganarki haka yake, don wasu mazan zuma ne a sha zak'i a kuma sha harbi lolz......


Sai Monday kuma, ku yi mun uzuri please ❤👌🏻


Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/29, 11:57 AM] Phatyma: [8/29,16,11:32 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪34

©MRS SAIF



Yau ta kasance ranar alhamis, kuma yau ne aka fara gudanar da shagalin biki, a yau d'in ne a ke saran yin kamu da k'arfe 4:00pm.

Faty ana can ana faman shiri, kamar ta cire kanta don murna da zumud'i, ku kuwa ba dole ba, ita ce babbar k'awar amarya kuma k'anwar ango tilo, don haka ita abubuwan ma har sun mata yawa, bata nan bata can.

****AMNEEF PALACE a k'arfe hud'u da mintuna arba'in, Wurin ya cika ya kuma tsaru ba k'arya, duk mutanen dake gurin suna dakon zuwan amarya ne,yayin da Ali jita da muk'arabansa ke cashewa a tsakiyar filin gurin da wak'ar AURE.

5:5pm convoy na motocin amarya suka danno kai harabar wurin, nan da nan MC ya fara sanarwa ga amarya nan, cikin k'warewa a harkar suka chanza salon wak'ar zuwa ta bikin... Mai taken :Alk'wari ya cika auren so k'auna tsakanin Faruk da Fateema.

Hankalin kowa ya raja'a ga hanyar shigowa wurin, don bawa idonsa abinci, 'yan mata amarya ne a gaba don haka su suka fara shigowa ciki kuwa har da fatyma, ta sha kyau har ba a magana, cikin wani lace dark green, mai adon orange riga da skirt ne, d'inkin ya zauna das a jikinta, komai orange colour ta yi amfani da shi ta yi kyau sosai.
K'arasowar amarya ne ya sa na manta kyan da faty ta yi, wohoho! Ku zo ku ga amarya yanda madarar kyau ke zuba, Abun ba a cewa komai sai dai na ce Masha'Allah TubarakallAllah! Don amarya Teema ta yi kyau tamkar ka sureta ka gudu.

Su Nadeeya ma ba a bar su a baya ba don sun zo ita da gayyar mutanen dutse, da mak'otanta irin su maman Nabeela, itama ta yi kyau sosai, sai dai ganin Teema yasa ta raina kanta, don nan da nan zuciyarta ta cunkushe da wani azababben kishi, wanda take ji kamar ta je ta shak'e teeman sai dai ba hali, daga k'arshe ma ji take kamar ta yi tafiyarta ta bar wurin don duk mutanen dake gurin haushin su take ji, amma a dole ta cize ta daure ta zauna har zuwa lokacin da za a tashi gudun tsegumin mutane.


An ci an sha an kuma yi lafiya an gama lafiya, k'arfe takwas na dare aka watse ko wa ya nemi hanyar da zata sada shi da mazauninsa.

[8/29,16,11:32 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪35

©Mrs Saif

K'arfe goman dare Faruk ya nufi tamfatsetsen gidansa, wanda suka koma shi da uwargida Nadeeya, kafin isowar amaryarsa Teema, duk da bai so hakan ba shi yaso ne sai an kawo Fateema sannan Nadeeya ta tare Umma ta ce "sam ba ta san da haka ba, idan ya yi haka tamkar ya ciwa Nadeeya mutunci ne.

Amma duk da haka sai da yasa Umma ta nemo masa 'yan aiki dattijuwa d'aya da yarinya, duk da kowa da part d'in sa amma gaskiya shi ya tsorata da k'azantar Nadeeya, duk da kwana hud'u kachal za su yi a gidan Teemansa ta tare, amma ji yake kamar zata chanza kalar gidan kafin lokacin, don da yana da dama har ita kanta da ya chanza tunaninta kafin dawowarsu, don tsohon gidansu gaba d'aya ta gama condemning nasa.

Gama tunaninsa ya yi daidai da k'arasowarsa gate d'in gidan, horn ya dannawa mai gadin, cikin azama ya ja gate d'in, Farouq ya danna hancin motarsa zuwa wurin da aka tanada don motoci.

Bayan ya yi parking kaitsaye main parlourn gidan ya nufa, sai dai wayam ba kowa a ciki sai TV da ke 6a6atu ita kad'ai, juyawa yayi da dubun sa 6angaren dama inda part d'in Nadeeya ya ke, anan ya jiyo tashin hayaniyarsu ita da 'yan uwanta, da alama ba a parlourn ta suke ba, suna can cikin d'aki ne, don maganar ta su can nesa yake jiyo su.
Don haka ya sauke k'wayar idonsa a part d'in Fateema wanda ke kulle, murmushi ya yi, kafin daga bisani ya haura sama don zuwa nashi part d'in.

Kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shiga toilet ya yi wanka, sannan ya samawa kansa kaya marasa nauyi, dama ya ciko cikinsa daga gidan abokinsa Abbas, don haka bai ma yi yunk'urin kiran Nadeeya ba, don ko ya kirata ba lallai ta zo ba, domin fushi take yi da shi ba na wasa ba,idan kuwa ta zo yasan ba za su rabu cikin arzik'i ba, don haka ya shareta.

Wayarsa ya janyo ya danna kira a lambar Fateema, a lokacin Fateema na zaune ta saka wata k'atuwar gora mai d'auke da ingantaccen tsimi a gaba, tana faman ya tsine fuska, tana cewa "Ummy ni dai na gaji da shan wad'an nan kayan kusan sati nawa ina fama da su", ta k'arashe maganar tare da kwa6e fuska kamar zata yi kuka.
Ummy har za ta yi magna sai wata yarinya ta shigo da gudu tana cewa "Aunty Fateema ana ta kiranki a waya, ga shi har ta kuma tsinkewa".

Kar6ar wayar Fateema ta yi ganin sunan Farouq da ta yi saving da QALBY ya bayyana a fuskar wayar d'auke da 3 missed calls, ya saka ta wani tattausan murmushi tare da mik'ewa.
Ummy ta ce
"ina zuwa kuma ??? kin bar abun na ki anan".

Dawowa Fateema ta yi tare ta d'aukan goran da cup, ta fita don itama ana so ne ana kaiwa kasuwa don sarai ta san mazan yanzu sai ana had'awa da 'yan sinadarai musamman ita mai kishiya.

Side d'in Abbanta ta nufa don gidan na su cike yake da'yan uwansu wanda suka zo don biki musamman mutanen Garko,don har d'akinta cike yake taf da' yan mata.
Guest room dake part d'in Abba ta bud'e ta shiga, daidai lokacin kiran Farouq ya kuma shigowa wayarta, don ji yake idan bai ji muryarta yau d'in nan ba, ba zai iya barci ba.
Can k'asan murya ta ce
"hello"
Wani sanyi Farouq ya ji tare da fad'in "Fatyna wai ina ki ka shiga tun d'azu na ke kira ba ki yi picking ba"??
Cikin siririyar muryarta ta fara fad'in" na ajiyeta a parlor ne, ni kuma ina d'akin Ummy".

Ajiyan zuciya Farouq ya yi, sannan ya ce "please Teemana ki rik'a yawo da phone d'in ki,, kin san fa yau kusan sati kenan ban ganki ba, kin hana ni ganin kyakkyawar fuskarki wai sai ranar da za a kawoki sannan zan kuma ganinki, amma ai ya kamata ko muryar ki na rik'a ji akai-akai ko na samu sauk'i".
[8/29, 12:09 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪36

©Mrs Saif

Murmusawa ta yi tamkar yana gabanta, ta dad'a kashe murya ta ce "haba Qalby dududu kwana nawa ya rage na zama mallakin gaba d'aya, ka kwantar da hankalinka nan da kwana uku Teema ta zama ta ka kai kad'ai".

Wata ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonsa, ya ce "fatyna kin san hausawa sun ce aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi, Allah kwana ukun nan da ya rage ji nake kamar shekara uku".
Dariya Fateema ta yi sosai tare da cewa "ni fa kana ba ni mamaki idan ka fad'i haka, kai ba saurayi ba, ba kuma tuzuri ba, ga yayata a kusa da kai, to saurin me ka ke yi kuma".???

Hmmm! Ba za ki gane ba ne Fateema ni fa son ki a jinina yake, Allah dai ya kai mu lokacin".
"ameen" Fateema ta ce, suka cigaba da hirarsu cikin nishad'i kamar ba gobe.

Washe gari Ummy ta had'a k'ayattacciyar walima ta mata zalla, wadda aka gabatar anan harabar gidan, malamai da dama sun wa'azantar tare da nasihohi duk akan zaman aure.

****
Ranar lahadi Misalin 11:00am dubban jama'a suka shaida d'aurin auren FATEEMA & FAROUQ akan sadaki dubu hamsin.
Duk wanda ya kalli farouq ya san yana cikin tsantsar farin ciki a wannan lokacin,abokan arzik'i sai zuwa ake yi ana masa Allah sanya alkhairi.

6:00pm ***

Motocin ango suka dira k'ofar gidan su Fateema don tafiya da ita gidan aurenta, a lokacin har an gama shiryata cikin wata dakakkiyar lafaya red da ratsin black ta yi matuk'ar kyau, sai wani mahaukacin k'amshi dake tashi daga jikinta, don ko zama ta yi a guri sai ya dad'e bai daina k'amshi ba, haka idan mutum ya ra6eta tabbas shi ma zai kwashi irin k'amshi, don wasu turaruka ne, na musamman wadda ta mata gyaran jiki ta mata amfani da su.

In ban da kuka ba abinda fateema ke yi, ta k'wak'ume Ummy tana fad'in "ita ba za ta je ba, ta fasa auren ba za tafi ta bar Ummynta ba, duk dauriya irin na ummy sai da Teema ta sakata kuka, rungumeta ummy ta yi sosai tana hawaye tana fad'in
" yi hak'uri mamana, duk 'ya mace ta haka ce, muma duk haka aka mana, wata rana sai labari, ina dai kuma nanata miki ki yi hak'uri, zaman duniya duk d'an hak'uri ne, ki bi mijinki sau da k'afa, matuk'ar bin bai shafi sa6awa shari'a ba, ki kuma yiwa abokiyar zamanki biyayya daidai gwargwado, duka nasihohin dana dad'e ina miki Azzarah ban yarda ki jefar da ko d'aya ba, Allah ya miki albarka ya baki zaman lafiya a gidan aurenki, tare da zuri'a d'ayyaba".

Duk wanda ke gurin sai da ya amsa da ameen, sannan aka 6an6are fateema da k'yar daga jikin ummy, aka wuce da ita wurin Abbanta, shi ma naseeha ya yi mata sosai sannan aka fito da ita aka sa ta a mota sai gidan Farouq.

Kamar yadda aka saba bisa al'ada akan fara kai amarya ne wurin uwar gida kafin akaita na ta d'akin, to haka ce ta kasance da Fateema don sai da aka fara kaita wurin Nadeeya aka damk'a mata amana sannan aka wuce da ita 6angarenta.

K'arfe takwas kusan duk 'yan kawo amarya sun watse, daga amarya sai faty da wasu k'awayensu guda uku, a dole Fateema ta ware lafayar ta tashi don d'auro alwala ta yi sallah Faty sai tsokanarta take yi ganin kayan da ke ciki, riga da skirt ne na wani rantsatstsen swiss, d'inkin ya yi kyau sosai tamkar tare aka halicce shi da jikinta ya yi  bala'in fitar da kyakkyawar surarta, ta yanda ita kan ta sai da ta ji kunya ganin irin kallon da sauran friends d'in su ke mata.

Tana idar da alwala ta d'auki lafayar ta mai da, Faty na mata mitar tana idar da sallah za ta warware mata lafayar don ba za ta ma yayanta k'wange ba".

Sauran 'yan matan suka bushe da dariya, d'aya daga cikin su mai suna safeena tace" ke ma Fatyma da son zance, yau yayanki ai har... Wacce ke kusa da ita ta bige mata baki tare da cewa "ke fa safeena akwai iskanci, ki na so ku yi fad'a da Faty ke nan don ta sha gaya mana yayanta ba d'an iska ba ne don haka ki yi shiru da bakinki."

" uhmm" kawai Fateema ta ce ta koma bakin gado ta zauna don ita duk Jin su take yi, ita kad'ai ta san abinda take tunani.

K'arfe 9:40pm Farouq ya shigo gidan shi da abokinsa Abbas, sai da suka fara zuwa wurin Nadeeya ya jiye mata irin ledar da ya shigowa Fateema da ita, Abbas yana ta bata baki ita kuma sai wani cika take tana batsewa, a haka dai suka barota suka yo part d'in Fateema.

A bakin k'ofa suka ci Karo da Faty ta za ta fito, da sauri ta yi wurin yayanta tana cewa "ga ango, ga ango".
Murmushi ya yi ya ce "Fatyma yau na zama dai abokin wasanki ko"??
Ita ma murmushin ta yi ta ce" yayana ni fa nan jira nake mu siye baki, sannan mu tafi".

D'an zaro ido Abbas ya yi, ya ce "zamani k'anwa da siyen bakin wa."
Dariya suka saka gaba d'ayan su, sannan Farouq ya janyo hannun Fatyma yana cewa
" yanzu mu k'arasa ciki k'anwata akwai kyauta ta musamman da na kaiwa Umma ta ajiye miki, don kin taka muhimmiyar rawa ganin na aure k'awarki, thank yhu so much".

Fatyma ta ce "never mind bros, farin cikinka shine nawa so dole na ba ka gudummawa don ganin hak'an ka ya cimma ruwa".

Sakin hannun faty da yayi, yai daidai da k'arasawarsa, inda fateema ke zaune, yana daf da K'arasawa saitin fuskarta da ta ja mayafin lafaya ta rufe... Abbas ya katseshi ta hanyar cewa "Farouq wooo! Ka na ji ana maka magana amma gaba d'aya hankalinka ya tafi gun amaryarka, shafa sajen dake kwance a fuskarsa ya yi tare da cewa
" am sorry! Me ka ce ne"??
Abbas ya ce
"ba ni nai magana ba k'awayenta ke ta Maka magana ka share su, "oh! Sannunku k'awayenmu ban ji ba ne". Cewar Farouq gaba d'aya suka kwashe da dariya.

Lokacin Faty ta dawo daga part d'in Nadeeya tana cewa
"to na yiwa Aunty Nadeeya sai da safe, don haka kuma ku kwaso bags d'in ku mu yi gaba".
Abbas ne ya ce
"ke da kika ce sai kun saye baki, kuma kike maganar su zo ku tafi".
Dariya Faty ta yi ta ce
"ya Abbas dama da wasa nake yi, kai muke jira ka kai mu gida, ka ga dare ya rigaya ya yi, don na san bros ko bai zo da kowa ba, zai zo tare da kai, shi yasa muka tsaya jiranka, idan ka zo ka mai da mu."


Haka ne Abbas ya ce tare da ja musu, doguwar addu'a ta fatan zaman lafiya, su faty suka amsa da ameen, sannan suka mik'e da zummar tafiya.

Farouq ko irin rakiyar nan da ake yi wa abokan ango bai yi wa Abbas ba, suna fito ya rufo k'ofar ya datse da key, ya nufi wurin amaryarsa zuciyarsa taf farin ciki kamar wanda aka yiwa bushara da aljanna.

Nima ganin haka na tarkato takarduna na yo waje, tun kafin su Fateema su wuce, don na samu su d'an la6ani ko a hanya sa saukeni, don haka sai dai na ce "asuba tagari Farouq da Fateema, Nadeeya kuma Allah ya ba da ikon danne kishi" ...



Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/30,2016) phatyma 🌻: ▪BALLAGAZAR MACE ▪37-40

©MRS SAIF


Duk sammakon da na yi, don ganin yanayin da amaryar ta tashi a banza, don ko da na isa na tarar Fateema har ta yi wanka ta shek'a kwalliya cikin dark purple shadda wadda aka yiwa aiki da zare pink, ta sha English gold mai kyau yari da sarqa d'aya daga cikin na lefenta.

Ta kashe d'auri ya zauna d'as akanta tamkar gwaggwaro, fuskarta ta sha maka-up mai kyan tsari, sai walwali take yi tamkar tauraruwa, jikinta sai wani asirtaccen k'amshi ke tashi, tana cikin zira wani flatshoe pink colour mai kyan gaske, Farouq ya bud'e k'ofar ya shigo, shi ma ga dukkan alamu bai dad'e da gama shiri ba, ya yi kyau sosai ka na ganin shi ka ga ango mai cike da farin ciki da annushuwar halin da ya tsince kansa a ciki.

A bakin k'ofar ya tsaya tare da kafe Fateema da ido, fuskarsa d'auke da murmushi ya ce "yhu look very beautiful, komai na ki burgeni ya ke fatyna".
"thanks" ta fad'i tare da k'okarin gyara igiyar takalmin da ya d'an karkace, K'arasawa inda take sunkuye ya yi,ya d'agata ya zaunar da ita akan gefen gado sannan ya ce" lemme help yhu"... Yana k'okarin kai hannunsa kan takalmin, ya gama gyara takalmin sarai, amma sai ya kasa sakin k'afar, yana k'arewa had'ad'd'en Jan lalle da zanen bak'n fulawan da ke k'afar kallo.

Shirun da ta ji yayi ne ya tabbatar mata ya gama gyara mata takalmin, don haka ta ce "bari na je na gaishe da mutanen gidan, kar su jini shiru".
"hmm"Farouq ya ce tare da lumshe ido sannan ya jingina bayan sa a kujerar da yake zaune.
Don ko kad'an ba ya son missing k'amshn jikinta, in dai yana tare da ita sai ya manta duniyar da yake, rufe idonsa ya yi sosai don tuna irin farin cikin da ya samu a daren jiya, sosai yake Jin k'aunar Fateema a ransa, fatan da yake Allah ya sa ta d'ore a haka, don daga gani za ta yi sanyin hali.

Bata wani sha wahala ta gano part d'in Nadeeya don ba wani nisa ne na ku zo mu gani ba a tsakanin su, kuma tsarin wurin d'aya ya ke da na ta.
Da sallamarta ta kutsa kai cikin parlourn, sai dai da alama Nadeeyan ba ta parlourn sai Ansar da ke zaune ya bud'e gwangwanin madara duk ya barbazar a gurin, ya kuma d'iba ya saka a jikin sa, da alama tea suka gama sha ba a kwashe kayan ba.
Da d'an hanzarinta ta k'arasa gurin yaron ta d'aga shi tana kakka6esa masa, a ranta ta ce "wow! Yaron kyakkyawa da shi".
Dama Fateema akwai masifar son yara, duk wanda ya san ta ya San halinta na son yara.
Da ta ga madarar duk ya manne a jikinsa ya k'i fita, don da danshin ruwa a jikinsa, sai kawai ta tu6e masa kayan,ta bar shi daga shi sai diaper tana cewa "bari mummynka ta fito sai a chanza ma wani kayan ko"??

[8/30,16,5:16 PM] phatyma :

Ta k'arasa maganar tare da sakarwa yaron murmushi kamar yasan, me take cewa shima ya 6angale baki yana dariya, sai dai tun da ta cire masa kayan take Jin d'an wani wari - wari yana tashi, don haka ta bi jikin yaron da kallo daga k'arshe idonta ya sauka kan diaper'n yaron wadda ta cika mak'il har ya fara zuba, da alama tun jiya yake a jikinsa ba'a cire masa ba.

D'an fito da ido waje Teema ta yi tana kallon yaron, ta rasa mai za ta yi masa, ga shi har yanzu mamansa ba ta fito ba, don da alama tana cikin toilet don ta ji motsin mutum a ciki.

×××××××××

Daga k'arshe ta yanke shawarar ta tafi da yaron side d'in ta kawai ta masa wanka a can idan mamansa ta fito ta dawo da shi a saka masa wani, don haka ta sunkuya da nufin d'aukan shi su tafi, ta ji an banko k'ofar toilet da k'arfi an fito.
Nadeeya ce d'aure da zani da alama daga wanka ta fito, kana ganinta kasan ba ta fita, jikinta sai wata walk'iya yake yi na alamar daud'a ta taso amma ba a samu damar darjeta ba, tamkar watsa ruwan ta yi ta fito.

Kallo d'aya Fateema ta yi mata ta sadda kanta k'asa tare da fad'in ina kwana"?
"lafiya " ta bata amsa a tak'aice, Sannan ta cigaba da fad'in " ya aka yi na ga kin cire masa kaya, ko kinibibi ne irin na amare masu neman shiga za ki fara akansa.??
Ja gale Fateema ta yi tana kallonta, a ranta ta ce "to fa ita na ta salon kishin kenan...??
" kin shigo d'akin mutum kin ga baya nan ba sai ki fita".
Maganar Nadeeya ta katse mata tunanin.
Nuna Ansar ta yi da hannu, ta ce "yaro na tarar yana 6arna na tsaya gyara shi, sai kuma daga baya na ankare da ya cika diaper'n sa, so shine da zan tafi da shi na yi masa wanka sai ga shi kin fito".

"To uwar iya zance, na ji na kuma gode kya iya tafiya, Nadeeya ta fad'a tare da gyara mazaunin zanin dake jikinta.
Murmushin takaici Teema ta saki tare da kad'a kai ta yi hanyar fita, dogon tsakin da Nadeeya ta saki shi ya tilasta mata jiyowa, daidai lokacin ta kakka6e kayan Ansar dake k'asa tana niyyar mai da masa.

Mamaki sosai Fateema ke yi tana tunanin, wannan wace irin mace ce, tana nufin haka zata maidawa yaron kayan ba tare da ko diaper'n jikinsa ta cire masa ba.

"Tab" ta ce a ranta lallai akwai magana a gidan nan, da wannan tunanin ta k'arasa part d'in ta, in da ta bar Farouq har lokacin yana zaune a gurin, sai dai yanzu ya mai da hankalinsa ga TV, yana kallon news na safe.

Sallamar da ta yi shi ya dawo da hankalinsa gareta, cikin k'ank'anin lokaci ya fuskanci sauyawar da fuskarta ta yi, a hankali ya taka zuwa inda take, gaba d'aya ya janyota jikinsa, cikin muryar rad'a yake cewa
"something troubling yhu babe, what happened???
A hankali ta girgiza kanta alamar ba komai, don har ga Allah ba ta so ya gane damuwarta ba, domin abun da Nadeeya ta mata ba ta d'auke shi wani abu, don ta shirya d'aukan k'alubalen da ya fi wannan.

Sai dai Farouq ya santa sosai, fiye da yadda yasan yunwar cikin sa, ta yanda a kowa ne hali take ciki zai iya tantancewa.
Cikin son bagarar da zancen ta ce "Qalby ni fa yunwa na ke ji".
Murmushi Farouq ya yi ya ce
"Ai ke ce na ce zan fita na siyo mana abinda za mu yi breakfast kin k'i, kin ce sai dai ki girka da kanki ni kuwa yaushe zan bar amarya ta shiga kitchen washe garin ranar da ta tare, ki yi hak'uri baby idan kin k'ara hutawa sai ki mana, ni kai na zan yi matuk'ar farin ciki da hakan, na yiwa Umma waya yanzu haka fatyma na hanya za ta kawo mana breakfast.

Bai dad'e da rufe baki ba suka jiyo sallamar Fatyman, cikin d'auken ganin juna, suka rungume juna suna murna kamar wad'anda suka shekara ba su ga juna ba.

Sannan Faty ta juya tana gaishe da yayanta, kafin daga bisani su shige kitchen Faty rik'e da foodflask da ta shigo da shi, Fateema kuma ta kar6a mata d'ayan teaflask da ke hannunta.

Kunun gyad'a ne mai kyau a cikin teaflask, sai kuma yam fritters with chicken souce a d'aya foodflask d'in, bayan sun gama zubawa a plates, sai suka d'oro akan tray tare da cups, suka dawo parlourn.
A dining table suka dire kayan sannan suka yi kiran Farouq, anan suka ba je suna cin abincinsu cikin nishad'i suna firansu jefi-jefi har da Farouq, Faty tana son tambayar Fateema first night amma Farouq ya kasa ya tsare ya k'i ba su damar su d'an ke6e, kun san 'yan mata da maitar son Jin ya first night ya kasance...lolz......




Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/31, 4:24 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪41&42

©Mrs Saif


Sati d'aya cif suka yi suna kwasar amarci, tamkar za su had'iye junansu don so da kulawa, yayin da Fateema ta shige lungu da sak'o na zuciyar Farouq, ta yadda ba shi da wani muradi, da ya wuce kasancewa tare da ita.

A kwanakin da suka yi kullum Fateema ke jigilar kawo musu abincin safe kasancewar suna cikin hutu, na rana da dare kuwa Farouq ke turawa a kar6o, don in dai ta Nadeeya ne sai dai su mutu ba su ci ba, don yanzu haka, 'yan aikin da Farouq ya kawo kafin tariyar Fateema suke girkin gidan, idan sun gama Nadeeya ta yi zaune ta nad'i abinta tashi, ita kam Fateema tun da ta ga haka ta ce "ba za ta iya ci ba, don ba ta saba da cin girkin masu aiki ba, don a gidansu ita da ummynta ke girki, ko da wasa Ummy ba ta saka masu aiki a harkar da ya shafi kitchen".

"musamman wad'an nan ta ga ko tsaftar kirki ba su da shi, daga su har uwar d'akin ta su, don cikin sati d'ayan da ta yi ta gane wacece Nadeeya, don haka ta k'udurci niyyar kawo gyara a cikin gidan ko don samun kwanciyar hankalin mai gidan, domin da Farouq ya amince da zancen ta da tuni ta tsufa a kitchen, amma ya dage ta bari ko sati d'aya ne ta yi, sannan ta fara shiga kitchen kafin lokacin ta k'ara hutawa, ba ta son yi masa musu shi yasa ta amince, don haka yanzu jira kawai take yi, girki ya kuma zagayowa kanta, ta fara shiga office mai daraja ga duk macen da tasan kanta."

*************

Tun safe yau da ya tashi yake Jin shi wani iri, kamar ba shi ba duk jikinsa ya yi sanyi, ba wani fara'a a tare da shi ba kamar yadda ya saba a 'yan kwanakin nan ba.
Fateema har ta kula da yanayin da ya ke ciki, don haka a gurguje ta k'arasa shirinta cikin atampa super lucca's grey colour, fitted gown ce wadda ta zauna jikinta cas ta yi kyau sosai, fuskar nan ta yi fayau ta k'ara hasken amarci, kana ganinta ka ga amaryar da ke samun cikkakiyar kulawa gun angonta.

K'arasawa ta yi kan gadon da yake zaune ya jingina bayansa da pillow, ta zame pillown sai ta yi replacing kanta da pillown, sosai ya ji dad'in kwanciya fiye yanda ya ke a da.
Cikin salon maganarta mai Jan hankali ta ce "Qalby wai me ke damunka ne, na ganka yau a cikin wani yanayi please gaya mun abinda ke damunka"?? Ta k'arasa maganar cikin sigar shagwa6a kamar za ta yi kuka.

Rufe idonsa ya yi sosai, sannan ya bud'e su akan fuskar Fateema, ya ce" ke"a tak'aice. Zaro ido Fateema ta yi tare da nuna kanta da yatsa, "ni kuma"??
Gyd'a kai ya yi alamun hakan ya ke nufi,sannan ya yi murmushi ganin yadda take masa wani kallo na rashin fahimta, ya ce
" I'll miss yhu Fatyna, rashinki a tare da ni, ji na ke tamkar na rasa wani 6angare na jikina, zan yi missing wannan daddad'an k'amshi dake tashi daga jikinki, k'amshin parlourn ki da d'akin ki... nd everything from yhu babe"

********

Murmushi Teema ta yi tare da fad'in
"common! Qalby I guess two days ne kawai, za ka yi ka dawo wurina".??
"haka Nadeeya ke so,amma ni na gaya mata idan ta yi girki yau gobe ki yi, ku rik'a kwana d'ai d'aya kawai".

Shiru fateema ta yi tana nazarin maganarsa, don duk ta fahimce abinda ke damunsa,don d'an zaman da suka yi ta fuskanci Farouq mutum ne,mai matuk'ar son k'amshi, da k'amshi kawai za ka iya siye zuciyarsa, don haka ta k'udiri aniyar zage damtse don ganin ta faranta masa ta kowace fuska, haka ba za ta yiwa Nadeeya k'eta ba, za ta lurar da ita, idan ta fahimceta shi kenan, don akwai gyara sosai a lamuranta, domin ba ta Jin ko d'an turaren nan, na stick Nadeeya na sakawa a d'akinta, domin idan ta shiga part d'in ta tana Jin d'an wani bashi-bashi yana tashi wanda ko ita da take mace Allah Allah ta ke ta fito, bare kuma namiji, ko ajikinta ba ta ji tana saka turare yanda ya kamata".

Gyara kwanciya Farouq ya yi, yana shirin komawa barci, sai a lokacin Fateema ta ankare ta ce
"Qalby ni kam ina ga, da ka hak'ura an yi yanda take so, ni dai in don ta ni ne, na amince da hakan, zai fi ma a rik'a kwana biyu,don mafiyawancin gidaje na ga haka ake yi".

"ni dai to ban amince da haka ba, ba zan iya rashinki har na kwana 2 ba".
"haba Qalby, ka ga za ta ga kamar an danne hakk'inta ne, tunda har ta riga ta gaya ma ga yadda ta ke so, in dai don k'amshin part d'in nan ne, duka turarukan da air fresheners da na ke using da su anan, duka na maka amfani da su a part d'in ka, ai ka shiga ka ga ni ko"???
Ta k'arasa maganar tare da zuba masa ido, "hmm" kawai ya ce, don da alama har barci ya fara fizgarsa.

Bin shi ta yi da kallo daga k'arshe, ta sauke idonta akan agwogwan da ke manne a bangon d'akin, 11:43am ya nuna,zaro manyan idanunta waje ta yi, tana cewa har lokaci ya tafi haka, a hankali ta sa hannu a jikin sa ta fara  k'ok'arin tashin shi, duk da bata son tashin shi idan yana barci amma ya zama dole, don kar ya shiga Hak'k'in Nadeeya, gwanda ya je can part d'in ta ya kwanta, ko part d'in sa,don abinda ba ta so a mata, ba za ta bari a yiwa wata ba, d'an girgiza shi ta fara tana k'okarin d'aga shi daga jikinta... Ta ji an turo k'ofar an shigo ba ko sallama.

Nadeeya ce ta shigo, k'ik'am ta yi a kan su ta zuba musu ido, cike da masifa ta fara magana "aa dole ka manta da k'urar da ta kwasoni, kana nan ta wani rungumeka sai ka ce d'an goye ana nuna maka karuwanci".
Fateema ba ta ce komai ba illa k'okarin d'aga kan Farouq daga cinyarta da take yi.
Farouq da tun shigowarta ya farka ya fara magana ba tare da ya tashi daga kwancen da yake ba, ya ce
"yanzu shigowar da kika yi ba tare da neman izini ba kin kyauta kenan"???
Nadeeya ba ta ce komai ba illa karkad'a jiki da ta fara.
Don haka Farouq ya cigaba, "sannan mai kika tarar ana yi da har kike kiran karuwanci,mace ta zama sama da karuwa ma in dai a gidan ta ne ai ba laifi ba ne...

 Nadeeya ta katse shi ta hanyar cewa " Farouq ya ishe ni haka, ya za a yi a gaban yarinya ka zo kana ci mun fuska, dama an ce in dai namiji ya yi sabon aure, dole sai ya wulak'anta ta gida, to na gode da ka fara gwada mun kalar ka ta d'a namiji tun kafin aje ko'ina", daga haka ba ta kuma cewa komai ba ta nufi hanyar fita daga d'akin.




Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [9/2,16, 7:59 PM] phatyma : ▪BALLAGAZAR MACE ▪43

©Mrs Saif


Ranta a matuk'ar 6ace ta koma part d'in ta, ta yada zango a parlor tare da zubewa akan d'aya daga cikin kujerun wurin.
Yanzu a duniya ba ta da wata matsala da ya wuce Fateema, ta tsani ta bud'e ido ta ganta cikin gidan, wani mahaukacin kishinta take ji,tashi ta yi daga zaunan da take ta fara safa da marwa, don duk ta lalubo mafita amma ta kasa samu, daga k'arshe dai ta yanke shawarar yin amfani da magungunan da mai maganin mata ta bata, ko ta dace hankalin Farouq ya jiyo gareta ita kad'ai.

Da wannan tunanin ne ta samu hankalinta ya d'an kwanta, don ta d'au alwashin in dai hankalin Farouq ya dawo gareta lallai sai Fateema ta raina kan ta a cikin gidan, don zama gidan sai ya mata wahala.

Farouq kuwa tun bayan fitar Nadeeya Fateema ta takurashi sai ya fito zuwa part d'in Nadeeya, ba don ya so ba ya fito, da kamar ya wuce 6angaren sa, sai kuma ya ga rashin kyautawar hakan don haka ya fara shiga part d'in Nadeeya.
Ko da ya tarar da ita sai wani cin magani take, shi dariya ma ta so ba shi ya dai gimtse ya ce
"yanzu me ye abun fushi, mu fa ki ka yiwa laifi, sannan ki juye abun ya dawo kan mu"???
"haka ma za ka ce, bayan sanin kanka ne kun shiga hakkina, kamata yayi ace zuwa yanzu ka yi sallama da amaryarka ka dawo wurina, har zuwa lokacin da za ta kuma kar6ar girki".

'au haba, dama haka mu ka yi dake? Ni fa ba wasu k'aidoji da za ki gindaya mun, don nasan abinda na ke yi, ba ki isa ki ce mun wai don kin kar6i girki ba, shi kenan sai na fito daga d'akin Fateema tun da asuba na dawo gun ki, all i know yau kwanakin ne, ba zan kuma d'auka na kai wa Teema ba, don nima ina da burin adalci a tsakanin ku."

"hmm!haka dai ka ce", Nadeeya ta fad'a tare da K'arasawa cikin d'aki don d'auko Ansar da ya fara kuka, da alama tashinsa ke nan daga barci. Saboda haka shi ma Farouq ya fice daga parlourn don dama fita yake son yi duk da ba aiki zai je ba, don hutunsa sai gobe Monday zai k'are, amma yana so ya je gaishe da Ummansa.

[9/2, 7:59 PM] phatyma ▪BALLAGAZAR MACE ▪44

©Mrs Saif


Tun bayan fitar Farouq Nadeeya ta fara had'ed'an kayan da za ta yi amfani da su, daga na sha har zuwa na inserting, maimakon ta had'a da gyara lungu da sak'o na jikinta, a'a ba ta san da haka ba ta dai yi wanka yau, shi ma bur-bur ba yanda ya kamata ba.

Sai bayan takwas na dare ya dawo don Umma ta d'an tsaida shi da hira, yana shigowa ya tarar da Nadeeya sai cika take tana batsewa akan ya jima bai dawo ba, ko sannu da zuwa ba ta yi masa ba ta hau yi masa k'orafi.
"yanzu Farouq abinda ka yi ya dace ina fa gani kwanan ba ka zuwa ko'ina kana mak'ale a d'akin amarya, amma saboda yau mak'iyarka ta kar6i girki shine sai yanzu ka ke dawowa gida"??ta k'arasa maganar da rawar murya alamar kuka ya taho mata.

Tausayinta Farouq ya ji, ya tako zuwa inda take zaune ya ce "haba Nadeeya ki daina fad'an ke mak'iyiya ta ce in da ina k'in ki da ba zan zauna da ke ba, har kawo wannan lokacin, ke ki ka kasa fahimta ta tun tuni, kuma daren da na yi Umma ce ta tsaidani".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "shi kenan".
Ganin ta sauko ya sa Farouq cewa "bari na je na watsa ruwa sai na fito".
"to " ta ce da shi sannan ya haura sama don zuwa part d'in sa.

*****9:45pm
Ya fito cikin brown jallabiya, sai k'amshi ke tashi daga jikinsa main parlourn su ya zauna yana jiran fitowar Nadeeya cikin d'an k'ank'anin lokaci kuwa ta fito, tana fad'in" bari a kawo maka abinci".
Bayan ta d'auko abincin ta ajiye akan dinning table, ya ce" Fateema fa"??
Sai da ta 6ata fuska ta ce "na saka su Raleeya su kira ta ci, amma da ta zo bud'e abincin kawai ta yi ta ce
" ta k'oshi".
K'wafa ta ja, tace "ai yarinyar nan sai na koya mata hankali sai ta rik'a nuna kamar ta fi kowa".
Bai ce da ita komai ba, ya nufi dinning area, bud'e abincin ya fara yi tuwon shinkafa ne amma ya wani cakalkale daga ga ni an sakarwa shinkafar ruwa fiye da k'ima, sai miyar d'anye ku6ewa wadda itama ga ta nan ne dai, don yana bud'e miyar k'arnin naman da aka yi miyar ya dake hancinsa tamkar ba a dafa shi ba.

Rufewa ya yi sannan ya mik'e yana shirin barin wurin, cikin rashin fahimta Nadeeya ta ce
"ina za ka je kuma"??
"zan je duba Teema ne".
Bin shi ta yi da kallo tare da ta6e baki, bayan ya juya baya ta bi shi da harara.

Teema na zaune a cikin d'akinta ta sauya kayan jikinta zuwa wadatacciyar night gown, plate ne d'auke da indomie da fried egg, sai ruwan lipton a cup da take kur6a a hankali kasancewar ta ji cikinta duk ba dad'i, ta kasa cin abincin.

Farouq ya turo k'ofar ya shigo la66ansa d'auke da sallama, amsa sallamar ta yi sannan ta d'auke kan ta daga kallonsa, haka kurum itama yanzu sai ta ji tana tsakanin kishinsa, yau ita d'aya zata zauna kamar mayya, sai kuma wata zuciyar ta ce da ita "haba fateema ki zo ki aurewa mace miji, don zai koma wurinta shine har za ki fara Jin haushi, to ita kuma kwanakin da ya kwashe tare da ke sai ta mutu ke nan".

Da wannan tunanin ta k'arfafa zuciyarta har ta k'wak'ulo wani murmushi ta ce
"sannu da shigowa".
Bai amsata ba illa mazauni da ya yiwa kan sa, sannan ya kar6i cup d'in hannunta ya yi kur6a d'aya ya ajiye, tare da cewa "Fatyna ban yarda da wannan fake murmushin ba don na hango damuwa a idanunki, gaya mun me ke damunki"???

[9/2, 7:59 PM] phatyma : ▪BALLAGAZAR MACE ▪44

©Mrs Saif

Murmushin ta kuma yi ta ce "ba komai".
"ban yarda ba akwai komai gaya mun what's wrong with yhu".
"nothing, but... am just feeling lonely".
"olright, ya fad'a tare da watsa hannayensa duka biyu, sannan ya cigaba da fad'in "na fasa zuwa wurin Nadeeyar bari na yi zama tare da ke", ya k'arasa maganar tare da d'aga mata kira.
Zaro ido ta yi waje tana fad'in "a'a wallahi ba haka nake nufi ba, ka yi hak'uri ka je wurinta, bana son ka janyo mun magana, ko ba haka ba ma, ba kyau abinda ka ke shirin yi".

Sosai dariya ta zowa Farouq ya danne, don yadda ya ga duk ta rikice, yana sane ya gaya mata haka don ta saki ranta.
Ya ce "okay, yanzu ki ci abinci sosai ina ga ni, idan har kina so na tafi, kin ga nima yunwa na ke ji, amma ganin ki cikin wani yanayi ya sa na manta da ita".
"a haba! Ka zo mu ci wannan kawai a zai ishe mu".
Ba musu ya zauna, ita kuma ta tashi ta d'auko masa folk, sannan suka fara ci, Farouq bai an kara ba ya kwashe abincin tas sai maimaita dad'insa ya ke yi.
Fateema kuwa sai dariya take masa, ta ce "ai wannan agurguje na yi shi, don na d'an samu abinda zan sakawa cikina, da na san za ka ci ai wanda ya fi wannan zan dafa Maka".
Murmushi Farouq ya yi ya ce "Allah Fatyna amma kuwa zan yi farin ciki sosai ki ka kasance gwana wurin iya kirki".

******
Da haka dai ya yiwa Fateema sallama ya nufi sashen Nadeeya, nan ma wata rigimar ce ta 6arke, don ta ji haushin dad'ewar da yayi d'akin Fateema, bayan nan kuma ya ce "sai dai ta biyo shi part d'in sa, don shi tun daga parlourn ta da k'yar yake iya had'iye yawu, yanda ya ji gurin na wani tsami-tsami kamar an ajiye kwanannen abinci.
Yayin da ita kuma Nadeeya ta tsaya kai da fata, sai dai ya kwana anan 6angarenta, tunda amarya ma bin ta, yayi ba ita ta je ba.
Ganin za ta 6ata masa lokaci yasa ya fice daga parlourn ya bar ta tsaye, don ya gaji da shak'ar gubar d'akin ta.

Ganin ba Sarki sai Allah ya sa ta ajiye girman kai ta yi shirin bin sa, ko ba komai tana da buk'atar mijinta, sannan tana son gwajin magungunan da aka ba ta.

Farouq dai kusan duk abinda ya wakana tsakanin sa da Nadeeya zan iya cewa ba a hayyacinsa ya ke ba, tsabagen hamami da warin dake tashi a jikinta, don ji yake kamar har tafi da, ko don ya saba da k'amshin Fateema ne???
Ya jefawa kan sa wannan tambayar, don sai yanzu yake tabbatarwa kan sa da lallai Nadeeya ba za ta rasa warin k'ashi ba.
Juyawa ya yi gefen da take kwance yana kallonta, tana ta shak'ar barci hankalinta kwance, wanka ya je yayi sannan ya koma d'akin ya d'auki pillownsa ya koma parlour ya kwanta.
Abinda Farouq bai sani ba cushe-cushen da Nadeeya ta yiwa kan ta shiya k'ara tsananta warin jikinta, saboda ta yi cushe-cushe da yawa sannan ga shi ba wata cikakkiyar tsafta, don haka abin ya had'e mata biyu.

******
Da k'yar Farouq ya ga kwana biyun Nadeeya ya wuce don ji yake kamar yana prison, yau kuwa cikin annuri ya tashi, don Jin sa yake kamar wanda aka yiwa gafara.
Kamar yadda ya saba fita haka yau ma shirya ya fita.
Nadeeya ko yana fita itama ta sa kai ta fice, don tana son had'uwa da mai magani.....



Mum Twins 😘
[10/16, 4:38 PM] mrm kd: [9/5, 5:29 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪46

©Mrs Saif

Fateema na fitowa ta ga bata nan don haka ta kira su Raleeya (masu aiki) tana tambayar in da Nadeeya ta je, suka ce "ba su sa ni ba, don suma ta kai musu Ansar ta ce su rik'e shi har ta dawo".
Hannu ta sa ta kar6i yaron duk ya yi wani kaca - kaca ta ce "ku yanzu don Allah ko yaron ba za ku iya gyarawa ba, to miye amfanin ku ke nan"???
Shiru suka yi suka kasa cewa komai, saboda haka Fateema ta cigaba" yanzu ku kalli parlourn nan, sannan ku kalli jikin ku tare da nuna qaramar da ya tsa ta cigaba da cewa "ke kam ina ga tun da na zo da wannan kayan na ke ganinki, ba ki chanza ba, hatta aikin da aka kawo ku yi ba wani yi kuke yi ba iya kacin ku ku yi girki ku ci ku je ku kwanta, ba ruwanku da gyaran gida,kalli parlourn nan bana Jin yau kun gyara shi"??

Babbar ce ta fara magana cikin sark'ewar murya "hajiya ai mu ba a sanar da mu aikin da za mu yi ba, mu dai mun san hajiya na cewa mu yi girki kuma duk...
Fateema ta katseta" ku ba ku san abin da ya kamata ku yi ba sai an gaya muku, ko anan gidan kuka fara yin aiki".

Girgiza kai ta yi alamar a'a, "don haka ku saurari abinda zan gaya muku domin idan ta ni ce bana buk'atar wasu 'yan aiki amma tun da an kawo ku, ba ni da ikon korarku amma zan gindaya muku sharud'a don ni bana buk'atar girkinku duk ranar girkina.
Don haka daga yau idan kun tashi a gyara parlourn nan ciki da waje, da kitchen da toilets na nan da na 6angaren ku, daga cikin gidan nan har farfajiyar gidan nan bana son na ga ko tsinke a k'asa aikinku ne wannan,zan nuna muku duk yadda za ku yi, idan maman Ansar za ta had'a mu ku da gyaran part d'in ta shi kenan amma ni dai wad'annan ayyukan na ke so duk ranar aiki na".

D'an rusunawa suka yi suka ce "shi kenan hajiya yanda kike so haka za'a yi".
Fateema ta ce "yawwa bari yanzu na je na yiwa Ansar wanka sai ku fara aikin, amma kafin nan je ki d'auko mun kayansa set d'aya na samu na saka masa idan na masa wanka".

Jim kad'an Raleeya ta fito ta ce "hajiya ai kayan nasa duk ya yi daud'a iya wanda na gani".
Juyawa Fateema ta yi tana kallonta cike da mamaki ta ce "yanzu don Allah Raleeya kayan Ansar ba za ku iya wankewa ba har sai sun yi datti gaba d'aya"?
K'asa raliya ta yi da kanta alamun Jin kunya ya bayyana a fuskarta.
" shike nan yanzu ki je ki kwaso kayan ki bawa Habi ta wanke, yasso sai ke ki fara wani aikin kafin ta gama".

Haka kuwa aka yi nan da nan suka hau ayyukan gidan Fateema na taya su, har suka gama yayin da ita kuma ta yiwa Ansar wanka ta gyara shi tsaf sai k'amshi yake yi, zuwa lokacin har ta gama girkin rana amma ko alamar dawowar Nadeeya babu...
[9/5, 5:29 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪47

©MRS SAIF

K'arfe uku Teema ta fara preparing dinner, zuwa lokacin zuciyarta cike take da tunanin inda Nadeeya ta je ta bar
yaro, duk da dai ta yayeshi amma ita a tunaninta bai kamata ace ta dad'e kamar haka ba, shi kam yaron ko ajikinsa sai wasan sa yake yi hankali kwance.

*****
Nadeeya kuwa tunda ta fita bata zame ko ina ba sai gidan maman Nabeela ranta a jagule ta shiga gidan, maman Nabeela na ganinta ta san ba lafiya ba.
Da hanzarinta ta nufeta tare da fad'in "lafiya Nadeeya na ganki da sassafen nan"??

Wata katuwar ajiyar zuciya ta sauke ta ce" ina fa lafiya ai yau matar nan ko ni ko ita don sai ta biyani kud'i na,wai har ni zata yaudara cewa ta yi muddun na yi amfani da magungunan nan tun daren ranar zan ga sauyi, zan kuma sha mamaki".
"au bai yi ba ne"?? Maman Nabeela ta tambaya.
A na sha mamaki amma fa na wulak'anci, don ba ki ga yanda muka k'ark'e da Farouq ba, don maganin tamkar bak'in jini ya k'ara mun a wurinsa, baki ga wulak'anci ba, har wani d'auke numfashi ya ke yi idan muna tare, sai ka ce wanda ke tare da ja6a, wallahi maman Nabeela daren jiya na k'unshe bak'in ciki, don duk son 6oyewar da yayi sai da na gano shi don yanayinsa kawai ya nuna mun komai yake yi don dole ne don ransa na so ba."

Ajiyar Numfashi maman Nabeela ta yi sannan ta ce "ni dama ai kin ji sai da na yi magana a gabanta na ce mata, na matsin nan warinsa ya yi yawa, ta ce ai idan kin yi amfani da turarukan tsugunno da miski ba za'a ji warin ba, kuma duk Kin yi haka"??
Ta6e baki Nadeeya ta yi ta ce" ni ba abinda na yi, kasa kud'i irin haka ka saye magani sannan sai ka had'a da wani turare-turen jiki ba zan iya ba gaskiya, ni na fison yanke take".
Shiru maman Nabeela ta yi don babbar matsalar Nadeeya k'in d'aukar shawara, duk da haka ta ce "kin san fa su magungunan nan musamman na matsi matsala ne da su, sai kin san irin wanda za ki na amfani da shi, tabbas akwai masu kyau da inganci, amma ni wanda aka ba ki tun fil'azal warin da suke yi bai mun ba, har da wai wani kashin birbiri ka kuma kwasa ka cusa a jikinka guri mai k'ima da daraja ga duk wata 'ya mace, ni don na ga kin rud'e akan kayan ne kawai na yi shiru amma...

"don Allah ni tashi mu je gidanta tun bata kad'a ta je wani wuri ba, duk Kin cika ni da surutu".

Ko da suka je gidan ba su tarar da ita ba har ta fita sai yaranta' yan mata a cikin gidan, don haka Nadeeya ta ce "ba ta ga ta tafiya ba har sai ta jira dawowarta".

Maman Nabeela da ta ji shiru ba ta dawo ba, ta yi gaba don tana da abin yi a gida ta bar Nadeeya anan tana jiran gawon shanu.
[9/5, 5:29 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪48

©MRS SAIF


K'arfe 5:47pm zuwa lokacin Fateema ta gama aikinta tsaf, in da ta dafawa Qalbynta had'd'ad'en girki mai kyau wanda zai saka kunnensa motsi, oriental rice ne ta dafa tare da nugget fish, kasancewar ta fuskanci Farouq akwai son kifi sai paw-paw slush wanda ya ji k'ananan ice a ciki.

Hatta su Raleeya da suka ci abincin sun mutu da dad'insa don tamkar za su tafi da yatsun hannunsu don gard'in da suka ji yayi musu, tambaya Teema ta sha ta a wurinsu ta yadda ake girkin, ita kam murmushi kawai take musu tana ba su amsa, don d'an zaman da suka yi da ita sun fuskanci ba ta da wulak'anci ko kad'an ga ta da faran-faran ga jama'a.

***

Ita kan ta Fateeman ta kuma yin wanka ta cake cikin wasu english wears yellow and black rigar yellow skirt black 'yar k'arama ce rigar mai siririn hannun ko cibiyarta  ba ta rufe ba, gaban rigar net ne black colour wanda ta cikin net d'in ba abinda ba a gani, shi kansa skirt d'in d'an k'arami ne don bai kai guiwarta ba ga shi very tight don ko motsin arzuki baya barin ta ta yi, ganshin kanta tattare shi ta cure a tsakiyar kanta sannan ta matse da ribbon yellow, light makeup ta yi daga powder sai lipstick pink da ta saka sai kwallin da ta zizara a kyawawan idanunta mai k'ara musu haske da kyau, simple Indian earing ne a kunnenta golden colour da stones black.

Teema ta yi kyau sosai tamkar 'yar tsana, kan three seater ta zauna ta mik'e k'afa abinta, a main parlour ta zauna don a cewar ta ta gaji da k'ullewa cikin part d'in ta ita kad'ai kamar mayya, gwanda ta zauna anan ta sha iska ko banza za tana Jin motsin su Raleeya.

Gaba d'aya hankalinta na kan TV tana kallon wani series, Ansar na gefenta yana shan sweet abinsa, tun daga gate d'in gidan ya ji wani k'amshi ya cika masa hanci take ya ji zuciyarsa ta yi wani haske, parking ya yi ya fito a lokacin gaba d'aya k'amshi gidan ya gama rikita shi, don ya rasa wanne ya fiso a ciki, k'amshin girkin da yake ji yana tashi ne ta wani 6angaren gidan ko kuma na wani mayataccen k'amshin turaren wuta wanda 'yan kwanakin nan har ya saba da daddad'an k'amshin sa a part d'in Fateema.

****
Tsaye yake k'yam yana k'are mata kallo wanda ko alamar tsayawarshi ba ta ji ba, bare sallamar da ya yi, K'arasawa ya yi inda take zaune gaba d'aya ya sa hannu ya d'agata sama yana juyi da ita kamar irin babba ya d'auki yaro yana masa wasa.
Da farko har ta d'an tsorata da ta ji ta a sama ba tsammani amma tana ganin Farouq ne sai ta sakar masa wani lallausan murmushi tare da k'ok'arin saukowa amma ko alama ta kasa in ban da dariya ba abinda Farouq ke yi, a haka Ansar da ke gefe a zaune ya taso shima yana mik'awa Abbansa hannu alamar ya d'auke shi, Farouq ko lura da shi bai yi ba don gaba d'aya Fateema ta gama rikita masa lissafi, sai Fateema ce ta ankare da shi a haka ta mik'o hannunta zuwa k'asa da zummar d'aukan Ansar, sannan Farouq ya lura da shi, duk da haka bai sauke Fateeman ba, bai yi yunk'urin d'aukan Ansar ba, sai Fateema ke ta yunk'urin kai hannu ta d'auke shi ta kasa, Farouq sai dariya ya ke mata don ta masifar masa kyau a hakan da take ko don shine first time da ya ganta da english wears, hatta Ansar sai ya ga yaron ya masa kyau yau don har haske ya qara.
Maganar Fateema ce ta katse masa tunani
"don Allah Qalby ka saukeni na d'auke shi, murmushi ya sakar mata tare da kwaikwayon yadda ta yi magna ya ce "o'o ba zan sauke ki ba".
Sannan ya k'ara wullata sama ya cafe, har da 'yar k'ararta alama ta tsorata.
Dai_dai lokacin Nadeeya ta shigo idonta ya sauka kan su, wani tarin bak'in ciki da tsananin kishi ne ya lullu6e mata zuciya, cike da tsiwa da masifa ta fara magana...



Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪49

©MRS SAIF


"Amma wallahi an yi girman ka wai yanzu kai ko kunya ba ka ji, ka biye mata ko shakkar wani ya shigo ya sameku haka ba ka yi ,kalli kayan jikinta sai ka ce wata tsohuwar ashawo da haka ai... Farouq ya yi saurin katseta ta hanyar d'aga mata hannu sannan ya dire Fateema ya fara magana daga gani shima ransa ya 6aci da Kalaman na ta.
"wai ke make damunki komai abin k'orofi ne a wurinki, daga yau duk abinda kika gani na ki ido ne, idan ba za ki iya ba ki bar wurin that's all, and then ina kika je na ga kin fito daga waje"??

Nadeeya da haushi ya cikata tun fara maganarsa ta kasa cewa uffan don taikaci, illah harare-harare da take yi.
"uhmm say something bakinki yana motsi kin kasa magana".
Wurga masa harara ta yi ta k'ara tsuke bakinta, don yadda take jin zuciyarta na tafasa kamar ta zabga masa mari ta tabbatar idan har ta furta wata kalma dole ta kasance masa mai d'aci, so ya fi kawai ta kama bakinta ta yi shiru".
"Nadeeya ki na ji ina miki magna kin wa mutane shiru".
Can k'asa-k'asan murya ta ce "mak'ota na je".
"ban hana ki zuwa ko ina ba sai kin tambaye ni"??
Banza ta masa kamar ba ta ji shi ba.
Ganin haka yasa Fateema mik'a hannu d zummar ta d'aukan Ansar ta yi gaba, don ba ta so Nadeeya ta ga kamar ta tsaya Jin abinda ke tsakaninsu.

Ai kuwa tana mik'a hannu Nadeeya ta doke hannun tare da fad'in "munafurcinki ya tsaya iya gun ubansa kar ki sake ki kuma ra6ar mun yaro idan ban da rashin zuciya irin naki ki yi ta cusa kanki in da ba za'a kar6eki ba,wannan ai shine cusa kai ba kwarjini".
Fateema ba ta ce da ita k'ala ba illa nufar shashinta da ta yi, ta bar ta da Farouq suna cigaba da fafatawa.

*******8 months later

Haka rayuwa ta cigaba da gara musu, Nadeeya kwata - kwata ta k'i fuskantar Fateema komai ta yi haushinta take ji, amma ita kanta ta san Fateema ta yi mata fincikau ta ko ina musamman a zuciyar Farouq.
Amma abin mamaki duk ranar da Fateema ke girki kowa na gidan murna yake yi, har Nadeeyar saboda sun san ranar za su kwashi girki mai dad'i, ranar girkin Nadeeya kuwa sai dai a bawa almajirai, zuwa yanzu kuwa Farouq ya saba da abincin Fateema ta yanda duk inda ya je ya dawo sai ya zo gida zai ci abinci, tun Nadeeya na mita har ta gaji ta hak'ura don komai dare idan ya kasa cin abincin da Nadeeya ta dafa ranar girkinta zai tashi Teema ta dafa masa wani, a dole Nadeeya ta hak'ura da hakan tunda ita ba zata iya yi masa kalar wanda ya ke so ba, don yana da kadara irin Fateema ba zai rik'a bin gidajen cin abinci ba.
Sai dai girman kan da Nadeeya ta dorawa kan ta, ta kasa sauke shi duk yanda Fateema ta so nuna mata hanya sai ta rufe idonta ruf ta k'i bi, k'arshe sai cin mutunci da zagi ya biyo baya.

Zuwa lokacin Nadeeya na d'auke da ciki na kusan 6 months, don haka Fateema ta kar6i girkin gidan gaba d'aya, ga shi lokacin karatu ya musu zafi don suna second semester 300 level, amma duk da haka ba ta ta6a nuna gajiyawa ba, ta tsara ayyukanta dai_dai yanda ba zata wahala sosai ba.

A lokacin Farouq ba shi da wani buri da ya wuce ya ga Fatynsa da ciki yanda ya ga tana masifar son yara,don yana ganin yadda Nadeeya ke mata wulaqanci akan Ansar tana shanyewa.
Fateema har ta fuskanci hakan sai dai ta tabbatar komai lokaci ne, sai lokacin da Allah ya nufeta da samu zata samu duk zumud'inta.


▪BALLAGAZAR MACE ▪50

©Mrs Saif


Sanye take da wata riga peach colour da ratsin sky blue, rigar armless ce sai wata igiya da ake zagaye wuya da ita a d'aure da kad'an tsayin rigar ya rufe cinyoyinta, sai dai ta bud'e daga k'asa sharp d'in umbrella iya sama ne kawai a tsuke, k'ananun calba ne akanta wanda suka zubo har kafad'arta, ta yi kyau har ta gaji.

Sai safa da marwan jera abincin kan dining table take yi, Farouq ne ya shigo da murmushi d'auke a fuskarsa ya kar6i trayn hannunta tare da cewa
"haba Fatyna na ce idan ina nan ki rik'a kawo wani abun ina tayaki, yanzu sai mai za a kuma d'aukowa ranki ya dad'e"??
Dariya Teema ta yi sosai don yanayin sigar da yayi maganar ya bata dariya kamar irin d'an aiken tan nan.
"duka na gama jerawa fa da ma wannan ne na k'arshe".
"okay".
Zaunar da ita yayi a d'aya daga cikin kujerun d/table d'in ya d'ago fuskar ta yana kallonta almost 5mnts bai ce k'ala ba illa ido da yake bin ta da shi
"Qalby lafiya kuwa"??

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce
"babe I really don't know where to start, don ba ni da bakin magana, I didn't have words to express how i feel about yhu, Teemana kin zama jinin jikina a kowane second da numfashi na ke fita tare da kaunar ki ne, kin gama siye zuciyata ta kowane fanni, I really luv yhu so very much, kin ga yanda kayan nan ya miki kyau kuwa, you're more than beautiful."

"Thanks " ta fad'a tare da mik'ewa don ta fara serving nasa kafin fitowar Nadeeya, tana Jin dad'in yanda Farouq ke yabonta amma ta fison in suna part d'in ta ko na shi don bata son masifar Nadeeya.
" me kika dafa mana ne,? Don na ji k'amshi har ya cika mun ciki kafin na ci".
Murmushi ta yi ta ce
"cous-cous with veggies sai grilled fish da na maka, don na ga ka kwana biyu ba ka ci mutumin na ka ba".
Murmushi sosai Farouq ya yi, ya ce
"fatyna shi yasa kike k'ara shiga raina don duk wani abu da nake so, kin san shi, yanzu kalli kifin nan kin iya sarrafa shi nau'i kala_kala ba abinda zan cewa Allah sai dai godiya".

Nadeeya ce ta k'arasa wurin da suke zauna ta tsaya tare da 6arkewa da wata mahaukaciyar dariya, don tun d'azu tana tsaya a k'ofar parlourn tana Jin duk abinda suke fad'a.
Sai da ta yi dariyar ta gama ba wanda ya tanka ta, sannan ta fara magana "ni kam ku na ba ni mamaki kullum cikin soyayya kamar kwa had'iye junanku, amma har yau cikin nan an kasa samu sai mu da ba' a so muka yi, ai ni wannan soyayyar ta ku sam bata birgeni ba kyau a ce zuwa yanzu kina nan da tsohon ciki, kin ga da kin huta da wannan d'an banza son yaran naki, amma ina sai soyewar amma har yanzu result ya k'i fitowa"...



Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/8, 7:20 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪52


©MRS SAIF


********Bayan wata Uku********

Fateema na zaune a parlour hannunta rik'e da wani hausa novel kasancewar suna cikin hutu kuma zaman haka duk ya isheta, mai suna Muguwar sakayya, littafin ya tafi da ita sosai duk da haka lokaci zuwa lokaci takan kalli part d'in Nadeeya, don ta yi mamakin har zuwa yanzu k'arfe 2:30 ba ta lek'o waje ba tun daren jiya.

Ba zato ta jiyo muryar Faty na k'wala sallama, k'arasowa ta yi cikin parlourn ta ce
"oh! Friendy wai me kike yi haka ina ta sallama shiru".
Cikin murna Fateema ta rungumeta ta ce "sorry tawan ban ji ba ne, ya gida ya su Umma"??
" lafiya Lau".
Ta fad'a tare da neman wurin zama.
"wai ni kam yau na ji gidan na ku shiru lafiya "?
Lafiya Lau, su Raleeya na part d'in su Ansar kuwa kin san yana Dutse, sai dai Mamansa ce ban ji motsinta ba".
Ta6e baki ta yi ta ce "hmm ita ta sa ni kar ma ta fito, ni ai Aunty Nadeeya ta gama ba ni mamaki wai har ni zata rik'a gaba da ni, ko magana na mata ba ta amsawa".

Fateema ta ce "bari ke dai ai abun na ta sai addu'a, yanzu ki lek'a ki gaishe ta kin san ta da d'an banzan k'orofi".
"ba in da zani ni, duk k'orafinta sai dai ta yi ta gama tunda ai ba zata dake ni ba ko".
"eh amma kin san idan ta gayawa umma za ta miki fad'a".
"Ai duk Umma ce ke d'aure mata gindi take abinda ta ga dama". Cewar Faty.

"Yanzu dai don Allah namesake je ki, ki dubata duka duniyar nawa take kowa ya yi nagari kansa".

*****
Da k'yar Fateema ta shawo kan ta, ta nufi part d'in Nadeeyar, sai dai yanayin da ta tarar da Nadeeyan ya d'aga mata hankali ba ta san lokacin da ta fito hankali tashe tana kiran Fateema.
Da gudu suka burma cikin d'akin Nadeeyar, rud'ewa da Fateema ta yi har ba a magana, don dukkan su ba wanda ya ta6a ganin yadda ake labour sai yau, musamman ita Nadeeya ta wahala ba kad'an ba don duk ta yi wani wujiga-wujiga numfashinta har wani sama da k'asa yake yi kamar zai d'auke.

Cikin rashin sanin taikamammen abin yi Fateema ta fara magana har da 'yar k'wallar tausayi a fuskarta,"sannu sannu... "abinda ta ke ta maimaitawa kenan.
Faty ce ta yi dabaran kiran Farouq ta sanar da shi.
Shima cikin tashin hankali ya bar office ya nufo gida,yana zuwa ba su tsaya wani abu, suka nufi asibiti kowa hankalinsa a tashe.

K'arfe 6:39pm Allah cikin hikimarsa ya nufi Nadeeya da haihuwar ' yar ta kyakkyawar gaske, ba inda ta baro Farouq dogon hancinsa ta d'auko da manyan idanunsa sai dai hasken fatarta na Nadeeya ne,don fara ce sosai don har tafi Nadeeya fari ko don ita Nadeeyar ta dafe ne oho!.

Har zuwa lokacin su Fateema na asibitin, suna zaune a reception sun yi jugum-jugum wata nurse ta fito da baby ta mik'iwa Farouq tare da masa congratulations.

K'ok'arin kai hannu yake yi ya Kar6i babyn amma ina Fateema ta riga shi kai hannu ta kar6eta, murmushi Farouq ya yi tare da mai da hannunsa baya yana lek'en fuskar babyn daga hannun Fateeman.

"wow! Hasbunallah Wani'imal Wakil" Fateema ta fad'a tare da zaro duka idanunta waje, "friendy zo ki ga babyn nan don Allah".
Haka Faty ta zo ita ma ta gama santin kyan babyn Farouq yana kallonsu yana murmushi, a ransa ya ce "ina ma baby nan ta tsatson Fateema ta fito da farin cikin da ya ke ciki sai ya linka wanda yake yi a yanzu sau dubu,don yasan yanzu wuyarta Nadeeya ta wartsake ba lallai ta amincewa Fateeman ba ta rik'a ra6ar babyn ba,don yasan halin ta sarai na son k'untatawa Fateema ta wannan hanyar, daga k'arshe ya jadadda godiyarsa ga Allah na wannan ga garumar kyauta da ya masa.



Mum Twins 😘
[9/8, 7:20 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪53


©MRS SAIF


washe garin ranar da ta haihu aka sallamo musu daga asibiti, Nadeeya ta warke ras kamar ba ita ba, ko da ta isa gida ta tarar da 'yan uwanta sun iso daga dutse.
Duk wanda ya kar6i babyn sai ya ya ba da kyawun da ta ke da shi.

Fateema dai tsakaninta da baby sai hange daga nesa don yadda Nadeeya ta fuskanci tana son yarinyar yasa duk wata hanya da zai sa babyn ta kai hannun Fateema ta datse, k'iri-k'iri idan ta zo d'aukan ta za ta ce bacci take yi, ko kuma yunwa take ji da dai sauran dalilai, idan ma fa da idon jama'a a wurin take mata wannan kawaicin, idan kuwa ba kowa sai dai ta ce ba za ta ba ta ita ba idan ta yi zuciya ta haifi ta ta.

Farouq ya sha yi mata fad'a akan hakan, yana nuna mata duk wanda ya ce yana son naka ya gama maka komai sai dai hausawa sun ce "wanda ya yi nisa ba ya Jin kira". Don kuwa Nadeeya ko a gefen gyalenta.

A wani bangare na zuciyarsa yana mamakin son yara irin na Fateema, ya ci ace zuwa yanzu ta yi watsi da shiga shirgin yaran Nadeeya amma ina wata rana har kuka take masa ya d'auko mata baby ta gani,a dole ya ke zuwa ya d'aukota don shi kansa babyn ta shiga ransa fiye ma da Ansar.
Sai dai k'aunar da take nunawa yaran, ba k'aramin rura wutar soyayyarta a zuciyarsa yake yi saboda ko banza yaran jininsa ne kuma duk wanda ya so yaransa dole ya k'auna ce shi bare kuma Fateemansa.

****
Yau ya kama kwana bakwai cif da zuwan baby duniya, saboda haka tun asubar fari aka fara hidima don daga ganin alama taro za a yi ba na wasa ba.

K'arfe biyun rana gidan ya cika taf da jama'a 'yan taron suna, mai jego da baby an sha kyau, Fateema ma ta yi kyau sosai abun ta kamar sabuwar amarya, sai kai da kawo take yi don ganin komai ya tafi dai_dai duk da' yan uwan Nadeeyar sun cika gidan da dangin su Farouq amma duk da haka bai sa Fateema ta zauna ba.

Wasu mata ne suka shigo su biyu yanzu, bayan sun shiga wurin maijego sun mata barka, sai aka mik'o musu baby d'aya ta ce
"babyn TubarakallAllah! Me ye sunan ta ne "??
Sai ko wace ta mik'o musu babyn ta ce" ni inama na san sunanta na zo sai kwasar sinasir na ke yi amma ban San sunan 'ya ba, barin in tambayo muku".
A haka ta rik'a bin jama'a tana ratsawa tana wucewa kuma duk wanda ta ga ni sai ta tambaya ya sunan baby ya ce "Ai bai sa ni ba".
Tun tana ganin abun kamar wasa har kuma ta fara mamaki, daga k'arshe ta dangana da wurin maijego.

"Nadeeya wai ya sunan baby kowa na tambaya sai ya ce bai sa ni ba".
Jim ta yi alamun tunani, ganin kowa ya zuba mata ido yana jiran amsa, yasa cikin takaici ta ce "ni kai na ban San sunanta ba".
Gaba d'aya d'akin suka d'au salati.
Wata tsohuwa dake gefe ta ce "garin yaya haka ta faru 'yar nan"??
Yak'e ta yi ta ce" sha'afa na yi har maigidan ya fita ban tambaya ba".
Waya ta d'auka ta kira Farouq, yana d'agawa ta ce "wai an sawa yarinyar nan suna kuwa ga jama'a nan sai tambayan sunan baby suke yi, ko ka manta ne ba ka rad'a mata suna ba"??
Ya ce" suna ai tun ranar da ta zo duniya na rad'a mata ke ce dai ba ki nemi sani ba".
"meye sunan"??
Nadeeya ta tambaya cike da Jin haushin maganarsa.
"FATEEMA" Farouq ya fad'a kaitsaye ba tare da shakka ba.
Wata irin zabura Nadeeya ta yi tare da lailayo wata ashar ta danna, wadda ta yi sanaddiyar jawo hankalin duk wanda ke d'akin.
Tuni Faruk ya kashe wayarsa don dama ya san za a yi haka, sai dai duk abinda zata yi sai dai ta yi ba zai ta6a chanza k'udirinsa ba.

Nan da nan Nadeeya ta fita daga hayyacinta sai maganganu take yi "ba zan ta6a yarda a saka mata sunan wadda na fi tsana a gaba d'aya duniyar nan ba, dole a sauya sunan nan ko da hakan zai yi sanaddiyar bari na duniya, ba zan taba lamuntar 'ya ta amsa sunan FATEEMA ba muddun ina numfashi...



Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪51

©MRS SAIF


Farouq ne ya d'aga kan sa ya kalleta cike da mamakin kalamanta don sautari idan ta yi magana sai ya ji maganarta ta kamar ta marasa ilimi, sai da ya kur6i sanyayyen lemon pineapple & yoghurt ice da Fateema ta had'a ya ce
"tunda an gaya miki ni ke ba da haihuwar ba, ko kuma ke da kika samu k'arfin ki ne ya baki".

Ta6e baki ta yi ta ce
"Ai na tabbatar da ba kai ke bayarwa ba, don da kai ke bada haihuwa da ba wannan cikin a jikina, don nasan ba k'aunata ka ke yi ba, sai dai ka bawa wacce kullum ka ke so ka ke kuma riritawa".
Ta k'arasa maganar muryarta na rawa alamar kuka na son taho mata.

"Ya ILLAH!", Ya fad'a tare da mikewa zuwa inda Nadeeya ke zaune, kujerar dake fuskantarta ya ja ya zauna sannan ya fara magana
"duk lokacin da kika furta irin wad'annan kalaman sai ki saka zuciyata cikin tararrabin anya kuwa ina adalci a takaninku"??
"Duk da na gama amincewa zuciyata da ina adalcin tsakininku don wallahi Allah ne shaidana ba ni da burin danne hakkinki duk abinda ya rataya a wuya ina k'ok'arin saukewa kamar yadda na ke wa Fateema ko da kuwa hakan zai yi sanadiyar rasa farin cikina."

Ajiyar numfashi ya yi sannan ya cigaba da cewa
"sai dai kin manta abu d'aya, domin hadisin Annabi Muhammad (S.A.W) yace
"An halicce zuciya da son mai kyautata mata."
Saboda haka ba zan iya hana zuciyata k'aunar Fateema ba, don kuwa ita ta yi k'ok'arin gina soyyatar a cikin zuciyata ginin da ba abinda zai iya rusa shi, saboda da haka ki yi k'ok'arin gina naki 6angaren ke ma, ba wai ki zauna kina haukan kishi akanta ba, da za ki yiwa kan ki fad'a da kin gyara halayenki, ki ga in akwai wanda zai kuma Jin kanmu".

Wani mugun tsaki ta ja tare da cewa
"kai kullum maganarka na gyara halayena me na ke yi wanda ba shi da kyau".
Zuba mata ido yi yana nazarin maganar ta sannan ya ce abubuwa da dama wanda in zan fara k'irgo sai mun ci dogon lokaci ba mu gama ba, yanzu ki kalli dogon tsakin da kika mun a matsayina na mijinki, don Allah ki na ganin Fateema na yi mun ko makamancin haka??
Me yasa ba za ki kwaikwayi kyawawan halayenta ba, domin ki ci ribar zama da ita".

A zafafe ta mik'e tsaye har tana bige d'an cikinta da ya fara fitowa ta ce
"ba zan ta6a kwaikwayonta ba, domin ni ban ga abin kwaikwayo a gareta ba, ka ma raina mun hankali yarinyar ta zo bayan bayana sannan don komawa baya na zo ina kwaikwayonta, ba zai ta6a yiyuwa ba, don da na kwaikwayi abinda take yi gwanda mu mutu a yanda muke".
Sannan ta juyawa wurin da Fateema ke zaune tun d'azu tana bin su da ido ta ce "ke kuma mu zuba ni da ke shege ka fasa, sai ki wani zubowa mutane ido kamar na mujiya kina kallon mutane ba za ki ce komai ba, wai ke ga ki saliha, bacin na tabbatar ba haka abun yake a zuciyarki ba, Allah kad'ai yasan mugun abun da ki ke shiryawa to ni dai na fi k'arfinki komai ki ke yi sai dai ya koma kanki.....



*******

Daga haka ba ta kuma cewa k'ala ba ta nufi part d'in ta.
Fateema da ke zaune sai juya spoon d'in hannunta take yi ta kasa k'ara kai ko loma d'aya bakinta, ba ta san sanda ta ji wani hawayena bin kuncinta ba, don takaicin Kalaman Nadeeya.
Ya salam! Farouq ya fad'a tare da janyota zuwa jikinsa, "Fatyna why are you crying, ba dai maganar Nadeeya ne yasa ki kuka ba"??
Ba ta yi magana ba illa sautin kukanta da ta k'ara.
Sosai Farouq ya shiga damuwa ganin ta k'i yin shiru.
" please stop crying babe, kukan ki ba k'aramin ta6a mun zuciya ya ke yi ba, in dai don ta maganan Nadeeya ne ki share ba wani abu ba ne idan kika yi la'akari da yanayin da take ciki".
Still ba ta yi shiru ba sai dai ta rage sautin kukan, "don Allah ki yi hak'uri ki share hawayenki Teemana ki yi mata uzuri ko don cikin dake jikinta, kin sa fa ko shi yana iya sa ta yawan masifa, ina yabonki Fateema fili da bad'ini kyawawan halayenki suna burgeni ba don ke Nadeeya ta samu a matsayin kishiya ba da ta gane kuskuranta, da ko wannan abun da take yi baza ta yi ba, ina rok'onki alfama ki cigaba da hak'uri da ita sakamakonki sai a wurin Allah don ko ni ba ni da abinda zan saka miki da shi, sai dai ba zan gushe ina nema miki ki rahmar ubangiji ba, Allah ya miki albarka ya kuma nuna min lokacin da zan d'auki babyn ki da hannuna, huh!! ranar ban san inda zan tsoma kai na ba don farin ciki ga Fatyna d'auke da gudan jinina, musamman baby girl kyakkyawa like yhu".

Fateema ba ta san lokacin da ta saki wata dariya ba tare da rufe idonta ita a dole ta ji kunya.
Sai kuwa Farouq ya d'aga cak ya sa6ata a kafad'arsa ya nufi part d'in sa yana cewa ba dai kunya ki ke ji ba bari mu je sai na sauke miki ita".
Ita kuwa sai wutsil-wutsil take da k'afa tana dariya kamar za ta fad'o ,sai dai Farouq ya rik'eta tamau a dole ta hak'ura ta ce "ni kam Qalby ka mai da ni kamar 'yar tsana d'aukana kwata-kwata baya ma wahala".
Murmushi ya yi ya ce kamar ko kin sani don idan na d'auke ji nake kamar na d'auki baby sabuwar haihuwa".

Dai_dai lokacin Nadeeya ta saki labulen parlourn ta don ganin sun wuce ba suma lura da k'urar da ta kwasota ba, zuciyarta cike da k'una ta shige cikin d'aki.....




Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪54

©Mrs Saif


Nan da nan wurin ya hargitse da hayaniyar jama'a sakamakon gaya musu da Nadeeya ta yi yanda suka yi da Farouq, daga masu cewa ba kyauta ba sai masu cewa ai ba wani abu ba ne, saboda ba sunan kishiyarta za ta duba mai asalin sunan shi ne abun duba.

Nadeeya duk ba ta ma fiskantar mai suke cewa daga k'arshe ta fito daga d'akin ta nufi part d'in Fateema sai dai wayam ba ta nan, don kuwa tun lokacin da Faty ta zo suka fita don dama ta gayawa Farouq za ta lek'a bikin wata k'awarsu da ake yi.

Haka dai taron suna ya watse ba wani armashi, sai 'yan tsirarin dangin Nadeeya da ba su tafi ba, sai jibi.

K'arfe 8:10pm Farouq ne ke driving Fateema na gefensa don tunda suka yi dare ya ce su yi zaman su idan ya gama abinda yake yi zai zo ya d'aukesu sun baro sultan road kenan Fateema ta juya tana kallon Farouq ta ce

"ni kam wai ya sunan baby ne sai fa da muka fito Faty ke tambayana, na ce ban sa ni ba, kamar mu koma mu tambayo kawai kuma sai muka share don ba kowa ya ga fitar mu ba".
"Faty da ke baya ta ce wallahi fa, sai ka ce an shafewa kowa tunanin tambayar sunan".
Murmushi Farouq ya yi ya ce sunan Ku d'aya ai, Fateema".
A tare suka zaro ido alamun mamaki, Fateema ta ce
"what a pleasant surprise, wai da gaske ka ke yi Qalby"??
"sosai kuwa da gaske na ke".
Faty ta saki wata dariya mugunta tare da cewa
"lallai ka ce Aunty Nadeeya za ta sha poison ta mutu don bak'in ciki".

Murmushi Fateema ta yi tare da cewa
"huh! Thanks sooo much babe da Namesake da ka yi mana, we really appreciate".
Faty ta kar6e "millions thanks to you bros, duk da ba mu da bakin godiya".

"my pleasure darlings, kun zarce haka a wurina, ina masifar son sunan dama can ina da ra'ayin sa ma 'ya ta Fateema".


***********


Tun kafin ya yi parking ya ke jiyo ihun yarinya kamar za ta tsaga gidan, a hanzarce ya yi parking ya fito ko kulle matar bai yi ba, Fateema ce ta tsaya kullewa, sannan ta shiga cikin gidan.

Wata k'anwar Nadeeya ce rik'e da babyn dama daga ita sai wata gwaggon su Nadeeya suka rage, yarinyar sai kuka take yi, buduwar da ke rik'e da ita sai jijigata take yi ta k'i yin shiru.
Nadeeya na gefe sai cika take tana batsewa ko kallon in da suke ba ta yi.

Yana shigowa kaitsaye part d'in Nadeeya ya yi, yana shiga ya ci Karo da su, hannu ya sa ya karbi babyn yana cewa "ina mamanta ta je take wannan kukan ha.....
Ba k'arasa rufe baki ba ya hango Nadeeyan
" wai mai ya faru yarinya na kuka irin haka kin k'yaleta"??
Shiru ta masa, sai k'anwarta ce ta ce
"tun d'azu yarinyar ke kuka tana Jin yunwa, amma ta k'i kar6anta ba irin bakin da ba a bata ba amma ta k'i bawa yarinyar abincinta". Ta k'arasa maganar tana kallon gefan da Nadeeya ke zaune.



Mum Twins 😘


▪BALLAGAZAR MACE ▪55


©MRS SAIF


Kallonta Farouq ya yi ya ce
"akan wani dalili ne ki ka yanke mata wannan hukuncin"??
A tsawace ta ce
"akan sunan da ka saka mata muddun ba ka cire mata wannan sunan ba sai dai kai ka shayar da ita, ko kuma ita wadda ka sa sunan na ta ta shayar da ita".

Ran Farouq in ya yi dubu ya 6aci cikin zafin rai ya ce "yanzu me ye na ta a ciki da za ki d'auki alhakinta har haka an ya Nadeeya ki na da hankali??
To tun muna cike da juna ki kar6i yarinyar nan ki ba ta abincinta".
Ya k'arasa maganar tare da d'ora mata yarinyar a cinyarta, zunbur ta mik'e ba don Allah ya sa Farouq ya yi zafin naman kai hannu ya tare yarinyar ba da tuni ta sha k'asa.
Rungume yarinyar ya yi tsam a k'irjinsa sannan ya d'aga hannu ya zabgawa Nadeeya wani uban mari har sau biyu gefen hagu da dama har sai da Nadeeya ta ga wasu stars sun gilma ta idanunta.
Cikin k'unan rai ya fara magana
"sai yau na tabbatar da rashin hankalinki ko na ce rashin imani to kin yi kad'an ki wulak'anta mun 'ya a gabana, kina tunanin sai da ke za ta rayu ki rubuta ki ajiye ba ke ba ita har abada zan kai wa wacce kika ce akaiwa ina da tabbacin za ta rik'eta da amana kuma cikin kulawa fiye da ke kanki da kika haifeta, a gurinki idan ban da k'azanta da munanan halaye mai zata koya, tsayuwata anan ji nake kamar amai zai taho mun idan ban da k'arni ba abinda ke tashi, ana miki kawaici ana rangonta miki saboda wasu dalilai amma ba ki san haka ba, gani ki ke kamar tsoron ki ake yi, to daga yau na shata layi duk irin rayuwar da ta kama ita zan yi da ke a cikin gidan nan, baby kuma ko ki na so ko ba kya so sai ta amsa sunan FATEEMA sai ki shirya barin duniya ko ki had'iye zuciya ki mutu don bak'in ciki".

Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice daga d'akin, kaitsaye wurin Fateema ya nufa bai rufe mata komai ba ya gaya mata duk abinda ya faru.
Fateema tuni tausayin yarinyar ya kamata har da hawayenta a ce baby kamar wannan rabonta da abinci tun bayan Azahar kai gaskiya Nadeeya ba ta da imani akan wata hujjar banza ta yiwa 'yar cikinta haka.

Kai dubansa ya yi ga babyn da wahala ta sakata baccin dole ya ce
"ina ga fateema zuwa kawai za ki yi mu je asibiti mu nemi shawarar doctors akan yanda ya kamata a kula da ita musamman ta 6angaren abinda za ta ci".
Fateema da ke rungume da little Teema ta ce
"sosai nima tunanin da na ke yi kenan".

A cikin daren nan suka nufi PREMIER kasancewar akwai wani Dr. abokin Farouq da ke aiki acan, ba su fita ba sai da ya sanar da shi a waya.
Ba su sha wahala ba suna zuwa ya had'a su da wata consultant a pediatric Dr Amisha, da yake matar akwai kirki ta yi musu bayani dalla - dalla yanda za su kula da babyn daga k'arshe ta ce su gwada ba ta madara NAN1 insha Allah za a dace ta kar6eta amma sai dai su rik'a ba ta ruwa akai-akai,suka yi mata godiya suka fito.


Nadeeya kuwa tun fitar Farouq ta durk'ushe tana wani irin kuka da na kasa tantace na me ye, ba abinda yake mata yawo a k'wak'walwa irin kalamansa, ta ji ciwon Kalamansa ba kad'an ba, sai dai ta saka a zuciyarta ba ita ba yarinyar har abada kamar yadda ya ce, gidansa ma za ta bi duk hanyar da za ta bi ta bar masa kayansa kawai don tana shakkar mamansu ne da ba abinda zai hana ta barin gidan a yau d'in nan .....


Hehehe! masu cewa Fateema ta yi yawa a buk d'in nan, ku yi hak'uri saboda I dedicated this buk to all my namesakes (FATEEMA'S) so fagen namu ne sai sorry akwai wasu ma anan gaba lol.

Asma'u (Husna), Aysha & Hafsat Birum, kun san ina son sunayenku cox akwai sunan my mum & my elder sister a ciki so duka sunayen suna da daraja a wurin, da duk wani sunan d'an musulmi mai asali ina alfahari da shi wallahi.

Sai mun had'u a happy Sallah idan Allah ya nufe mu da gani ❤👌🏻




Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/17, 5:17 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪60

©MRS SAIF


                       THREE MONTHS LATER


Har zuwa lokacin Nadeeya ba ta samu tudun dafawa ba, duk abubuwa sun cakud'e mata, ta rasa me ke mata dad'i cikin fad'in duniyar nan, yanzu har Mamanta ba ta jindad'in yadda ta ke mata, don ita ma yanzu goyon bayan Farouq take 100%.

Tana ji tana gani Farouq ya siya musu motoci masu masifar kyau ita da Fateema, amma Mama ta ce "ya siyar da tata ya aiko mata da kud'in ta ajiye har sai lokacin da ta yi hankali sannan a koma siya mata wata".

Da yake yanzu Farouq sun had'a business tsakaninsa da abokinsa Abbas suka bud'e k'aton wurin sayar da motoci, dama shi Abbas sana'arsa kenan, sai dai yanzu da suka had'a hannu da Farouq Allah ya k'ara sawa wurin albarka don a 'yan watannin da suka yi suna kasuwancin ba k'aramar riba suka samu ba.

Juyi ta kuma yi don tuna yadda Fateema ke hawa tata motar hankali kwance, da kyaututtukan da take samu wurin abokan harkar Farouq duk ta sanadin Fatyma (Basma), a' yan kwanakin nan kawai an yiwa yarinyar kyautan English gold, ya kai guda uku, kuma duk sun mata yawa sai ajiyewa Fateema ke yi,kud'i kam ba a maganarsa don kullum cikin su Fateema take,ba ya ga kayayyakin da Farouq ke siya mata, don komai ya samu yarinyar.

Runtse idonta ta yi sosai tana Jin wani ciwo na shiga cikin k'irjinta wanda ke zarcewa har zuciyarta, da yanzu 'yar ta na hannunta duk wani alkhairi ita zata samu, ba wanda zai bi ta kan Fateema, amma yanzu komai za a yi a gidan in dai ta 6angaren Farouq ne Fateema ce kan gaba kowa ma ya fi saninta, don sai a yi bak'i a gidan su zo har su tafi ba su san da wata k'urar Nadeeya ba.

Wata zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"dole na d'auki mataki akan yarinyar nan ba zai yiwu ta zo a bayan-bayana ta k'wace gida ba,duk da zuwa yanzu na gane akwai abubuwan da dama da na yi watsi da su tun farko, wanda hakan shi ya bata damar samun matsayin da take kai".
Ta k'arasa maganar tare da Jan wata doguwar k'wafa, don har yanzu ba ta wani tunanin gyara halinta, don gani take idan har ta chanza halayenta tamkar ta fad'o ne, don za a rik'a ganin kamar ta kwaikwayi Teema ne, ita kuma girman kan ta, ba zai bar ta ta yi haka ba.


*****

Fateema ce sak'ale da Basma a kafad'arta sun shirya tsaf da su, sun yi kyau har sun gaji, baby Basma ta k'ara girma abinta don yanzu tana da six months, ta daina shan madara frisogold take sha, ya kar6eta sosai  wayonta har ya wuce watannin ta, don tuni ta fara rarrafe har kama abu take ta mik'e tsaye.

Rik'e take da handbag da key d'in mota da alama fita za su yi, suna daf da fita parlourn ita da Habi don idan zata je school tare take zuwa da ita, ta rik'e mata Basma har ta gama lectures sannan su dawo gida.



Mum Twins 😘
[9/17, 5:18 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪61
©Mrs Saif


Suka ci karo da wasu 'yan mata su biyu, cikin fara'a Fateema ke musu sannu da zuwa duk da ba ta gane su ba, ko na ce bata san su ba.
Fuska suma' yan matan suka saki suna amsa gaisuwar ta.
Ganin haka yasa Fateema komawa zuwa cikin parlourn suma suka bi bayanta, sai da suka zauna sannan ta k'walawa Raleeya kira don ta kawo musu abin ta6awa.

D'aya daga cikin su ce ta fara magana " An ya kuwa ba mu yi 6atan kai ba"?
Kallonta Fateema ta yi cikin rashin fahimtar maganar ta ce" kamar ya, wani guri kuke nema ne"??
"eh, gidan wata Nadeeya nan aka kwatanta mana aka ce gidanta yake sai dai kuma yanzu na ke tunanin, kamar ba nan ba ne".
Murmushi Fateema ta yi, ta ce
"ba batan da kuka yi nan ne, Raleeya je ki kira musu Maman Ansar".
"to,"Raleeya ta fad'a tare da nufan part d'in Nadeeya.

Kallonsu Fateema ta yi ta ce "bari na tafi dama school zan je, ku gaida gida".
Da fara'a d'auke a fuskarsu suka ce "yawwa mun gode".
"ba komai". Fateema ta fad'a tare da nufar hanyar fita.
Su kuma suka bi ta da ido cike da sha'awar babyn hannunta.

"lalalalala! Su zee na ke gani yau, ko dai kun yi 6atan kai ne"???
Nadeeya ce ke fad'an haka bayan ta fito.
Harara suka watsa mata ta wasa, sannan suka ce
"bayan mu kad'ai ke neman ki, ke ba neman mu kike to ba, ko sanin tashin ku fa ba mu yi ba, sannan idan mun kira wayarki ba ma samu, sai da muka je unguwar ku ta da sannan wata makociyarki ta mana kwatancen nan".

"hhhhmm! Ku dai tashin bana dad'i ba shi yasa ba wanda ma ya sa ni sai na jiki sosai".
"to me ya faru?, mu tambayoyi ne nan fal cikin mu, lokacin da za mu shigo mun ga wasu flowers masu masifar kyau ina ga kamar 'ya da uwane su waye halan".

Nadeeya da ba ta fuskanci mai suke nufi ba ta ce
"flowers kuma, ban gane me kuke nufi ba"?

Dariya suka kwashe da ita sannan suka ce "wata fa kyakkyawa muka gani zata fita yanzun nan tare da wata kyakkyawar baby a hannunta".

"mtss, wacce ku ka gani ba kowa ba ce sai kishiyata, babyn hannunta kuma da take fashion da ita ba kowa ba ce illa 'ya ta da na haifeta da ciki na...



Mum Twins 😘
[9/17, 5:19 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪62
©Mrs Saif

Dariya suka bushe da ita, suna mata kallon ko kin fara shaye - shaye ne.
Cikin takaici Nadeeya ta kalle su ta ce
"wai wannan dariyar ta miye ko ba ku yarda da abinda na ce ba ne"??
Gyad'a kai suka yi alamar eh.
Hannunsu Nadeeya ta kama tare da fad'in "ku zo mu je part d'ina na fayyace muku duk abinda ya faru".

Ba musu suka bi ta, sai dai shigarsu part d'in ta shi ya tabbatar musu da hali na nan ba abinda ya sauya,don sai suka fi jindad'in zaman su a parlourn da suka fara zama akan na Nadeeyar, amma ba halin komawa dole su hak'ura su zauna tunda suna son Jin k'wak'waf.

****

Nadeeya ba ta rage musu komai ba dangane da abinda ya faru, duk ta kwashe ta gaya musu, cikin ta'ajibi suke jinjina kai.
Zee ta ce
"tunda dai haka ne nima na watsar da makamai na, na hak'ura da k'udurina, don na tabbatar da ba nasara saboda ko lokacin da ya ke tare da BALLAGAZAR MACE bai amincewa buk'ata ta ba, bare kuma yanzu da ya samu MACE irin Fateema".

Cikin rashin fatimar inda maganar Zee ta dosa Nadeeya ta fara magana
"ni fa kin sa ni a duhu gwanda ki fitar da ni, don ban fahimce ki ba".

Sai da zee ta d'an muskuta sannan ta ce
"yanzu a tsakanin mu ba wani 6oye-6oye zan gaya miki gaskiyar abinda ya faru, a da na so mijinki dan kuwa har tallan kaina na kai masa, sai dai sam ya nuna bana gabansa, ba irin bibiyar da ban masa ba amma ya wulak'anta ni amma duk da haka ban hak'ura ba, don yanzu haka zuwan da na yi don na d'ora in da na tsaya ne, sai dai labarin da kika ba ni yasa na zubar da makamaina na hak'ura da shi, zan kuma ba ki shawarar da ta dace, wata kila Allah sai ya ga zuciyata ya sauya mun da mafi alkhairi gare".

Wani kallo Nadeeya ke watsa mata tun fara maganarta, wanda na kasa tantace na meye.
"hmm! Ke na ke saurare fad'i shawarar ta ki ".

" gaskiya Nadeeya zan gaya miki lokaci ya yi da zaki daina wannan bak'ar k'azantar ta ki, da rashin ta idon da kike yiwa Farouq, ki gyara halinki ki daina wannan ballagazanci, ki rungumi abokiyar zamanki ku yi zaman Amana don daga ganinta za ta yi dad'in zama, ki kuma kai gwiwoyinki k'asa ki nemi afuwar mijinki, na san ba zai... Nadeeya ta katseta ta hanyar d'aga mata hannu.

"ki mun shiru zainab, wato kin gama yawon dandin ki, za ki zo ki ce za ki mun wa'azi, ai ke ba ki da darajar da zan tsaya na saurareki, bin mazan ki ya kai har wurin mijina, sai dai ki ga ni ki k'yale don kuwa Farouq ya yi k'arfinki, shi yasa sai fama kuke da hanya kun k'i auruwa.......

A zafafe zainab ta katseta "ke dabba ke ga ni kike yi har macece,?? Barin in gaya miki kin ci darajar kishiyarki ne, don na fuskanci ita cikakkiyar MACE ce, amma in dai don irin ki ne kwace miji a wurin ku ba wani abu mai wahala ba ne, ni shawara ce na ba ki idan ki ga dama ki d'auka idan ba ki ga dama ba, ki watsar ".

Daga haka ba ta kuma cewa k'ala ba, ta ja hannun k'awarta suka fice.
Kan kujera Nadeeya ta zube tana mai da numfashi, a ranta take cewar
" me yasa ne kowa ya d'ebo shararsa ya ke watsa mun ne, me na yi wa mutane ne haka".
Rashin mai ba ta amsa yasa ta fashe da wani irin kuka, wanda na kasa tantace ma'anarsa......


Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/20, 9:26 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪63
©Mrs Saif


Haka rayuwa ta cigaba da gudana a gidan Farouq yayin da Fateema da 'yar ta ke cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, don ba su da wata damuwa, idan ban da Fateema da ke fama da kasala da yawan barci a' yan kwanakin nan.
A 6angaren Nadeeya kuwa sam abun ba haka yake ba, don yanzu ta rasa natsuwarta gaba d'aya, muradin ta bai wuce ta ga 'yarta ta dawo hannunta ba, don wata irin k'aunar yarinyar take yi, wadda yanzu tana ji a zuciyarta ko da za' a kirata da Fateema za ta amince, burinta kawai a bata 'yar ta.
Sai dai tun bayan zuwan su Zee gidan take neman ta yadda za ta 6ullowa lamarin amma ta kasa samun mafita ga shi lokaci sai tafiya ya ke, tunda har an ci wata uku da zuwan su, amma har yau shiru mak'atau, wai an aiki bawa garinsu.

"Fateema! Fateema!!", Farouq ne ke tashin Fateema tare da girgiza k'afarta, don ta tashi daga nauyayyan barcin da take yi tun safe.
Da k'yar ta iya bud'e idonta ta ce "don Allah Farouq ka bar ni na yi barcin nan ka ji".

Murmushi ya sakar mata, ya ce "haba babe, ke ma kin san ba don na san kina da test 11 ba, ba abinda zai sa na tasheki ko da kuwa za ki kwana ki na barcin nan".
Ai da sauri Fateema ta diro daga kan gadon tana mutsutstsike idonta, ta ce
"ni ba na manta ba".

Murmushin dai Farouq ya kuma yi sannan ya ce " shi yasa na had'a miki breakfast, na kuma yiwa Basma wankan, don na rage miki aiki, sai ki yi sauri ki shirya, ki k'arasa shiryawa Basma sai na fara ajiyeki a school sannan na wuce office don yanzu gaskiya kin daina driving har sai mun je asibiti na ji dalilin wannan barcin, gudun kar ki je ki na driving barci ya kwasheki, ki je ki kaini ki baro ni."

Hararar wasa Fateema ta watsa masa tare da cewa "haba sai ka ce wadda tsetsefly ya ciza".
Dariya ya yi sosai tare da mik'ar da ita tsaye, "don Allah yi sauri ki shiga wanka kafin nima na makara da yawa".

A cikin mintunan da ba su gaza talatin ba ta shirya ta shiryawa Basma cikin wata doguwar riga fara k'al sai ratsin red flowers a jikin rigar, twisting ne akanta ya yi kyau sosai, don idan ka gani sai ka rantse ba gashinta ba ne attach.ne domin ya sauko sosai kamar ba gashin 'yar 9mnths ba.
Abinda ya ke k'ara bawa kowa mamaki da yarinyar saurin iya tafiyarta, don yanzu haka tafiya take sosai, kamar wadda ta bawa shekara baya....


Mum Twins 😘
[9/20, 9:26 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪64

©Mrs Saif


Fitar su ke da wuya Nadeeya da ke la6e tana kallonsu, ta yi wuf ta fito daga ma6uyarta, ta fara wani tsallen murna har da rawa, ta d'auki tsawon lokaci tana rawar har da juyi kasancewar ba kowa a gidan, don su Raleeya sun je ganin gida, Ansar kam ya zama d'an dutse don bai fiye zama a wurin Nadeeya ba.

Sai da ta yi mai isar sannan ta nufi part d'in ta, cikin sauri ta janyo wani trolley ta fara loda kaya a ciki, sai da ta zuba duk abinda ta ke buk'ata, sannan ta saka hijabinta ta yo waje jaye da trolleyn.

Fateema kuwa tunda suka fito gabanta ke fad'uwa, dama tun jiya ta yi wani mafarki mai ban tsoro wanda ta kasa gayawa kowa, sai yanzu da gabanta ya tsananta fad'uwa take gayawa Farouq.

Juyawa ya yi yana Kallonta cikin kulawa ya ce
"Fatyna ki cigaba da addu'a duk da na san kina yi, idan Allah ya yarda ba koma sai alkhairi".

"to, ni dama addu'a na bai wuce Allah ya k'ara tsare mun ita ba, don idan wani abu ya same ta ban san ya rayuwata za ta kasance ba". Ta k'arasa maganar tare da gangarowar hawaye daga idanunta.

"Ya Salam, Teema mai yasa kuka wallahi bana son kukanki ko na second, ki yi hak'uri ki yi shiru Insha Allah ba abinda zai faru da ita kin ji Fatyna". Ya k'arasa maganar cikin sigar rarrashi.

*****

Daidai lokacin su ka k'arasowa gate d'in BUK, bayan ya ajiyeta daidai faculty d'in su, ta fito ta zagaya bayan motar tana k'ok'arin fiddo Basma da ke bayan... Farouq ya ce "haba Fateema ina kuma za ki je da ita bayan kin san kwanan wurin Umma ki ke kai ta in dai za ki zo school kasancewar su Habi ba sa nan".

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"Ni kam yau da ita zan je, don bana son barin ta a wani wuri".
K'uri ya yi yana kallonta don yau ya fuskanci tana cikin wani yanayi.
Cikin tattausan lafazi ya fara magana
"Babe ki yi hak'uri, ki bar ta na kai ta gun Umma kin ga test ne kawai za ki yi, don haka kina gamawa ki yi kirana zan zo na d'auke ki sai mu je mu d'aukota na wuce da ku gida, kin ga yanzu idan kin je da ita da wane za ki ji ga ta ga test ga ki ke kanki ba ishasshiyar lafiya ba, don Allah ki yi hak'uri kin ji Fatyna".

Da k'yar dai Farouq ya shawo kanta, ta amince, amma har ta shige hall d'in tana jiyowa tana kallon Basma.


Mum Twins
[9/20, 9:26 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪65

©Mrs Saif


Nadeeya na fita ba ta zarce ko ina ba sai gidan su Farouq, tun daga gate ta bawa mai gadi ajiyar trolley'n ta, ta ce "ya ajiye mata yanzu za ta fito ba ta son ta yi ta gayansa".
Ba tare da komai a ransa ba ya kar6a ya ajiye mata, tunda yasan wace ita a gidan.

Ko da ta shiga Basma na cinyar Umma tana mata wasa, da yake har ta saba da ita 'yan kwanakin nan.
Cikin mamaki Umma ta fara magana
"yau ke ce a gidan na mu Nadeeya"?
Cikin kunya Nadeeya ta ce "eh Umma".
Don ba za ta iya tuna dogon lokacin da ta d'auka ba ta je gaishe da Umman ba.
Umma ba ta nuna mata komai ba, ko a fuskarta, don haka suka cigaba da hirarsu kamar yadda suka saba a lokutan baya.
Har agogon dake manne da bangon parlourn ya buga k'arfe d'aya dai_dai, adaidai wannan lokacin ne masallacin da ke jikin gidan suka fara kiran Azahar, saboda haka ne Umma ta mik'e ta ce
"barin je na yi sallah".
Murmushi Nadeeya ta yi cike da zumud'i ta ce
"to Umma sai kin fito kawota na rik'e miki har ki fito".

Kallonta Umma ta yi sosai sannan ta ce
"ke fa ba sallar za ki yi ba"?
Cikin Jin kunya ta ce "a'a ba yi zan ba".
Kamar Umma kar ta mik'a mata ita sai kuma ta ba ta, ta ce "Ai ni ma ba dadewa zan yi ba yanzu zan fito".

Tana shigewa d'aki Nadeeya ta bi bayanta da harara, sai da ta tabbatar ta fara Jin k'arar ruwa alamun an shiga toilet sannan ta fito a sukwane d'auke da Basma, lokacin mai gadi yana masallaci shi ma, don haka trolley'n ta kawai ta ja ta fice daga gidan.

*******

Kaitsaye adaidaita sahu ta tara straight Kano line ta nufa don shiga mota, don ta k'udurce a ranta sai ta kar6i 'yar ta shi yasa ta dad'e tana shirya wannan ranar sai yau burinta ya cika, don ta sawa ranta ba za ta nufi Dutse ba, domin Mama ba za ta goyi bayanta ba, Kazaure za ta nufa gidan wani Baffanta kasancewar ba zuwa wurin sa suke yi ba, ba wanda zai kawo tana can, sai dai ita za ta rik'a neman su a waya idan har sun amince mata ta rik'e 'yar ta sai ta dawo, idan ba su amince ba kuwa har court ta iya kai su , don yadda take Jin Basma a ranta yanzu za ta iya asarar komai domin ta.

Ba su k'arasa tasha ba, ta ga wata mota k'irar Gulf a gefen hanya ana lodi, ga dukkan alamu hanyar su za ta yi ga shi ta kusa cika, saboda haka ta sa d'an sahu ya ajiyeta anan.

Illai kuwa mutum biyun gidan gaba suke nema, nan da nan Nadeeya ta biya kud'in ta shige gaba, kafin k'yaftawar ido sun chilla kan titi kamar walk'iya haka drivern ke gudu, Nadeeya sai murna ta ke yi ta samu abinda ta ke so don bata son su ja wani dogon lokaci har a biyo sawunta.

Gudu ya ke ba na wasa ba nan da nan suka gan su a D'anbatta, sai dai me?? kafin su shiga cikin garin D'anbattar motar ta k'wacewa drivern da ya zo shan kwana saboda tsananin gudun da yake yi, haka motar ta rik'a sama da k'asa tana lolli da su, kafin daga bisani k'ofar da ke gefen su Nadeeya ta bud'e, ba ta an karaba, Basma da ke hannunta ta su6uce ta fad'a saboda k'arfin iskar da ke fizgar su, cikin tashi hankali Nadeeya ta saki wani razanannen ihu da zummar fad'awa ta d'auko Basma da k'arfi wani mutum ya sa hannu ya janyota, idan ban da salati ba abinda ake yi a cikin motar, cikin taimakon Allah motar ta tsaya da gudu Nadeeya ta fito kamar mahaukaciya tana neman Basma, hango ta yi a hannun wani mutum da gudu da k'arasa in da ya ke tsaye, sai dai sau d'aya ta kalli yarinyar ta kau da ganta tare da fashewa da wani kid'imammen kuka, gaba d'aya kayan jikin yarinyar ya koma Jan jini, don duk ga6o6in jikinta  zuba yake da jini duk da ka na ganinta ka san ba ta da rai, kusan duk mutanen da ke wurin hawaye suke yi baya ga masu kuka wiwi.....
Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'un! (ni kai na maman Twins hawaye ya hana ni typing ku biyo ni zuwa gobe don Jin yadda za ta kaya)..........



Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/21, 7:17 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪66
©Mrs Saif


Nan da nan aka kira police ba da jimawa ba aka kwashesu don zuwa asibiti domin da yawan mutanen da ke ciki sun d'an samu raunuka, Nadeeya ma ta samu tarkad'e a hannu lokacin da take k'ok'arin fita d'auko Basma, jawowar da aka mata da k'arfi ya yi sanadiyyar samun tarkad'enta.

Cikin garin Kano aka dawo da su direct AKTH aka wuce da su 6angaren A&E, Doctors da yawa suka yo kan su musamman Basma sai dai gwajin farko ya nuna musu yarinyar ba ta da rai, ban da wani azababben kuka ba abinda Nadeeya ke yi don gaba d'aya ta kid'eme, tunani take yi ina ma a mafarki ta ke ganin wannan abun da ke faruwa da tafi kowa murna a wannan duniyar,sai dai ina zuwa lokacin da likita ya tabbatar mata da mutuwar Basma ta tabbatar da ba mafarki ba ne a zahiri komai ke faruwa.


Fateema na rubuta test amma sam ta kasa nutsuwa kaf hankalinta ya kasa kwanciya, a gurguje ta gama rubuta test d'in ta yi submitting ta fito, ko tsayawa jiran Faty ba ta yi ba,hatta Farouq da ya ce ta kira shi idan ta gama ba ta bi ta kansa ba ta nemi keke napep ta hau sai gidan su Farouq.


Umma kuwa bayan ta idar da sallah ta fito zuwa parlour in da ta bar Nadeeya da Basma a zaune, sai dai wayam ba kowa, sai ta d'auka ko ta shiga toilet nan ma dai shiru, daga baya take tunanin ko da toilet ta shiga ya kamata ta ga Basma tunda ba da ita zata shiga ba.

Wasa - wasa sai da Umma ta duba ko'ina cikin gidan ba alamar su Nadeeya, ba shiri ta nufi bakin gate.
"Iro! Iro!! "
Umma ke k'wala kiran maigadi a hargitse ya fito daga cikin d'akinsa dake daf da k'ofar gate d'in gidan.
" na'am Hajiya, Allah ya sa lafiya".

"ina fa lafiya, ka ga Nadeeya ta fita d'azu"?? Umma ta fad'a tana haki kamar wadda ta yi gudu.
"A'a ban ga fitar ta ba, don akwatin da ta ba ni ajiya ma ina masallaci ta d'auki abin ta, don ko da na dawo ban ganshi ba, ina ma shirin zuwa yanzu na tambayi ko ta d'auka ne, domin na tabbatar gudun samun matsala sai ga ki kin fito".

Salati Umma ta saki tare da tafa hannu,sannan ta ce
"wato har da akwati ta zo?".
kafin Iro ya bata amsa suka ji tsayuwar d'an sahu a waje, ba d'auki wani dogon lokaci ba Fateema ta kunno kai cikin gidan.
Yanayin da Fateema ta tarar da su Umma ne ya sa gabanta mummunan fad'uwa, da k'yar ta k'arasa ciki.
Cikin nauyin baki ta ce
"Um...Umma lafiya na gan ku a tsaye anan kun yi jugum-jugum"??
Kasa magana Umma ta yi illa hannun Fateema da ta kama suka shiga ciki...
[9/21, 7:17 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪67
©Mrs Saif


Anan Umma ta juyewa Fateema duk abinda ya faru, tuni hawaye ya wanke ma Fateema fuska tana fad'in
"shi kenan na rasa Basmana, ni na san na rasata ba zan kuma ganin kyakkyawar fusk..... Sai kuma kuka ya ci k'arfinta ta kasa k'arasa maganar.
Rungumeta Umma ta yi, cikin sigar rarrashi ta fara magana "ki yi hak'uri Fateema, gudun Nadeeya ba zai rage ki da komai ba don kuwa dole ta dawo, domin duk in da za ta je na san ba zai wuce Dutse ba, don haka wannan ba wata babbar matsala ba ce, yanzu zan kira Farouq sai a san yadda za a 6ullowa lamarin".

Ba a d'auki dogon lokaci ba Farouq ya iso sakamakon kiransa da Umma ta yi zuwa lokacin ita ma Faty ta dawo nan da nan Umma ta fad'a musu abinda ke faruwa, idan Farouq ransa ya yi dubu to duk sun 6aci, ba tare da 6ata lokaci ba ya yanke shawarar bin bayan su Nadeeya.

Saboda haka Umma ta ce
"a tafi har da ita, tunda ba su San yadda za ta kaya ba idan an je can ba".
Fateema da Faty suka ce suma za su je, adole dai aka shirya tafiyar dukan su.


******

Suna daf da shiga mota wayar Farouq ta hau ringing alamar call ya shigo, hannu yasa ya d'auko wayar duk da bai san number ba haka ya d'aga.
A d'ayan 6angaren wanda ya kira shi ya ce
"don Allah da Farouq na ke magna?".
Da sauri Farouq ya ce "eh".
"okay, idan ba damuwa ka zo Aminu Kano yanzu 6angaren A&E".

Cikin rashin k'warin jiki Farouq ya ce
"me zan zo na yi Accident and Emergency kuma"??
Mutumin ya ce
"ba wani abun tashin hankali ba ne, matarka ce suka d'an samu matsala a hanya, amma ka kwantar da hankalinka ga ta ma ku yi magana".

Bai jira abinda Farouq zai ce ba ya mik'awa Nadeeya wayar, duk da muryar ta ba ta fita sosai sakamakon kukan da ta ci, amma hakan bai hana shi tambayar Basma ba tunda ya ji tata lafiyar, kukan da ta 6arke da shi yasa ya katse wayar a gurguje ya yiwa su Umma bayani, sannan suka shiga mota don zuwa asibitin, kowa zuciyarsa cunkushe da damuwa barin Fateema idan ban da kuka ba abinda take yi.

Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'un kawai suke maimaitawa sakamakon ganin gawar Basma da suka yi, gaba d'aya kuka suke yi har Umma idan ka cire Farouq da Nadeeya don ita Nadeeya ta yi kukan har idonta ya bushe sai na zuciya kuma, shi kuma Farouq hawayen ma ya kasa yi, sai tafasa da zuciyarsa ke yi tamkar za ta huda k'irjinsa ta fito, idonsa ya yi ja jajur addu'a yake yi Allah ya sa ya samu ko da d'igon hawaye ne ya fito daga idonsa ko ya samu ragin rad'ad'in da ya ke ji a zuciyarsa.

 Fateema ce ta yi kukan kura ta cafko wuyan Nadeeya ta fara magana cikin ficewar hankali
"tunda kika kasheta nima sai na kasheki, kowa ya huta sai da na gayawa Farouq kasheta za ki yi ya ce mun ba haka ba wai mafarki ne, ai ga shi nan ya faru a zahiri".

Sosai Fateema ta shak'e wuyan Nadeeya tana wasu suratai tamkar ta6a66iya kuma duk cikin gunshek'ar kuka.
Jin Nadeeya ta fara wani kakari yasa Umma da Faty suka ruga kansu dan jaye hannun Fateema daga wuyan Nadeeya, da k'yar da taimakon wasu Nurses guda biyu suka 6an6are hannun Fateema daga wuyan Nadeeya.

Wani kuka Nadeeya ta saki wanda daga Jin fitar kukan ka san yana tattare da nadama da tarin bak'in ciki, cikin kukan ta fara magana
"Umma na cuci kaina na yiwa kaina gi6in da ba zai ta6a cikewa ba a rayuta, na yi nadama na yi danasani marar misaltuwa, da kun bar Fateema ta k'arasa ni da na fi farin ciki, don na san zan huta da wannan azababben rad'ad'in da zuciyata ke mun... Don Allah Fateema ki kasheni... Ki kasheni na huta kin ji.... Sai kuma ta zube a wurin tana wani irin kuka tare da fitar wani wahallallen numfashi kad'an-kad'an.
Da sauri Nurses d'in dake gurin suka yi kanta don ganin numfashinta na k'ok'arin d'aukewa, ashe ba su sa ni ba ita ma Fateema tuni ta suma anan, don tun lokacin da aka 6an6are Nadeeya daga hannunta, ta ji wani mugun jiri na d'ibanta wanda ya hana ta aiwatar da komai illa zubewa da ta yi anan.
Cikin tashin hankali aka bawa Nadeeya gado kafin daga bisani aka bawa Fateema na ta gadon, kuka kam kala_kala ba wanda Umma da Faty ba su yi ba.

Faruk kam rasa duniyar da yake ya yi, don wani irin juyawa kan sa ke yi, wanda bai ta6a Jin irin sa ba a rayuwarsa, da k'yar ya sa hannu ya dafe bangon wurin tare da lumshe ido, tuni hawayen da yake muradin zuwansu, suka wanke masa fuska......




Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/22, 10:47 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪68
©Mrs Saif

A dole aka yi wa dangin Nadeeya waya aka sanarda su halin da ake ciki, haka ma Fateema sai waya aka yiwa su Ummy aka sanarda su Fateema ba lafiya tana kwance a asibiti, ba su d'auki dogon lokaci ba suka iso hankali a tashe, daidai wannan lokacin ne aka ba da gawar Basma don yi mata jana'iza kamar yadda addini ya tanadar.


Bayan kwana uku da mutuwar Basma aka sallamo su Fateema daga asibiti, zuwa lokacin Fateema ta dangana don likita ya tabbatar mata tana d'auke da juna biyu, saboda haka ya ba ta shawarar ta rage yawan damuwa don samun ingatacciyar lafiyarta tare da ta d'an da ke cikinta.
Kaitsaye gida Ummy ta wuce da Fateema don ta samu kulawa sosai tunda har yanzu jikin na ta da saura.

Nadeeya ma tun ranar da abun ya faru, Mamansu ta iso, ranta ba k'aramin 6aci ya yi ba, akan abinda Nadeeya ta yi, fad'a sosai ta yi mata, don ma Umma na ta ba ta baki.
Ta ce "duk da Nadeeya ce sila amma Allah ya riga ya k'addaro hakan sai ya faru, don haka babu tsimi babu dabara".
Har kawo yau da aka ba su sallama, Maman ba ta wani saki ranta ba, sai haushin Nadeeya ta ke ji.
Sam Nadeeya ba ta Jin ciwon abinda Maman take mata don ita kanta haushin kanta take ji, duk ta wani rame ta rafke lokaci guda kamar wadda ta shekara tana cuta.

******

Zaune suke sun yi jugum-jugum, kowa da abinda yake sak'awa a ransa, tun d'azu da aka ba su sallama suke jiran Farouq ya zo ya biya kud'i su san tudun dafawa.

"ni kam Farouq ina ya je har zuwa yanzu bai k'araso ba"?? Umma ce ke wannan maganar bayan ta duba lokaci a agogon wayar da ke hannunta.

Murmushi Mama ta yi ta ce
"Halimatu kenan kin san fa yau akwai sabga a gabansa tunda yau ne uku, da yawan mutane sai yau za su zo masa gaisuwa".
Umma ta ce
"haka ne amma na ga su Fateema sun tafi tun d'azu".
Kafin Mama ta ce wani abu suka jiyo sallamar Farouq daga bakin k'ofa.
Bayan ya shigo ya gaishe da su Umma, Mama ta dad'a masa gaisuwa, sannan ya kalli Umma ya ce

"Umma don Allah ki yi mun gafara ki yafe mun, don na yanke wani hukuncin da na san ba zai miki dad'i ba, amma ni hakan shi zai samar mun da nutsuwa, don duk lokacin da na ganta zan na tunawa da abinda ya faru da Basma ta sanadinta".

"Farouq wai me ka ke son ka ce ne?,ka fayyace mun manufarka don ban fahimci bayanin ka ba".
Hannu ya sa a aljihu ya ciro wata farar takarda mai d'auke da rubutu ya mik'awa Nadeeya.

Jiki na rawa ta kar6a ta bud'e ta fara karantawa abinda ke ciki kamar haka :Ni Farouq na SAKI matata Nadeeya saki d'aya kamar yadda shari'ah ta ba ni dama, idan ta samu miji ta yi aure.....
[9/22, 10:47 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪69
©Mrs Saif


Kukan da Nadeeya ta saki shi ya dawo da hankulan su Umma kanta, da sauri Umma ta kar6i takardar ta karanta, cikin razana ta yi kan Farouq idonunta cike da 6acin rai.
Da hanzari Mama ta sha gabanta tana fad'in "wai me ya faru"??.
" sakinta fa ya yi, bayan ban ba shi umurnin yin haka ba".
Murmushin takaici Mama ta saki ta ce
"akan wannan ki ke tada jijiyoyin wuya?, ki ma daina damun kan ki, domin abinda Farouq ya yi, yayi dai_dai sakamakonta kenan, dama ta dad'e tana neman sakin,
sai ta kai dubanta zuwa inda Nadeeya ke zaune ta cigaba da fad'in yau burinki ya cika sai ki d'ebi kayanki mu tafi".

Sosai Umma ta nuna damuwarta sai dai Maman Nadeeya tana ta nuna mata ba wata matsala har zuciyarta ta ga dacewar abinda Farouq ya yi don hakan da ya yi zai sa Nadeeyar ta k'ara koyon darasi akan rayuwa.,, duk da zuwa yanzu ta fahimci Nadeeyan na cikin tsananin nadama tare da datasani akan abubuwan da ta akaita, amma wannan ba zai zama hujjar da za ta nema mata afuwa ba gun Farouq, gwanda ta barta ta d'and'ani d'acin zawarci ta ji yadda ya ke, domin ko nan gaba idan ta yi wani auren ya zamar mata Izina.

Haka suka tattara yanasu - yanasu suka wuce tasha don zuwa Dutse.

Sai da Farouq ya je ya biya kud'ad'en da ake bi , sannan ya d'auki Umma a mota don maidata gida, a hanya ban da fad'a ba abinda Umma ke yi, shi dai Farouq ba shi da bakin magana, sai hak'uri ya ke ba ta don dama yasan dole za a yi haka, da k'yar ya shawo kanta ta daina mita, har ya d'an samu ta saki ranta kafin ya tafi.

Ko da ya koma gidansa sai ya ga gidan ya masa tangameme, ba ka Jin motsin kowa, nan da nan kewar mutanen gidan ta cika shi, saukowa ya yi daga saman sa ya bud'e side d'in Fateema ya shiga, yana shiga parlourn manyan toys d'in Basma tare da sauran tarkacen kayan wasanta suka yi masa welcome, wanda ko shi  ko Fateema ke siya mata, wanda da yawa daga cikin kayan sun fi k'arfin watanninta.

Teddy d'aya ya d'auka ya rungume, sai ya ke ji kamar Basman sa ya rungume tuni mutuwarta ta dawo masa sabuwa fil, bai yi aune ba ya ji hawaye na bin kumatunsa, a fili ya ce
 "ba zan iya rashin dukanku ba, Fateema ki yi hak'uri ki dawo gareni nima zan kula da ke kamar yadda Ummy za ta yi, tabbas idan na cigaba da zama ni d'aya na tabbatar da ciwon rashinku zai mun mummmunan kamu....




Mum Twins 😘
[10/16, 4:47 PM] mrm kd: [9/23, 9:53 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪70
©Mrs Saif


Kuka sosai Farouq ya ke yana sambatu shi kad'ai har sai da ya fara Jin kansa na wani mugun sarawa sannan ya rarrashi kansa ya yi shiru, ya fi k'arfin 30mnts zaune a wurin daga k'arshe ya ga zaman na shi damuwa kawai ya ke k'ara masa saboda haka ya zari key d'in motarsa ya fita da zummar zuwa gidansu Fateema.

Ko da ya isa gidan Fateema ta yi barci, sai Ummy ya tarar, bayan sun gaisa ya ke sanarda ita buk'atarsa na son a maida masa da matarsa, don yana tsananin buk'atarta a kusa da shi.
Guri Ummy ta nema ta zauna sannan ta ce
"Farouq ka yi hak'uri Fateema ta d'an k'ara warwarewa ka san har yanzu akwai damuwa a tare da ita,tana buk'atar kulawa ta musamman, zamanta anan ina kyautata zaton zai taimaka mata wurin saurin mantawa da mutuwar Basma, ka yi hak'uri har a kwana biyu sai a dawo maka da ita, tunda ga Nadeeya.

Girgiza kai ya yi sannan ya ce
"Ummy mun rabu da Nadeeya".
"Subhannallah! Ummy ta fad'a cikin mamaki.
"Ai da ba ka saketa ba, komai ai muk'addari ne,dama haka Allah ya tsara bai mai nisan kwana ba ce yarinyar".

Farouq dai bai ce komai ba illa bin ummy da ido, don shi kad'ai yasan irin halin da yake ciki a yanzu.
Shiru ita ma Ummy ta yi tana nazari domin duk wanda ya ga Farouq dole ya tausaya masa musamman yanzu da ta ji sun rabu da Nadeeya ta tabbatar shima yana da buk'atar mai rarrashinsa, amma kuma idan ta amince masa Fateema ta koma a yanda take gaskiya akwai matsala don a yarda take aiki ko na kitchen ne ba kamata ta yi ba don cikin jikinta bai yi k'wari ba, ga shi likita ya ja musu kunne sosai akan kula da yanayin motsinta don ana son ta samu hutu sosai, don Allah ne ya kiyaye ba ta samu miscarriage ba,don haka gaba d'aya kan Ummy ya kulle ta ma rasa mai za ta ce da Farouq.

Kamar ya san abinda ta ke tunani ya ce
"Ummy kar ki sawa kan ki damuwa wallahi zan kula da Fateema sosai, duk wani abu da ya kamata a yi mata zan yi kokarin yi, kuma ba zan bar ta ta yi ko wane irin aiki ba, sannan zan kira Faty ta dawo gidan da zama har zuwa lokacin da za ta warware, zan kuma yiwa Umma magana ta tuntu6i su Raleeya idan ba yanzu za su dawo ba, a nemi wasu kawai".

Ajiyar zuciya Ummy ta sauke ta ce
"shi kenan ba matsala sai ta koma, amma sai zuwa gobe tunda ka ga yanzu ta yi barci".
Murmushi Farouq ya yi ya ce
"ba komai na gode Allah ya k'ara girma".

Har ya mik'e da zummar tafiya, Ummy ta ce
"Amma Farouq kafin ta dawo ka yi k'ok'arin kwashe duk wani kaya da ya shafi Basma a wurin da za ta iya gani, za ka iya kai su ko part d'in Nadeeya ne ka kulle".

"okay, to Ummy dama nima na yi wannan tunanin, insha Allah zan yi yadda kika ce".

Yana gab da fitowa daga parlourn, Abbansu Nadeeya ya dawo tare da yayyanta guda biyu, anan ya tsaya suka gaisa tare da k'ara masa gaisuwa, sannan ya fito daga gidan...
[9/23, 9:53 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪71

Kwanaki na k'ara shud'ewa lokaci na tafiya, cikin Fateema yanzu har ya kai wata bakwai zuwa lokacin sun rubuta final exams d'in su, don haka yanzu ba su da wani lokaci da ya wuce na rainon cikinta, kullum Farouq na mak'ale da ita, idan har yana nan baya barin Fateema yin komai, da zarar za ta yi wani aiki zai kar6e ya ce shi zai yi ita ta zauna ta huta, ba yanda ta iya dole ta hak'ura ta bar masa ya yi.

Fateema ce zaune a parlourn Farouq akan rug ta mik'e k'afarta Farouq na matsa mata k'afar da ta d'an fara kumbura.
Dariya ya saki sannan ya ce
"babe an ya cikin nan ba 'yan hud'u ne a ciki ba, na ganshi wata bakwai amma kamar yau za ki haihu yayi wani k'atoto". Ya k'arasa maganar yana kwatanta girman cikin da hannunsa.

Pillow ta janyo daga kan kujera ta jefa mishi cikin sigar wasa ta ce
"wallahi ban ji bakin ka ba, duk son yarana hud'u sun mun yawa ni kam".

Dariya sosai Farouq ya yi ya ce
"ni dai in har ke za ki haifa mun ko goma ne ina so".

Dariya itama ta yi ta ce
"ni ban ma ta6a Jin d'an Adam ya haifi yara goma ba, sai ka ce Tinkiya"
Ai kuwa Farouq Me zai yi idan ban da dariya haka yai ta dariya Fateema na taya shi.

*****
DUTSE

Nadeeya ce a kitchen ke kiciniyar had'a girkin rana, don tun safe da ta tashi ba ta zauna ba ita ta yi share-sharen gidan da goge-goge, dama tun zuwanta ita Mama ta sakarwa aikin gidan, da kafin zuwanta yayyen ta ke yi wad'anda aka sako, to su yanzu Allah ya tarfawa garinsu nono don kuwa sun samu mazan aure sun d'aga sun bar Nadeeya.

Ga shi yanzu ba irin da ba ne don komai tsaftsaf suke yin sa, domin Mama ta d'auki darasi yanzu ba ta ta6a barin yaro ya zauna haka nan sasakai musamman Nadeeya da gayya take sakata ayyuka masu wahala don ta gane kuskuranta.
Adalilin k'azantar da suka tafka yasa, sai da suka saida gidan su, suka siye wani a wata anguwar daban, saboda ba k'aramin tambari mutanen unguwar suka musu ba, takai ko zuwa neman auren 'yan gidan ba a yi, saboda tsegumin da ' yan unguwar ke kaiwa duk wanda ya fito neman aurensu, daga k'arshe suka yanke shawarar tashi daga unguwar.

"Mama don Allah khadija ta zo ta k'arasa soya funkasun nan, bayana har ya k'age ga shi ina son na je na yi wanka don duk na yi gumi". Nadeeya ce ke maganar daga cikin kitchen.

"wai sau nawa zan gaya miki sai kin gama aikin nan tsaf kin wanke kwanikan da aka yi amfani da su kin share kitchen d'in kin goge sannan ki yi maganar fitowa, gwanda ma ki yi sauri kafin lokacin zuwa makarantarki ya yi".

Sai da Nadeeya ta gama aikin nan tsaf ta yi shirin zuwa makaranta, da yake tana zuwa makarantar islamiyya mai suna Mar'atussaleh, ba abinda ba koyarwa ta fuskar addini sannan ana koyawa mata duk wasu sirrika na mallakar miji a sauk'ak'e ba boka ba Malam.

Sai a sannan Nadeeya ta fuskanci ta yi babban kuskure a baya da take tunanin shan maganin mata ne kawai zai sa miji ya so ka, sai yanzu ta gane ashe sam abun ba haka ba ne, shi yasa ta k'udire a ranta duk mijin da ta aura nan gaba za ta zame masa salihar MACE mai biyyya ga miji, ta kuma bi duk wasu matakai da ta koya na siye zuciyarsa miji.

Tunda ta jefa k'afarta cikin gidan ta ji mayataccen k'amshin turarensa, ko kallon gefen da yake ba ta yi ba, ta yi hanyar shiga d'akin su.
Shi ko sai d'ashe baki ya ke yi a dole ya ga masoyiyarsa.

"Nadeeya! Nadeeya!"Mama ke k'wala mata kira lokacin da ta hango shigewarta.
[9/23, 9:53 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪72
©MRS SAIF


Dawowa ta yi ta tsaya ba tare da ta juya ba
Ta ce "ga ni mama".

"au yanzu wulak'ancin na ki ya kai ki na ganin mutum ki share shi ki wuce".
"ni fa Mama ban gan shi ba". Nadeeya ta fad'a tare da d'an turo baki.

"to barin in gaya miki ki shiga hankalinki, idan ba haka ba zan mugun sa6a ki, a wannan zamanin 'yan mata ma ya suka cika bare ke bazawara, don kin samu mashinshini shine har kike masa wulak'anci, to ahir na san hankalinki duk yana wurin tsohon mijinki, dama hak'ura kika yi da shi don na tabbatar zuwa yanzu Farouq ya manta da wata halitta ki, yana can da matarsa hankalinsa kwance, ko Ansar watansa nawa bai zo ya gan shi ba, ki na gani sai dai kakarsa ta zo duba shi, amma ni ban ga laifinsa ba, don duk ke ki ka jawo, don bahaushe ya ce na ji dad'i shine gari ba na saba ba".

Tunda Mama ta sako zancen Farouq Nadeeya ta fara share hawaye, don yanzu kuka akan Farouq ya zame mata jiki, ba ta da wani buri a duk duniyar nan da ya wuce ta kuma auren Farouq a karo na biyu, sai dai ita kanta ta san ya mata nisa, nisan da ba za iya tarar da shi ba.

Mama ce ta katse mata tunani ta hanyar fad'in
"yanzu haka maganar sa rana ya zo yi, kuma ni na ba shi damar gobe ya je gun baffa babba su yi magana yasso daga baya ya turo wakilansa kawai a d'aura aure ba wani abu da za a tsaya jira".
Ai kuwa tuni kukan Nadeeya ya tsananta fiye da d'azu.

"eh lallai! za ki wuce ki je ki same shi ko kuwa"?
"to " kawai ta ce, ta shiga d'akin su jaka kawai ta ajiye ta fito fuskarta duk ta kumbura alamar ta yi kuka, ta nufi inda bak'on na ta ke zaune.

Ko da ta gama tad'in ba ta kwanta ba sai da ta wanke tulin kayan wankin Mama sannan ta kwanta cike da gajiya da tsantsar tunanin abinda ke shirin faruwa da ita.

Yanzu ba ta da wani buri da ya wuce ta ganta gidan Farouq a matsayin matarsa, yanda ta ke Jin kaunar Farouq a yanzu ko rabinta ba ta ji ba lokacin aurensu, tana matuk'ar son ta koma auren Farouq a karo na biyu ko don ta gyara kurakuran da ta yi, sai dai ina har yanzu zuciyarta ta kasa hasko mata mafita, dole tana ji tana gani za ta auri mutum da ba son sa ko d'igo a zuciyarta.

Wani hawaye ta ji yana bin fuskarta wanda ba ta damu da ta goge ba, Ansar da ke gefenta a kwance ta rungume tana Jin tsananin k'aunar mahaifinsa na ratsa ko ina na sassan jikinta.
Ta d'auki tsawon lokaci a haka, kafin daga bisani ta kwantar da shi, ta d'auro alwala ta tayar da Nafila, ta dad'e tana jera nafifili sannan ta yi sallama ta d'aga hannayenta sama cikin kuka ta fara addu'a.

"Ya Allah, ya mad'aukakin Sarki, ya mai amsa buk'atun bayinsa ya Allah ka fini kusa da jijiyar dake wuyana ya Allah ka san na yi nadamar abun da na aikata ya Allah ka kawo mun mafita mafi alkhairi, idan har komawa Farouq alkhairi ne ya Allah ka tabbatar mun, idan ba alkhairi ba ne ka sauya mun da mafi alkhairi".
Ta shafa addu'ar tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi...


Mum Twins
[10/16, 5:08 PM] mrm kd: [9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪73
©Mrs Saif

Da sauri - sauri ya ke shirin kasancewar ya d'an makara zuwa office, Fateema da ke zaune a gefen gadon d'akin tana kallonsa, sai wani ciccin magani take, yanda ta wani had'e fuska abun har ya so ya bawa Farouq dariya sai dai ya daure don kar ya tsokano wa kansa rigima don yasan k'iris take jira.

Sai da ya gama shirin tsaf, ya juya da kallonsa gareta ya ce
"Fatyna zan tafi, sai na dawo"?
K'ara tsuke fuska ta yi ta ce
"uhmm".
D'an zaro ido waje Farouq ya yi cikin mamaki ya ce
"yau ko daddad'ar addu'ar nan ba za a mun ba, bare kuma rakiya"??
Gyd'a kai ta yi alamar eh.
Murmushi Farouq ya yi ya ce "lallai yau sarautar ta motsa, tunda haka ne na fasa fitar nima," ya k'arashe maganar tare da ajiye briefcase d'in hannunsa ya fad'a kan gadon ya yi lamo kamar wanda zai yi barci.

Shirun da ta ji ya yi yawa ne yasa ta kai hannu ta juyowa da fuskarsa, ba barci yake yi ba amma idonsa a rufe yake, cikin muryar shagwa6a ta ce
"don Allah ni ka tashi ka tafi aikinka".

 Bud'e idonsa ya yi ya d'ora akan fuskarta ya ce
"ba zan je ba har sai kin gaya mun dalilin wannan fushin".
"Ai ka fi ni sanin dalilin, wata nawa ina binka da magana d'aya amma ka k'i saurarata".

Ajiyar numfashi ya yi sannan ya ce
"Fateema ki share zancen na dawo da Nadeeya, kimanta da maganar don ba ya cikin tsarina gaskiya, haka kurum muna zaman zaman mu ki jaji6o mana ita ta zo ta wargaza mana jindad'in rayuwa, ba zan iya ba gaskiya".

"Haba Farouq ka yi hak'uri ka yafe mata tunda ta yi nadama, ta rok'i afuwa ba sai a mata ba, Allah ma fa muna masa laifi kuma ya yafe mana, yawan nacin kirana da take yi ba dad'i sai ta ga kamar nima bana son ta dawo shi yasa na k'i mata kokarin shawo kan ka, tun tana kiranka ka na mata wulak'anci har ta hak'ura ta dawo kaina, don tabbacin da ta da shi na zan taimaka mata".

"ke ma yanzu idan ta kiraki ki ce kar ta kuma kiranki, don na k'i amincewa faqat, kin ga sai kuma ta nemi wani tunda aikinta kenan bibiyar dangina".

"gaskiya ni kam ba zan iya cewa kar ta kuma kirana ba, ai sai ta ga kamar na mata wulakanci".
"Okay, amma don Allah ni ko ta k'ara kiranki kar ki kuma gaya mun don bana son maganarta kwata_kwata don tuni na rufe shafinta a cikin rayuwata".

"Amma ai..... Farouq ya saurin katseta ta hanyar d'ora hannunsa akan lips d'in ta ya ce
"shhhhhhh! Babe yaushe ki ka fara musu ne? Bana son maganar nan abarta haka."
"alright, yanzu tashi mu je na rakaka domin lokaci sai tafiya ya ke".
Murmushi ya yi ya ce
"ko kefa, dama na san maganar duk ta k'arfin hali ce kike don dai Farouq na Fateema ne ita kad'ai".
Dariya Teema ta yi sosai don ko Farouq ya harbo jirginta, a ranta ta ce
"dama wa zai so kishiya sai dai idan ta zame ma dole ba yanda za ka yi".....



Mum Twins
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪74
©Mrs Saif

Three weeks later
******

Zuwa lokacin Nadeeya ta zama abin tausayi, don duk ta fige ta lalace, don ciwo take yi ba na wasa ba, kuma ba abinda ya yi sanadinsa irin damuwa da tunani, don bikinta da Alh Sani saura sati biyu kacal, tun Mama na shareta har ta fara tausayinta, kun san tsakanin d'a da mahaifi, sai dai ta san ciwon Nadeeyar ba na komai ba ne illa na son Farouq, kuma ga shi ta yi rantsuwa ba za ta kuma shiga maganar aurenta da Farouq ba.
Wasa - wasa ciwo har sai da ya kai ta da kwanciya asibiti,a lokacin gaba d'aya ta saduda da rayuwar kira kawai take a kira mata Farouq ta nemi afuwarsa kafin ta mutu.
Sosai Mama ta shiga damuwa ba shiri ta kira Umma a waya ta sanarda ita duk halin da ake ciki.

*******

Don haka ne yau tunda safe Umma ta kira Farouq ta ce "idan ya tashi daga aiki ya je tana nemansa".

Bayan sun gaisa ne Umma ta fara magana kamar haka
"Farouq ba komai yasa na kira ka ba sai don maganar Nadeeya, bana son takura maka a karo na biyu, shi yasa ka ga duk tsawon lokacin nan ban yi ma maganar ka dawo da ita ba, amma jiya labarin da na ji akanta abin ya girgiza ni matuk'ar gaske".

Anan ta kwashe labarin komai ta gaya masa, sannan ta cigaba da cewa
"don haka na ke nema mata alfarma ka yi hak'uri ka dawo da ita, ka manta da duk abinda ya faru a baya, insha Allah dawowarta zai zama alkhairi gare mu baki d'aya".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in
"Umma ba na tunanin akwai wanda za ki nemawa alfarma a wurina na kasa yi miki matuk'ar abin bai fi k'arfina ba, don haka na amince da auren Nadeeya a karo na biyu Allah ya sa hakan ya zama alkhairi."
"ameen "
Umma to fad'a cikin jindad'i, sannan ta shafa kan sa ta ce" Allah ya maka albarka Omar Farouq, yasa ka samu yara masu maka biyayyya fiye da yanda ka ke mun".

"ameen, ameen Umma " ya fad'a tare da mik'ewa tsaye don tafiya.

Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka sa tafiya dutse, da Faruk ya so ya waske ya k'i zuwa Umma ta ce dole ya je, ba yanda ya iya dole ya ajiye ayyukansa ya tafi.

Tabbas shi ma ya ga canjin da ake cewa Nadeeya ta yi, don ta koma wata saliha ga nutsuwa har wani kunyarsa ta ke ji abun har mamaki ya bawa Farouq.

Matsala d'aya suka samu ta Alh Sani don ya tsaya kai da fata ba zai janyewa Farouq ba, tunda an riga an sa musu rana, da k'yar da sud'in goshi ya amince ya jaye.

Daga k'arshe aka yanke shawarar sati mai zuwa za a d'aura aure a yi bikin da ya sawwak'a amarya ta tare a gidan angonta.
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪75
©Mrs Saif

Haka aka yi kuwa sati na zagayowa aka d'aura aure aka sha biki amarya ta tare, daren farkon su Farouq ya k'ara tabbatar da chanzarwa Nadeeya, don sam ko alamar  warin da take yi ada bai ji ba,,idan ban da k'amshi dake tashi daga kowacce ga6a ta jikinta ba abinda ya ke ji, dama gashi ta samu ingattatun magungunan mata ta yi amfani da su tsaf ta d'inke abinta kamar sabuwar budurwa.
Ai kam Farouq ya sha mamaki a daren ranar sai yake ji kamar wata Nadeeyar ce ta daban aka kawo masa ba wadda ya sani ada ba.

Washe gari ko da ya tashi sai ya tsinci kan sa cikin annushuwa, wacce ko a daren farkon auren su na fari bai yi ba, har Fateema sai da ta fuskanci haka.

Nan da nan ta ji wani kishin Farouq na nuk'urk'usarta,kun san an ce
"kishi kumallon mata".
Sai dai da ta yi tunanin duk abinda Nadeeya za ta yi daga baya ne, don ita ta riga ta wuce wannan shafin, ta riga ta wa Nadeeya nisa a zuciyar Farouq, nisan da duk gudunta ba za ta iya tarar da ita ba, sannan ita ma ai ba zama za ta yi ba, za ta d'ora ne a inda ta tsaya don ta riga ta gama sa nin Farouq cike da bai, saboda da haka hanyoyin mallakarsa a tafin hannunta suke, don haka me zai sa ta rik'a kishi ma da Nadeeya da sai yanzu ne take gane waye Farouq, da wannan tunanin ta watsar da duk wani abu da shaid'an ke bijiro mata da shi a zuciyarta.

*******

Zaman su suke yi lafiya Lau cike da fahimtar juna, domin tuni zaman na su ya sauya salo idan ka gansu kamar ba kishiyoyi ba, sai ka rantse da Allah ya da k'anwa ne, ko gidan ka shigo ba za ka ta6a gane mai girki ba don tare suke shiga kitchen, musamman yanzu da Fateema ta yi nauyi haihuwa ko yau ko gobe, Nadeeya ce ta kar6i girkin gaba d'aya ta ke yi, sai dai fateema ba ta son zaman kawai ba ta komai, don haka lokaci zuwa lokaci ta kan shiga kitchen d'in ta taya Nadeeya aiki koda ba mai wahala ba, Nadeeya ta yi ta mata mitar ta je ta zauna ta huta amma ta k'i, a dole take k'yalleta.

Farouq ne ya dawo daga aiki tunda parlour ya ke jiyo tashin hirarsu a hankali daga kitchen murmushi ya yi ya nufi kitchen d'in, dukkan suka jiyo suna masa sannu da zuwa, cikin fara'a ya amsa musu.
Fateema da ke zaune tana tsige d'ayan zogole a wani d'an k'aramin bowl ta yi k'ok'arin mik'ewa don kar6an ledojin hannunsa da sauri ya zaunar da ita yana fad'in "oh! Fatina ki zauna abin ki zan ajiye da kaina, ke kanki kamata ya yi na rik'a d'aukan ki duk inda za ki je,Allah ina tausaya miki cikin har ya fi ki girma". Ya k'arasa maganar tare da kai hannunsa kan cikin.

Dariya Nadeeya ta yi ta ce
"wallahi fa kamar ba na farin ba". Murmushi Farouq ya sakar mata ya ce
"Amryata wai me kuke dafa mana ne, na ji gidan ya d'umame da k'amshi".

"mai cikin gidan nan ce yau ke son dambu, ka ga kuwa dole na mik'e na dafa shi".
"wow! Gaskiya kin kyauta Amryata kin san nima na dad'e ban ci dambu ba, musamman dambun amare akwai dad'i". Ya k'arasa maganar yana kannewa Nadeeya ido d'aya."

Shiru ta masa ba ta amsa shi ba, ganin haka yasa Fateema kwashewa da dariya don ta san abinda yasa Nadeeya yi masa shiru.
"Maman Ansar gwanda fa ki hak'ura da amaryar nan don kin san yanzu ni ce uwargida sarautar mata sai sorry". Fateema ta k'arasa maganar tare da sakin wata dariyar mugunta.
Shi ma Faruk dariyar ya ke mata, don haka Nadeeya ta ajiye ludayin da ke hannunta ta juyo garesu ta ce
"Abban Ansar da kai da Teema ina tunanin sai na kai ku court alk'ali ya mana shari'a da ku sannan kuma ba ni certificate da zai tabbatar da ni ce Uwargida a gidan nan, ku kuma a saka muku hukuncin mai tsauri ga duk wanda ya k'ara kirana da Amarya".

Farouq da Fateema me za su yi idan ban da dariya, Teema dariya har da hawaye, tana cikin dariyar ne ta ji mararta ta wani murd'a, tuni d'an da ke cikinta ta ji yana mata wani mugun juyi, dama tunda ta tashi take Jin ciwon mara kad'an-kad'an sai dai na yanzu yayi tsamari, ba shiri ta cakumo rigar Farouq tare da ruk'unk'ume shi tana fad'in "Farouq bayan marata, washhh"!!!

Cikin tashin hankali Farouq ya d'agata ya sunkuceta sai cikin mota, Nadeeya kanta ta shiga rud'ani irin yadda ta ga fateema ta fita hayyacinta lokaci d'aya.
Cooker gas kawai ta kashe ta fito daga kitchen d'in da gudu ta yi part d'in ta sako hijabi don bin su.
Sai dai tana fitowa mai gadi na rufe gate alamar har sun fice.

Cikin gidan ta koma ta shiga part d'in Fateema ta had'a mata duk kayan da ake buk'ata kama daga na ta har na baby kasancewar komai an siya, don dai Farouq ya rud'e ne shi yasa ba su tsaya d'auka ba......
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪76

Kaitsaye labour room aka wuce da Teema, ko da aka dubata she's almost 8cm ashe a tsattsaye take labour, Farouq na tsaye yana safa da marwa wata Midwife ta fito ta ce
"kai ne ka kawo wadda aka shiga da ita yanzu nan".
Cikin zak'uwa Farouq ya ce
"eh".
Insha Allah muna sa ran haihuwarta nan da 20mnts, don haka sai ka kawo kayanta a shiga da shi zan turo a kar6a yanzu".
"to " kawai Farouq ya ce don shi sai yanzu ma ya tuna da zancen kaya. Cikin sauri ya koma inda yayi parking mota ya figa sai gida.
Yana isa Nadeeya ta gama shiri har kayan ta fito da shi zuwa main parlourn su, ta zuba ruwan zafi a teaflask, da kayan tea duk ta had'a komai na buk'ata.

Ai kuwa Farouq ya ji dad'i kayan kawai aka sa a booth, Nadeeya ta bawa su Raleeya Ansar ta ce "su lura da gida kafin ta dawo".

Fifteen minutes later
*****
Fateema ta haifo santaleliyar yarinyarta, sai dai abun mamakin Jin da ta yi midwives da ke gurin na cewa ta yi nishi ga wani kan baby nan tafe.
Cikin kid'ama da rud'ewa baki na rawa ta ce "wai... wai me... kuke nufi da... sai dai wani azababben ciwo ne ya hana ta k'arasa maganar, a dole ta saki wani wahalallan nishi da ya yi sanadin zuwan wata babyn.

Gaba d'aya midwives d'in suka hau ihun murna, wasu daga cikin su sai addu'a suke Allah ya ba su yara kamar babies d'in nan, nan da nan aka gyara yaran, suka fes identical Twins ba k'arya kyawawa kuma ajin farko.

1st born d'in aka fara mik'owa Fateema, saboda da kid'emewa sai da fatyma ta silmiyo daga kan gadon da take kwance, idonta ta k'ara maidawa kan yarinyar tabbbas ba idonta ke mata gizo ba, fuskar Basma ce a jikin babyn sak tamkar Basma na jaririya, tuni hawayen farin ciki da jindad'i ya zubo a fuskar Fateema, kwantar da babyn ta yi a gefe sannan ta kai goshinta k'asa tana mai yin 'sujudu-shshukur' ga Sarki Allah mai yanda yaso a lokacin da yaso.

Ba ta k'ara girmama al'amarin ba sai da aka kawo mata 2nd born, ba bambanci a tsakaninsu kamar kwabo da kwabo Allah ya so an musu alama da komai k'wak'war mutum ba zai gane wadda aka riga haihuwa a cikin su ba.
Wani murmushi ne ya su6ucewa Fateema don tuna. yadda Farouq zai ji yau ga Basman sa har biyu Allah ya dawo masa da ita.
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪77
©Mrs Saif

Suna tsaye shi da Nadeeya don ko zama sun kasa sai gani suka yi an fito da babies biyu an nufo inda suke, kan Nurses d'in su k'araso har Farouq ya k'arasa gun su, da sauri ya ce "Allah dai yasa ta haihu"
Da murmushi d'auke a fuskarsu suka ce
"ta haihu lafiya k'alau ga ma yaranka".
Cikin zaro ido waje Farouq ya ce "yarana??".
"sosai kuwa, don ko matarka ta haifi Twins duka mata, suka k'arasa maganar tare da mik'a masa babies d'in lokaci d'aya.
Diriricewa Farouq ya yi ya kalli wannan ya kalli waccan ya ma rasa wa zai kar6a a ciki, ganin haka Nadeeya ta mik'a hannu ta kar6i d'aya cike da tsantsar farin ciki, sai dai fuskar yarinyar da ta gani sosai ya yi masifar bata al'ajabi don sak Basma ba maraba da lokacin da take baby.
Tuni son yarinyar ya tsarga zuciyar Nadeeya, ba ta yi aune ba ta ji hawaye na bin kuncinta don tunawa da Basman ta da ta yi.

Wohoho! Farouq kam murna kusan zauta shi ta yi, kar6ar babies d'in ya yi ya had'a su ya rungume tsam a k'irjinsa, ba abinda ya ke yi da ya wuce Tasbihi, gaba d'aya kud'in jikinsa sai da ya rabawa mutanen da ke zaune tsakanin labour room da postnatal.

Wad'anda suka masa albishir da haihuwar kam cewa ya yi "su ba shi account number d'in su zuwa gobe da yardar Allah za su ji alert, haka suka yi godiya cike da murna suka bar wurin.

Nan da nan Farouq ya fara sanarda 'yan uwa a waya na ko wane bangare kan ka ce me an cika asibitin mak'il domin duk wanda ya ji sai ya cika da mamaki, uwa uba ya zo ya ga babies da idonsa, tsantsar k'auna kam da kulawa ba wadda Fateema ba ta gani ba daga kan Farouq har danginsa, ba a maganar danginta, hatta 'yan uwan Nadeeya sun mata kara sosai.

RANAR SUNA
*****
Tsayawa fad'in shagalin da aka kwasa ranar suna 6ata lokaci ne, yara sun ci sunan Fateema Zahra da Fateema Zuhra.
Tun a daren ranar da suka dawo daga asibiti Farouq ya ke gayawa Fateema sunan da ya sakawa yaran.
Cikin mamaki ta ce
"haba Qalby sunan bai yi yawa ba dukan su Fateema".

Murmushi ya yi tare da cewa
"l like the name, you're more than all the sweet names in the world."
Murmushin Teema ta mai da masa sannn ta ce
Thanks alots babe really appreciate".
Sai da ya yi pecking babies d'in a goshi sannan ya yi wa Fateema sai da safe ya ja musu k'ofar ya fice.

*****
Haka rayuwar su ta cigaba da garawa cikin kwanciyar hankali ba wani tashin hankali tsakaninsu kan su a had'e yake tsaf, kun san Zuhra ma a hannun Nadeeya ta ke, idan ka ganta a gun Fateema to tabbata ta je cin abinci ne.
Shi yasa Farouq yanzu ba shi da wata damuwa kullum cikin nishad'i ya ke, shima yana kokarin kyautata musu iya kar k'arfinsa don komai ya samu darlings d'in sa, ba ya nuna wariya tsakanin su, yana kokarin yin adalci a duka 6angarorin biyu, sai dai so d'aya ne tak, yasan Fateensa ya ke yiwa shi, sai dai zuwa yanzu Nadeeya ta zama wani babban jigo daga cikin rayuwarsa, wanda rashinsa ba k'aramin barazana ne ga rayuwarsu ba.

One Year later
*****
Yau Twins suke cika shekara d'aya a duniya, don haka ne Nadeeya ta shirya musu k'ayataccen birthday party na zallar yara sai iyayensu, anan dai cikin harabar gidansu za a yi, an yiwa wurin decoration mai kyau an gyara gurin sosai, sai k'aton cake da aka ajiye a tsakiyar wurin da aka k'awata shi fiye da ko ina.

******
4pm wurin ya cika mak'il da jama'a kasancewar ranar Sunday kusan duk wad'anda aka gayyata sun samu zuwa, Faty amarya ma (kasancewar an sa ranar bikinta nan da 3mnths za a yi ita da masoyinta Naseer) ta zo tun safe da ita ake hudimar.

Huuuuuuuuh! Twins na hango tare da Mamansu suna tahowa, yaran kyawawa na bugawa a jarida sun sha ado cikin wasu dakakkun english wears riga da skirt pink colour da ratsin silver color a jiki yaran sun yi matuk'ar kyau ba kad'an ba, haka Fateema da Nadeeya abun dai gwanin sha'awa, Farouq ma ba a bar shi a baya ya cake cikin wani yadi tissue mai matuk'ar kyau da tsada, tamkar wani sabon ango, duk wanda ka gani a wurin yana cikin farin ciki.

Gifts kam Twin sun samu ba kad'an ba, don kyaututtaka na ban mamaki abokan Farouq suka ba su, duk wanda ka gani a wurin da irin kyautar da ya ba su....
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪78
©Mrs Saif

Daga k'arshe Farouq ya rik'e hannun Zahra Fateema ta rik'e na Zuhra suka d'ora hannayensu akan wuk'ar yanka cake d'in suka yanka, nan da nan wurin ya gaure da tafi tare da wak'ar happy birthday..... Farouq ne ya fara d'iba ya kaiwa Fateema a baki har ta bud'e bakin zai sa mata karaf idonta ya had'u da na Nadeeya da sauri ta kai hannu ta janyota, hannu suka sa a tare suka d'ibi cake d'in suka kaiwa Farouq a baki, ba yanda ya iya dole ya bud'e bakin duk suka saka masa da k'yar ya iya had'iyewa saboda yanda ya cika masa baki.
Yanda ya ke tauna cake d'in ya bawa kowa dariya a gurin, ai kuwa mutane mai za su yi in ba dariya ba, sai da kowa ya yi mai isar shi, sannan Abbas ya matso daf da su (da yake ya zo shi da matarsa da yaransa biyu) ya bawa Farouq hannu ya ce "ina yiwa Twins fatan rayuwa mai albarka tare da tsawon kwana mai amfani, kai kuma Allah ya k'ara had'a maka kan zuri'arka tare da farin ciki mai d'orewa".
"ameeeeeeen"gaba d'aya wurin aka amsa da shi.
Sannan Abbas ya k'ara damk'e hannu Farouq ya fara magana cikin zolaya,
"ka ga yayan Fateema mijin Fateema kuma Baba ga Fateema's... Bai kai ga k'arasa abinda zai ce ba ya hango Nadeeya sai ya cigaba da cewa "kuma miji ga  Uwargida Nadeeya amma fa mai retire.....".Gaba d'aya wurin aka hau dariya tare da tafi raf! raf!! raf!!.


TAMMAT BIHAMDULILLAH
Godiya ta tabbata ga Allah da ya ba ni ikon fara littafin nan lafiya na kuma gama lafiya, Ya Allah kurakuran da na yi a ciki a bisa rashin sa ni ko kuma ajizanci na d'an Adam ya Allah ka yafe mun.


I dedicated this buk to all my namesakes (FATEEMA'S)

Bazan ta6a mantawa da ke ba matuk'ar numfashina yana tare da gangar jikina, beloved daughter kuma namesake
Fateema Basma Saifullah Allah ya kai rahma k'abarinki tare da 'yan uwa musulmi, Allah ya sa ki zama mai ceton iyayenki.

Kin wuce k'awa kin zarce aminiya sai dai na kiraki da
rabin jiki Fateema Farouq Azzarah, Allah ya bar k'auna

Namcy dia Teema Cool, you're one of the best

Ku na Raina.....
My in-law Lubabatu Sani Maitafsir
My namcy pherty
Ma Mumcy Om Samha

Special Thanks to.....
Mrs Adams (namesake) k'awar Nadeeya lol...
Mrs Umar (namesake)
Asma'u Sanusi (Ummy)
Aunty jidda Musa (maman Twins)
Miss Hafsy
Ummul Fadeela
Queen mimi
Jam33ler
Nabeela

Da duk wanda ban fad'a duk Kuna raina ku yi hak'uri ciwon kai ke damu na wallahi.
Dole na jinjina muku NWA Family Allah ya sa mu fi haka 👏🏻

My Fanx sai dai na ce da ku Ana'uhubbuku
kathir-kathir

Fateema A Imam (Mrs Saif)
               Kuma
Maman Twins ke muku fatan alkhairi.

Sai mun had'u @ma next novel...............

10 comments:

  1. to idan mutum ya yi copy amma ya bar komai, ma'ana sunan marubuciyar da dukan bayanan ta fa?

    ReplyDelete
  2. Na yi imani da wanda ya mallaki 100% na zuciyarka ya cancanci yaƙin. Haka ne, ina alfahari saboda ban taɓa bin shawara mai kyau daga iyayena ba lokacin da nake son yin aure. Akwai yakin tsakanin iyalinmu biyu sannan mijina ya kasance jaririn uwarsa, 'yan uwansa sunyi amfani da shi da yawa wanda ya yanke hukunci ba tare da tuntube su ba. Abinda ya mamaye ni shine lokacin da dan shekaru 36 ya nemi iyayensa da wasu dangi su yarda kafin su gana da kowa da kowa, mafi munin abin da ya faru lokacin da aka umurce shi ya kawo ni zuwa ƙasarsu a Rampart, New Orleans, yana da haɗari don karɓar wannan gayyatar.Gamar tsakanin iyalanmu ya fara lokacin da ya karshe (wannan kimanin shekaru 4 da suka wuce), iyalinsa sun ba da wasu ka'idoji idan yana da matata (muna zama tare da su), na yi fushi lokacin da miji yarda da farin ciki da yanayin su (don haka mahaukaci). Iyalanmu sun yi tawaye kuma sun bukaci ya kamata in rabu da shi nan da nan.Na yanke shawarar ba shi harbin karshe kamar mutum wanda ya riga ya dauki 100% na zuciyata, na dauki haɗari na tafiya ta ruhaniya tare da su ta hanyar tuntuɓar Doctor Sharaja ta sharajasid @ Gmail.com, Ban sani ba amma mahaifin ruhaniya ya rigaya ya san zan shawarce shi. Da farko dai ya gaya mani hatsarin da nake ciki da kuma yadda miji ya zama bautar tun lokacin da aka haife ni, yadda suke ci gaba da kwakwalwa ta wanke shi don yin abin da suke so. Kamar yadda abin da mutum yake gani a hankali kawai, na gane cewa babu wanda ya ga abin da na gani a cikin mijina kuma wancan ne dalilin da ya sa na yi amfani da taimako na SHARAJA SHIRYA don cire shi daga cikin wahala. Idanunsa inda aka bude ta SHARAJA SID a karo na farko, iyalinsa sun ƙaunace ni kuma sun ba da duk bukatunmu, iyalanmu sun san zaman lafiya tun bayan ƙaunar da aka yi. Yana da shekaru 2 bayan ƙauna da mijina ya ci gaba da inganta kowace rana ba tare da tsangwama daga iyalinsa ba. Na jira tsayi sosai don raba wannan yanki mai ban mamaki. Na gode da lokacinka da kuma SHARAJA SID. Na san shi ta hanyar karatun wasu shaidun ban mamaki game da blogs .. rubutu firist sharajasid ++ (234) 9066-376197

    ReplyDelete
  3. domin samun littafain hausa ziyarci wannan shafi www.share4world.com.ng

    ReplyDelete
  4. hello 4 letest hausa novels complete visite www.hausabook.com

    ReplyDelete
  5. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete